KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Doctor muyis ya dawo hankalinsa sosai yana duban dady kamar me yin wani nazari “Kayi hakuri dady zamu iya kasan lalura irin wanda yake kokarin samunta dole yana bukatar bincike gabadaya mun gama gwaje gwajenmu wasu result sun fito wasu basu fito ba ,wadan da basu fito ba muna son mu bashi lokaci ne saboda tabbatar mana da amsar da zai bamu daidai ne da abinda muke tunani kuma dole sai dr sadiq yazo tunda mu baa aikinmu bane amman ina da tabbacin zata dawo daidai kaga result dinta ya mika masa wanda muka sake yi jiya ne ya saura ina tunanin zai fito kafin dr sadiq yazo
nan dady ya fahimcesa ya karbi result din yana dubawa kasancewarsa shima likita ne ya koma zuwa dakin da mumy take ita kadai ya gani zaune kusa da tanwer tana shafa mata sumar kai .”
Ya mika file mata file wanda yake dauke da result din gwajin da sukai wa tanwer yace “komai na ciki ta kallesa “meye mafita “?meye maganinta ?”wai har yanzu suna kan bincike akwai wani babban likita da sukayi appointment dashi inshaallahu zai nemo mana magani matsalarta mumy ta fashe da kuka byn ta gama duba result din “kace kafin nan diyata ta qarasa haukacewa nan ta mike ta bar dakin tana wani irin kuka dady kam tuni yayi mutuwar tsaye agurin damuwa da tashin hankali yayi masa yawa ya rasa me ke masa dadi.”
A hankali jaguwa ya fara bude idanunshi cikin azaba dake tattare dashi gabadaya jikinsa duk inda ya motsa banda azabar ciwo babu abinda yake ji ,da kyar ya kai bangon dake dakin da taimakon allah ya ambaci sunan allah “ya hayyu ya qayyum abinda yake furtawa kenan shi kadai yasan azabar da yake ji a hankali ya rufe idanunshi da suke masa radadi tamkar su fado dan azabar zugi da suke masa.”ya ja jiki cikin tsananin radadi da yake ji acikin kwayar idanunshi tamkar kansa zai rabe gida biyu a hankali ya jingina da bangon sosai zuciyarsa ke kokawa akan abokan aikinsa ko a wani hali suke ciki? babu abinci sai ruwan sha a inda suke ko sun fito ko suna ciki .”?yayiwa kansa tambayar yasan bazasu ta’ba yunkurin fitowa ba muddin ba ganinsa sukayi ya dawo garesu ba ya ubangiji ka tallafa masu allah kasani kasan dalilinmu nayin wannan aiki .”
Lokaci daya ya juya sakamakon qarar da yaji karfe daaka datse shi aciki ya tabbatar masa da cewar shigowa ake shirin yi cikin cell din nan da nan zuciyarsa ta shiga harbawa duk da babu wani alamun tsoro a tattare dashi amman faduwar gaba ta zama dole a hankali yake kiran sunan allah domin neman dauki wasu kurata ne suka shigo cikin dakin su hudu banda mazurai babu abinda suke .”
Cak suka daukesa suka fita dashi zuwa wani daki dam gabansa ya fadi lokacin daya ga wasu gadaje gefe da gefensa tare da belt sama kuma wata fitila ce me shegen haske daya daga cikin gadon suka nufa dashi suka cilla da kan gadon bayan suka saka hannunsa kan belt sun dauki lokaci sannan gadon ya fara juyawa dashi hajijiya ya dinga yi dashi kusan minti biyar cikin wannan yanayi gabadaya hankalinsa ya gama fita daga jikinsa .”
Lokaci daya gadon ya tsaya kansa akasa haka ya dauki lokaci kansa gbdy ya juye sannan suka danna madanni abun gadon ya sake cigaba da aiki bibiyu ya dawo yana gani komai acikin dakin hakan ne yasa shi runtse idanunshi domin brain dinsa ta kasa daukar komai saboda tsananin juyin da kansa keyi wanda hakan ya haifar masa da tsayuwar kwakwaluwa cak .”
Gabadaya ya daina fahimtar komai saboda tsananin azaban da yake ciki ya tafi zuwa wata duniya da bai san daita ba jikinsa sai rawa yake duk wani kala na azaba sun masa amman dai yaki magana d’an haka suka tattara shi suka watsashi acikin wani mummunar daki suka garkameshi sai daya kwana ya wuni bai san a halin da yake ciki ba .”
Maganar abinci kuwa babu ita domin sai da lafiya zai ci ,dan abinci da suke kawo masa bai fi wanda yaro karami dan shekara uku zai ci ba dan haka ko dandana abinsa bai ta’ba yi ba domin shi mutun ne me tsantsani har da ruwa ake bashi sai dai baya iya sha saboda haka kafin wani lokaci ya fice daga haiyacinsa ya sauya matuka .”
yana zaune takure suka turo masa silver daake tura masa abinci ,yabi abincin da kallo sam bai bukatar komai sai taimakon ubangaji , har lokacin da yake cikin maseefa zuciyarsa na tare da jin soyayyar tanwer bai daina jin radadi sonta ba,da tunaninta yake samun natsuwa da karfin zuciya da sanyi rai yana samun duk wani comfort a hotonta da zuciyarsa ke hasko masa yana matukar jin sanyi da saukin zuciyarsa .”
adaidai wannan lokacin da yake tunaninta nabel da Ibrahim suka shigo nabel na gaba cikin bakake kaya suit , yayinda ib ke bayansa sanye cikin kananan kaya nabel ya cigaba da takowa a natse yana cewa “yayi gahurtacce me shegen taurin kai an fad’a min komai cewar kaki magana ko”?Kana son barin duniyar nan da sauri batare daka tonawa sauran abokan fashinka asiri ba, to wallahi baka isa ba dole sai kayi magana you most talk idan ba haka zaka cuci kanka da rayuwarka ne domin ni nan nake maganin irinka da duk ma wadan da suka daure maka gindi a kasar nan.” nabel ya fad’a cikin tsawa tare da nuna jaguwa nayi maka alkwarin ni nan zan sakaka kayi magana batare daka shirya ba “.
On expecting nabel yaji sautin muryar jaguwa yana cewa “ya isheka enough with your accusation ,ba nabel ba hatta ib ya firgita da jin maganar maganar jaguwa cike da karaji ya kalli nabel dake kallon jaguwa domin dai yasan waye nabel akan aikinsa da kuma karfin ikonsa duk zone 2 babu wanda ya isa ya takasa ya kwana Lfy tun kafin ya kawo matsayin da yake a yanzu da yake dc admin jaguwa ya cigaba da magana “ka daina cika baki ka jira lokaci kaga me zai faru ,ina tabbatar maka kai ne zaka shiga tsaka me wuya ko nace mutuwa zata daukeka batare daka shiyarwa hakan ba,ka fara gujewa mutuwa domin kuwa tun yanzu ta fara bibiyarka .”
wata irin mahaukaciyar dariya nabel yayi yana nuna sa da danyatsa “me maimakon kaji tsoro ko nemowa kanka mafuta shine kake barazana wa jami’an tsoro Irina “?wallahi ka qara lalata komai ka qarawa kanka wahala da tashin hankali zaka ga azaba ganin idanunka zaka ga wahala da ranka zaka zamo kai ba matacce ba kai ba rayayye ba ya qarasa maganar yana damkar wuyansa cikin zafin nama yace “idan duk garin nan da kasar nan gatanka ne sai na ‘batar da kai da ….”
“Dc Nabel!.”
Dcp A.A shalem ya kirasa cikin kunar rai nabel bai juyo ba har sanda dcp ya cigaba da magana “babban minister na kasa ya bada umarnin a fito dashi bayan an fito dashi akawoshi zuwa garesa “babban me ..”?ya fad’a tare da juyowa a matukar firgice zuciyarsa na karkawa …”
Mmm sudais????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
????️48
…..Kan DC nabel ya juye lokaci d’aya ya rasa madafar dafawa bai san lokacin daya kama girgiza kansa ba cike da tsananin mamaki sam bai yarda ba ace wai babban minister da kansa na bukatar ganin gahurtaccen d’anta’ada kamar wannan ba ,
”to yayi masa me ?”.“mai zai sa hakan ta faru ?”IB wanda ke tsaye har lokacin rungume da hannun wansa duka a qirji ya zubawa jaguwa idanunshi yana kallonsa zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin karfin gaske “shi ba wai umarnin da dcp ya bayar ne yafi damunsa ba kamar shamaki da jaguwa yake son yiwa rayuwarsa da tanwer dinsa yarinyar da yakewa mahaukacin so ,soyayyar mai karfi dake huda duka sansar jiki ,cikin wani irin sauri zuciyarsa ke cigaba da bugawa kamar zai fito daga qirjinsa.”