KUSKUREN BAYA 1 TO 48

????️45
…..Arikice mumy tayo kanta tana kiran sunanta “tanwer!tanwer!! amman Shiru bata motsa ba ta kai hannunta daidai saitin hancinta taji bata sauke numfashi, tuni ta sake rikicewa tare da fashewa da wani sabon kuka “tanwer karki min haka ,ki barni haka karki qara min wata damuwar akan wacce nake ciki , damuwarki tana d,aga min hankali ,ki tausaya min ,kinsan ina sonki fiyye da komai a rayuwa ina son ganinki cikin farinciki da kwanciyar hankali shiyasa ma na amince miki da auri adnan ta qarasa maganar tana tattarota zuwa jikinta ta rungumeta tsam ta manna kanta a daidai qirjinta tana jijigata had’e da kiran sunanta adaidai wannan lokacin ruky da masu aikin gidan suka fito zuwa parlour’n a rud”.
Da sauri ruky ta qaraso ta durkusa agaban mumy tana cewa “Lafiya mumy naga tanwer haka kamar ma bata numfashi ?bata bata amsa ba dan bata san me zatace mata ba ,ita kanta bazata so ruky tasan irin nmj da diyarta ke kwakwar so kenan ba “mumy me ya sameta please ?”bata gama rufe baki ba mumy ta saki wani kuka me karfi “ki taimaka min ruky mu kaita hospital tana kokarin tashi ta gagara saka makon sakewar da jikin tanwer yayi, ruky tayi wuf ta mike jikinta na rawa ta nufi hanyar kitchen karo suka ci da zulai ne aiki rike da goran ruwa dan ita tun fitowarsu ta fahimci suma tan tayi ,da sauri ta kar’bi goran ruwan ta dawo inda mumy take zaune rungume da tanwer wacce bata da alamun motsawa ,
ta bude goran ruwan ta tsiyaya a tafin hannunta ta soma shafa mata ruwa a fuska tana kiran sunanta amman still shiru “.
Hankali ruky ya tashi kwarai saboda alamarin tanwer ya fara damunta iya saninta soyayyar adnan ne matsalarta kuma iyayenta sun amince mata tare da bata damar aurensa me kuma ya saura ?”to ma yanzu me ya faru da tai mummunar suma haka ?”.
Dan ita kam ta kasa gane kanta ko adnan din ne kuma ya fasa aurenta yasa ta shiga mummunar hali haka”?ruky tayiwa kanta tambayar da bata da me bata amsa tare da shiga rudani sosai da tunani game da alamarin tanwer, yayinda shi kuwa dady har lokacin yana nan tsaye yana dubansu cike da bakinciki mara musaltuwa batare da yace komai ba saboda takaici amman kuma shima din a matukar rikice yake baya dai son ya nuna ya shiga damuwa ne adalilin halin data shiga dan abun na tanwer ya wuce tunaninsa .”
Zufa ne ke keto ma mumy a gabadaya ilahirin jikinta yayinda zuciyarta ke tsananin bugawa gabadaya a rude take kallon dady dake tsaye har lokacin yana dubansu bashi da alamun nuna tausayawa gareta “abubakar ka taimakeni kar na rasa yarinyarta ,ka taimakeni mu kaita hospital domin ceto rayuwarta bazan gwamaci mutuwarta ba ka taimakeni dan allah “ta qarasa maganar cikin raunanniyar murya “naji zan taimakeki amman kafin nan sai kinyi min akwatin zaki tursasata ta cire wannan damuwar a ranta sannan ta tsaida zuciyarta akan Ibrahim ko wani mutumin kirki dabam .”ta gyada masa kai tana cewa ‘”naji nayi maka wannan akawarin zan ma bar kasar nan daita ni dai ta dawo haiyacinta shine muradina “auren ibrahim fa “? ta cigaba da girgiza masa kai “alamun a’a “.
“Daman yasa da wahala ta amince tafi bukatar farincikin diyarta dashi koma yace tafi qaunar tanwer dashi muryarsa na rawa da jikinsa ya soma qoqarin neman gurin zama yana me danne damuwarsa da tashin hankalin ganin halin da tilon diyarsa take ciki ya zauna ya cigaba da kallon abinda ke tafiya a gari,har wannan lokacin jami’an tsaro ne ke kan aiki ,inda jama’ar dake unguwar jaguwa suka cika kofar gidansa makil suna zanga zangar bazasu yarda a taba masa gida ba, hakan yasa polisawa suka kunna tiya gas tuni mutane suka fara darewa saboda zafi me hade da yaji dake shigar masu ido gefe guda kuma yan jarida ne ke faman tambayar mutane goma daaka fito dasu daga maboyar jaguwa ciki kuwa har da alhji tahir mahaifin Ibrahim.”
Cike da tsananin tashin hankali mumy ta kalli bakin tanwer dake fitar da wani kumfa fari sol bude ,ta bakinta da kyar “a karo na biyu abubakar kaci amanata wannan kalmar kawai take furtawa tana hawaye yadda take magana haka farin kumfa ke sake dalalowa abakin tanwer wanda ya dagawa dady hankali wannan karon kasa jurewa yayi ya mike a matukar tsorace bai san sanda ya zari keyn motarsa ya cicibi tanwer ya rungumeta ajikinsa ,shi da ya dauka abun wasa ne ,a rude sukayi waje daita ya nufi inda motarsa take pake tun kafin ya qaraso ya danna keyn hannunsa mumy ta bude masa gidan baya ya sakata ,bai tsaya jiran wani direba ba ya shiga mazaunin direba ya shiga ya zauna yana tada motar tare da danna hon da karfi .”
tun kafin ya qaraso bakin get aka wangale masa tafkeken get gidan ya fice da mugun gudu securities din bakin get suka bi bayan motar da kallo zuciyarsu cike da mamaki abinda yasa minister ya fita cikin tsananin tashin hankali haka ? fatan a sauka lafiya sukayi masa sannan suka maida get suka rufe ,
hospital da tanwer suka nufa kai tsaye emergency aka shiga daita gbdy kusan rabin abokan aikinta ne suka rufa akanta ana kokarin ceto ranta amman kusan minti talatin likitoci na kanta amman numfashi yaki dawowa hakan kuwa ya daga hankalin mumy da dady dan sai yanzu yaji nadamar abinda yayi domin shine silar faruwar komai da bai kunna tv ba da wata killa hankalinta bai tashi haka ba ,nan take jikinsa da hannunsa suka kama rawa balle mumy data kasa tsaye ta kasa zaune sai kai kawo take tana furta duk adduar datazo bakinta tausayin diyarta da halin da take ciki yasa ta kife kanta a bango tana kuka .”
Dady ne yazo yana kokarin rarrashinta duk da yasan ba lallai ta fahimcesa ba wani irin nauyi da kunyar abinda yayi dazu ya kamashi shi kansa a halin yanzu yana bukatar yayi kuka ya fidda hawaye ko zai samu ya rage nauyin zuciyarsa mumy tun tana turesa har ta hakura ta fada jikinsa suka rungume juna yana rarrashinta daga bisani suka samu guri suka zauna jugun jugun suna jiran fitowar likitoci shiru wasu mintuna talatin tazo ta wuce lokacin har an kira sallahr laasar suka je sukayi alwala suka yi sallah tare da nemawa yarinyarsu sauki a gurin ubangiji allah madaukakin sarki .”
Suna zaune wayar mumy tayi qara ruky ta miko mata sunan ibrahim ta gani dan haka taki dauka dan yanzu haushi yake bata gani take kamar shine silar fadawar diyarta cikin fagarumin matsala tana mikawa ruky wayar kira ya shigo wayar dady ganin me kira ya daga da sauri suka gaisa anan yake fada masa cewa suna asibiti tanwer ce a emergency bai rufe bakinsa ba yaga an turota an nufi I.C.O daita da mugun sauri suka tashi atare suka shiga cikin suka samu tana sauke numfashi kadan kadan sai dai bacci take nan mumy ta zauna ta kife kanta da gadon da take kwance tana zubar da hawaye yayinda take tunanin jaguwa ko a wani hali yake .”?
Yadda jaguwa yayi shiru ya zuba masu rikitattun idanunshi da suka gama canza kala yana dubansu daya bayan daya domin jin abinda zasu ce ,haka suma suke kallonsa domin rasa abun cewa har sanda Ana’s ya zaro wayarsa da yaji motsinta ta hanyar bebriting tun kafin ya duba zuciyarsa ta bashi tabbacin me kiransa ai kuwa yana dubawa sunan my princess ya gani yana yawo a screen din wayar .”
JAGUWA ya dubesa cike da tashin hankali sai dai bai ce masa komai ba sai anas ne ya motsa labbansa a hankali maganarsa ta fito “hally ce !“.yana fadar haka yayi shiru “ka karka d’auka,idan wayar ta gama ringing ka kashe gabadaya .”