KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Wallahi har gara jaguwa duk da kasancewarsa dan taada yana da tausayi tunda har zai iya cetar rayuwar wani daga mutuwa “sosai kuwa.” sai lokacin yasan a fili yayi maganar “idan dai har wannan mutumin da’aka kama yau din nan shine ake kira da jaguwa yana da kyakkyawan zuciya kuma ina kyautata masa zato koni zan masa fatan fitowa domin ya samu yanci kamar sauran mutane domin shi din mutumin kirki ne .”
Bangaren hally kuwa da rashin sukuni ta mike ta shige uwar dakan ammi kasala sosai ta lullube duk ilahirin jikinta har ta rasa dame zata fara daga cikin abinda ya kamata tayi “ lallai jikinta na bata akwai wani abu dake faruwa da mijinta a duk inda yake dan yadda take ji ajikinta babu sauki ,ammi ta shigo dakin ta ganta kwance bata ce mata komai ba illa ta shige bayi ta dauro alwala ta fito ta shimfida sallaya ta tada sallah dan lokacin sallar magrib tayi .”
bayan ta idar ta zauna tana lazumi tana adduar allah ya tsare mata ya’yanta .”ammi ta mike ta zauna kusa da hally dake kwance har lokacin ita kanta yanzu tana jin jikinta wani iri amman ta daure ta kai hannunta kan hally tana shafawa tana rarrashinta da kyar ammi ta mikar daita tsaye “ba kwanciya ya kamaceki ba auta kije kiyi alwala kiyi sallah kiyi masu addua gabadayansu inshaallahu babu abinda zai samesu yadda suka tafi aikin nan lafiya haka zasu dawo lafiya “.banda inna lillahi wa inna ilaihi rajiun babu abinda hally take maimaitawa gbdy tayi rauni saboda tsananin fargaba.”
Karfe bakwai da rabi tanwer Ke fama kokarin bude idanunta amman ta kasa duk da akwai oxygen a hancinta amman numfashinta da kyar yake fita ,a hankali abinda ta gani a tv ya shiga kai kawo acikin kwakwaluwarta babu abinda take gani sai harbe harben da jami’an tsaro suka dinga zubawa a gidan jaguwa ,wata razannaniyar qara ta saki da karfi tana fixge fixge tana kiran sunansa da sauri iyayenta sukayo hanyar dakin da take wanda zuwa lokacin har ta fixge abun oxygen din daaka kafa mata a hanci tana ihu .”
Mumy da dady suka shigo dakin fuskokinsu cike da tsananin tashin hankali mumy ta kamota ta rungumeta ajikinta tana shafa bayanta tana kiran sunanta “ tanwer ki natsu please babu abinda zai faru dashi zanyi duk abinda nasan adnan zai tsira daga hannun hukuma batare da an ta’ba lafiyarsa ba magana mumy take mata amman ko ajikin tanwer dan bata ma san me take cewa ba bakinta kawai take motsawa a hankali mumy ta kai kunnenta daidai bakinta “an harbe adnan dina shikenan ya mutu nima na mutu ,ni yanzu gawa ce ,ya mutu na mutu shikenan daman zaman jiransa nake a duniya tunda ya mutu nima mutuwa zanyi duk wadan nan maganganun da take idanunta a runtse suke babu ma alamun zata budesu jikinta ya sake sakewa alamun ta tafi ”
“Wayyo! tanwer karki tafi ki barmu zamu tallafa miki babu wanda zai kashe miki adnan ta qarasa maganar tare da janyo hannun dady “ka fada mata da bakinka babu abinda zai samesa zamu yi komai ya fito.” tsananin tashin hankali yasa dady ya kasa furta komai ban da suya babu abinda zuciyarsa keyi cikin sauri ya rike hannun tanwer din kansa na wani irin harbawa gabadaya ya kasa kwakkwaran motsi “kace wani abu mana ,shikenan bata numfashi fa Wayyo allah ta mutu ta fada hade da kwantar da tanwer tayi waje da gudu tare suka dawo da likitoci nan suka sallamesu gabadaya da kyar suka fita suka tsaya a bakin kofa kana suka rufa akanta .”
adaidai lokacin ta sake sakin wani ihun “wayyo allah ku sakeni ku kyaleni bana son taimakon komai daga gareku nifa lafiyata lau amman ni yanzu ba mutun bace gawa ce, ku kai ni inda ake kai matattu ni yanzu gawa ce kamata yayi ku kai ni inda adnan ya tafi mu kasance tare ,na fadawa babana shi nake so shi nake so yaki yarda gashi nan an kashesa.”
cikin sauri doctor muyis ya bawa wata likita dake tsaye kusa dashi umarni ta kawo masa allurar bacci cikin tsananin tashin hankali ta fita bata jima ba ta dawo hannun rike da karamin tiren silve ta tsaya kusa dashi tana mika masa kwalba da sirinji ya karbi allurar ya zuka acikin sirinji yayi mata nan take jikinta ya shiga sakewa a hankali ta fara lumshe idanunta sai bacci likitoci suka fara fita daya bayan daya aka bar mutun biyu da likita ya basu umarnin su canza mata daki .”
Aka turo tanwer akan gadon marasa lafiya aka fito daita mumy da dady suka rufawa likitocin dake turata baya mumy ta rike hannunta daya cikin nata ta damke sosai kamar wacce aka cewa ta mutu ,da sauri take binsu tana wani irin kuka shima dady da sauri yake binsu zuciyarsa tayi masa nauyi , atare suka shiga dakin da zaa kwantar da tanwer likitoci na gama aikinsu suka fita suka barsu jugun jugun cikin tsananin damuwa suna duban diyarsu dake kwance cikin wani hali .”
mumy ta kallesa ta sake rushewa da matsanancin kuka tana cewa “dan girman allah abban tanwer kayi wani abu akan alamrin nan , nasan kana da karfi da ikon fada aji a garin nan ka nemi alfamar a saki adnan sau daya kayi aikin alkhairi arayuwarka sannan ka ceci rayuwar diyarmu ,kana kallo kuma kana ganin abinda ke faruwa daita akansa zamu iya rasata gabadaya ta qarasa maganar tana share hawayenta bai ce uhm bare uhm ya cigaba da kallon tanwer dake kwance duk ta hargitse .”
Har kusan awa uku da faruwar alamarin sannan a hankali kofar dakin da zaa iya kiransa da bakin daki ta bude wani kato karfafa me siffar majiya karfi ya kuso kai ciki banda mazurai babu abinda mutumin yake da gani babu alamun imani a tattare dashi baki ne wulak sai sheki yake tamkar an kwara masa man gyada ,tunda jaguwa yayi masa duban farko bai sake dago kai ya dubesa ba domin mummunar fuskarsa me saka faduwar gaba ce da firgici.”
Yaja kujera ya zauna agaban kujerar daaka daure jaguwa yana mazurai kai kace wanj gawurtaccen zakin daya nemi abinsa ya rasa ,zuciyar jaguwa ta cigaba dubansa madadin kwayar idanunshi dan kallonsa zai sa ya hadiye zuciya “.
mutumin ya ajiye kulkinsa da karfi akan table jaguwa ya dago yayi duba zuwa ga kulkin dake ajiye akan teburi dake gaban wannan katon mutumin yaji gabansa yayi mugun faduwa yau kam tashi ta kare domin duk wanda aka buga da wannan kulkin to kuwa sai dai wani bashi ba ahankali aka sake turo kofar asp isa ya bayyana acikin dakin da sauri wannna kato ya mike da sauri tare da kamewa
“sir!. ya fad’a yana raba idanu .”
Asp isa ya dubi jaguwa “menene sunanka?”ya fada shiru adinanu yaki magana “yaya sunan babanka ?”ya sake jefa masa wata tambayar sai lokacin jaguwa ya dago yana kallonsa batare daya bashi amsa tambayar da yayi masa ba, kusan minti goma ana jiran aji amsa daga bakinsa amman yayi shiru yaki cewa komai “asp isa ya cigaba da tambayarsa “ko zamu iyasanin wadan da suka dauki nauyiku da kuke wannan taadanci.”
“su wa kenan suke yin taadanci “?jaguwa yayiwa
asp isa wannan tambayar a dake ba zakace shi din me laifi bane shima asp isa shiru yayi dan shima miskilan kansa ne sautin muryar jaguwa ce tasa ya dago ya tsura masa ido “ni ba dan taada bane .”
Shiru asp isa yayi yana cigaba da dubansa gabansa na wani irin faduwa kafin daga bisa ya cigaba da magana “idan kai ba dan taada bane wanene kai “.
still yaki magana ya bashi minti goma yana jiransa amman stil yaki cewa komai asp isa ya ciza lip’s dinsa da karfi aransa yana cewa “wannan tantirin yafishi miskilanci .”
dan haka ya mike tsaye tare da duban wannan katon mutumin “sajan tomy ku tambayesa har sai ya gaya mana gaskiyar abinda yasa suke aikata wannan taadanci da kuma wadan da suke daure masa gindi yana gama fadar haka yasa kai ya fita daga dakin cikin bin umarnin ogansa tomy ya kai hannu ya zari kulki yayi kan jaguwa ya fara buga masa bai ji bai gani tun yana iya kare kansa har ya kasa dan tsabar galabaita da yayi , sai da tomy ya sumar dashi sannnan ya hakura ya barshi ya fice daga dakin.”