KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bai sake ganin kowa acikin ma’aikatan polisawa ba sai da yammacin kamar jiya wani murdade me  irin siffar jikinsa ya kutso ya shigo cikin dakin shima hannunsa rike da makeken kulki kamar na mutumin jiya yayinda dayan hannunsa ke rike da wata katuwar tocila me shegen haske saboda tsananin duhun dakin koda rana duhu ne babu haske .”

wani irin  kallo yayi masa yana mazurai “na shiga uku wannan ma da alamun duka zai sha agurinsa?”
ya fadi haka acikin ransa sai dai a zahiri bai nuna gazawarsa ba ,ya kafesa da kunburarun idanunshi jaguwa bai ankara ba yaji saukar wannan kulkin a damtsensa inda harbi ya samesa wani irin qara ya saki guda daya me karfi yana dafa daidai gurin tare da dukar da kanshi yana ciza lips dinsa na kasa da karfi dan shi kadai yasan irin zafin daya ji ya ziyarci ilahirin jikinsa.”
Mutumin ya tako har inda ya matsa duke da kanshi ya daga habarsa “zaka mana bayanin kanka da kuma wadan da suka dauki nauyin wannan fashin da kuke yi ? shiru ne ya biyo baya “baza kayi magana ba sai na karairayaka “?ya fada yana nuna masa jikinsa cikin ciza lip’s dinsa ya shiga girgiza masa kai alamun bazai fad’a ba “.

Police din yayi dariya me kama da sautin kukan saniya yace “lallai taurin kanka ya burgeni amman kuma kana tare da katuwar wahala idan kace bazaka fadi inda sauran abokan aikinka suke ba sannan da wadan da suka dauki nauyunku ba .”Ya kuma gyara zaman kulkin dake rike a hannunsa fuskar nan tashi ko alamun tausayi babu rashin mutunci da rashin imani ne kawai ke tattare acikinsu.”
Jaguwa ya runtse idanuwanshi wadan  da suka yi luhu luhu saboda tsabar azabar da suka shiga sakamakon shirga masa shirgegen kulkin da mutumin jiya yayi ga kuma na yau wanda ke nuna alamun zai fi na jiya rashin mutunci dan daga ganinsa ma kasan bazai yi tausayi ba ko yace da marasa tausayi aka hadashi  .”

Rufe shi yayi da duka har sai daya ga alamun ko hannunsa bai iya dagawa kana ya fice ya barshi shi ba matacce ba kuma babu wani alamun  na mai rai idan ka dauke numfashi dake fitarwa da kyar daga wannan dakin aka kwashesa aka sake canza masa wanj daki na mussaman ,wanda rodikan dake cikinsa sun kai girman muciya.”
Wannan dakin daki né na mussaman domin adana masu manya manyan laifuka irin su jaguwa da irin wadan da ake biyansu kudi su kashe mutane suka watsa shi kamar kayan wanki lokaci daya ya sake sunewa allah ne kadai yasan adadin awanin daya dauka cikin wannan halin amman ya kudurcewa ransa duk runtsi duk wuya bazai furta komai ba koda kuwa zai mutu ne ya gwamaci mutuwa daya furta inda sauran abokan aikinsa suke .”

Mumy na zaune a gefen gadon da tanwer take kwance ta zuba mata ido kawai tana kallonta hawaye masu zafi na gangaro mata sakamakon sambatun da tanwer din ke yi cikin zubar da hawaye tace “ki dauki qaddara tanwer adnan bai mutu ba har yanzu yana hannun hukuma idan ma mutuwa yayi kisa aranki allah ne ya baki adnan idan kuma ya karbi abunsa sai ki karbi qaddara daya daura miki .”cike da matsanancin mamaki mumy taji sautin muryarta cikin tsananin tashin hankali “haka né mumy nayi Imani da allah can kuma ta birkice,me yasa allah zai min haka “?wani irin zunubi na aikata da allah zai jarabeni da rashin adnan rayuwata ?” rayuwata né adnan ,duniyata né adnan ki kira min shi mumy bamu tsara cewar zai mutu ya barni ba ,zan bisa duk inda yake ta qarasa maganar tana kokarin durowa daga daman gadon mumy tayi wuf ta rikota da iyakacin karfinta ta rungumeta ajikinta tana wani irin kuka mai ta’ba zuciya gabadaya acikin kwana biyu duk ta fita haiyacinta.”

Doctor muyis yayi matukar jin mamakin wanda tanwer take kokarin haukacewa akansa d’an fashi ne da kasa ta dade tana nema “lallai karfin soyayya ya zarta kowani karfi da asiri tasiri ajikin dan adam .”bayan ya shiga inda take ya duba kafiyarta ya koma office dinsa ya shiga bincike game da ciwo mai kama da tabin hankali dake kokarin kama tanwer ,da kyar yayi nasarar gano abinda zaayi a shawo kan natsalar bayan ya gano komai ya tara sauran likitocin da suke aiki tare domin su tautauna ,a wannan daren ma shima kamar daren jiya ya kasance agurin iyayen tanwer da likitoci dake aiki a hospital din domin kuwa kwanan wahala sukayi sakamakon bakinciki , bacin rai ,kewa , dacin zuciya,hauka tare da fixge fizgen zata tafi gurin adnan dinta .”

Gari ya dauki zafi ko ina ka gilma magana biyu ake yi jaguwa dan fashin da hukuma ta dade tana nema ya shiga hannun da kuma labarin diyar minister ta samu tabin hankali wasu suce shaye shaye ta fara bai karbi kwakwaluwarta ba yayinda wadan da suka san gaskiya suke fadar albarkaci bakinsu .”
Haka yan gulma da tsegumi da kuma wasu daga cikin matan abokan minister suka dinga zariya zuwa hospital sai dai mumy bata barin a ganta domin tasan abinda zasu gani dabam abinda zasu qarar dabam ko hajiya basera basu yarda sun fada mata gaskiyar musababbin ciwon tanwer ba ta boye mata gaskiyar alamari d’an matsalar ba kowa né zai fahimta ba kuma duk zuwan da take bata cin sa’ar samunta ido biyu bare tayi hauka agabanta .”

Bayan kwana biyar

Dady yayi nasarar ganin kwararun likitoci da doctors muyis ya gayyato daga hospital dabam dabam tare da neman shawarasu ciki kuwa har da sadiq Kanin jaguwa wanda kusan shi yafi kwarewa akan irin matsalar tanwer sai dai alokacin bai samu damar amsa gayatar ba sakamakon tafiyar dake gabansa zuwa abuja ,tunda likitoci suka fara magana akan abubuwan da zaa fara mata domin gano ta inda zaa shawo kan matsalar dady ke dubansu yana sauraronsu one by one mutun na karshe ne yayi bayani kamar haka wanda yasa jikin dady ya qara yin sanyi “ firgici da tsananin tunanin da yayiwa brain dinta yawa ne yasa take qokarin losing momery dinta amman a hankali da zata samu abinda take zafafa tunaninta akanshi zata dawo normal .”
Naunayen ajiyar zuciya ya dady ya sauke dan yasan inda matsalar take ,ahalin yanzu ya sadaukar da komai kuma yayi Imani adnan shine rayuwar diyarsa shine farincikinta, kuma tabbas zata iya mutuwa ko haukacewa muddin babu shi ,dan haka ya tatttara komai ya sake watsarwa ya dauki dukkanin wata kulawarsa da lokacinsa ya mayar akan rashin lafiyarta tare da qoqarin ganin yadda zai yi ya fito da jaguwa wanda hakan ya janyo hankalin mumy ya dan kwanta dan ita kanta tana tsananin jin tsoro da fargaban tanwer ta haukace ,don yanzu kam ta zama kamar tababbiya tunda kullum cikin kukan son adnan take da son ganinsa take tana ihu tana kiran sunansa amman da zarar ance zaa kira mata shi sai tace bata son ganinsa.”

Tun lokacin da labarin wannan maseefar ta afkawa Ib ya kasa samun natsuwa sannan irin kyawawan halaiyan jaguwa da yaji a bakin jamar unguwar ya qara jin tsanar da yayiwa jaguwa ta kau domin dai ya sake komawa unguwar duba da yadda yaga mutanen unguwar suke kai kawo a headquarter har suna kokarin daukar masa lauya , saboda manya manya unguwar sun zo ba’abari sun gansa ba ,haka zalika zuwan malam mudi biyar sun hanashi ganinsa sun kuma tabbatar masa babu halin da zasu bashi damar shiga koda kuwa da lauya ne dan har lokacin basu samu wata hujar daga bakinsa da zatasa su bada damar a daukar masa lauya ba ”a halin yanzu shi kansa ib ya daina ganin laifinsa sai na mahaifinsa da sauran azzaluman da’aka fito dasu daga gidansa .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button