KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“tabbas a halin yanzu baya jin haushin jaguwa haka zalika baya jin qaunarsa acikin ransa domin kuwa yayi masa illa mai yawa a rayuwarsa tunda ya sace zuciyar cikar burinsa tsantsar soyayyar daya nuna mata da kuma kulawar na tsawon shekaru kafin zuwan girma duk ya tashi a banza kenan ,ya rushe masa komai , har yanzu da take haukan kiran sunansa da zantuttuka akan son da take masa bai ji soyayyar da yake mata ya ragu ba domin yana jinta aransa da dukkanin jinin jikinsa, sonta yabi jini da tsokansa, yayi yaqi mai yawa dan son ya mallaketa amman yanzu dukkanin alamun sun nuna masa zatai masa nisa .”
Ya runtse idanushi gam ya shiga tunani “da soayayyarta ya saba da ita ya bud’e idanunshi yana sonta so na hakika yabi rayuwarta ya koyar daita darasi na soayya iri iri ashe duk wahalar banza yake tun da gashi cikin lokaci kankanin ta haukace akan son wani , wani ma ba kowa ba sai zero tunda bai hada duk quality’s din daya hada ba.”
a hankali ya bud’e idanunshi akan jaguwa suka sauka Kurawa juna idanun daga IB har jaguwa sukai suna kallon junansu ,nan take tausayin kansa ya kamashi yana jin kamar ya taka ya isa inda yake ya tambayesa dalilin da yasa yayi masa haka ,”mai yasa zakayi min haka “? yayiwa kanshi tambayar cikin qunar rai cike da matsanancin bakinciki IB ya dauke idanunshi akansa yana shafa sumar kanshi batare da yace komai ba sai dai zuciyarsa zafi take masa tamkar zata kama da wuta .”
cikin tsananin kad’uwa DC nabel ya juya bayansa ya sake duban jaguwa da kyau dake cikin sarka hannu da kafa shima jaguwa kallonsa yake yana sauke ajiyar zuciya, shi kuwa DC auna dalilai dalilai yake har da zai sa babban minister ya nemi ganinsa amman ya rasa ko daya, ya sake kad’a kai cikin mawuyacin halin dan baqaramin tashin hankali ya tsinci kansa ciki ba zuciyarsa banda bugawa da sauri sauri babu abinda take .”
”dcp ya bawa sajant tomy umarnin ya shiga cikin dakin ya kwance mugun daurin da sukayiwa jaguwa “kuyi sauri ku kwancesa please dan duk abinda yasa babban minister ya bukaci ganinsa dalilin ne me karfi yana gama fadar haka ya juya da sauri .”
Iyakar tunanin mai tunani DC nabel yayisa har kwakwaluwarsa ta fara gazawa kasancewar tunanin na neman masa illa dan nan take ya hadu da wani matsanancin ciwon kai ,har aka kwance jaguwa ya mike tsaye da kyar yana taku da kyar saboda rauninka dake jikinsa bai sani ba , jaguwa yana daf da barin dakin hanakalinsa ya dawo jikinsa.”
“To waye shi da babban minister na jaha yace akawoshi? “waye kuwa bayan Karen farautarsu inji cewar IB ya fad’a cike da matsanancin bakinciki “ba wannan bane kawai dalili da yasa yace akawo shi lallai akwai wani abu atattare dashi .”a hankali jaguwa ya juyo ya kallesu daya bayan daya yana girgiza kai sannan ya tsaida kwayar idanunshi akan Ibrahim kana ya motsa labbansa “kai yanzu kaga nayi maka kama da Karen farautan yan siyasa?” Kuri IB yayi masa ido qirjinsa na sama da kasa dan duk sanda yayi magana sai yaji bugun zuciya, jaguwa na qoqarin sake cewa wani abu dcp ya sake dawowa da sauri yana sake bada umarnin “kuyi sauri mana yace daga nan a wuce dashi hospital “hospital .”? IB da dc nabel suka hada baki gurin fadar haka wani sabon mamaki na sake lullubesu.”
jaguwa bai qara yunkurin cewa wani abu ya sake juyawa ya qarasa ficewa daga dakin da sauri suka mara masa baya suna maimata kalmar hospital “lallai yana bukatar ya sake zurfafa bincikensa akan wannan matashin dan fashin akan wanda ya dauko yi da farko ,ya fara bincike akansu amman kuma ya dakatar domin abubuwa bai bari ya zauna ya duba na’ura me dauke da mahiman bayanai akan kowani jami’an tsaro dana sirri ba ,kamar iska haka nabel ya fice daga dakin zuwa haraban headquarter .”
Bai tsaya jiran direbansa ya bude masa murfin mota ba ,ya bude gidan baya ya shiga ya zauna yana sauke numfashi direbansa yaja suka wuce zone 2 cikin tsananin tashin hankali yana matukar jin tsoro ace shi din jami’in sirri ne gara ya tsaya a matsayin Karen farautar yan siyasa , amman kuma yanzu da bakinsa yaji yace” anga yayi kama da wanda zai zamo Karen farautansu .”?
“Lallai wannan abu akwai daure kai da jefa zuciya shiga tashin hankali, lallai sai na gano waye shi da matsayinsa agurin babban minister gudu direbansa yake akan titi amman sam baya ganin motar na gudu dan sai yaji kamar ya fita ya cigaba da takawa da kafafunsa zai fiyye masa sauki ,tunani kuwa yayi wannan ya ajiye ya dauko wani kafin direbasa ya qarasa zone 2 ya hada wata irin zufa data jika kayan jikknsa .”
Har suka qaraso abun na damunsa ya kasa samun sukuni acikin ransa kallo daya zaka masa kasan baya cikin haiyacinsa da kwanciyar hankali .”
Ko cikin gurin aiki ranar kowa yasan lallai akwai damuwa atattare dashi ,ko kuma an samu wanda ya tabo dc nabel ,duk wasu na kasa dashi wato masu qaramin matsayi suka kama kansu daga sara masa babu wanda yayi gigin shiga office dinsa da wata matsala domin sun san halinsa ,duk wanda yayi gigin shiga track dinsa a yau din nan ya kade har gayensa domin zai sha fada na tashin hankali idan bai ci saar ya dakatar dashi na wani lokaci ba.”
tunda ya shiga office dinsa bai fito ba hatta yammatan da’ake kawo masa yau bai bukata ba haka coffee da yake sha duk bayan minti talatin bai sa an kawo masa ba hatta sigari wanda ya zamo tamkar jinin jikinsa bai sha ba domin kuwa itace mafi kusanci da rayuwarsa duk damuwar da zai shiga baya iya hakura da shanta amman yau sai yaji ta fice masa arai dan duk wani abu nasa ya tsaya cak burinsa da kwanciyar hankalinsa ya san waye jaguwa da matsayinsa ,duk wasu jami’ai dake tafiyar da lamuran computer sai daya tura masu sako da hoton ainin fuskar jaguwa yana bukatar a duba masa waye shi da kuma matsayinsa .”
Likitoci sunce kar a dinga matsawa tanwer da hayaniya dan kwakwaluwarta bata bukata hayaniya dan haka duk masu son zuwa dubata suka hakura halin da tanwer take ciki mai wuyar sha’ani ne ,babu ranar da zaka same mumy ciki sukuni sai cikin zullumi da tashin hankali in lalura bata lullubeta ba to surutai da fadefaden maganganu zasu baibayeta ,
duk da lalurarta ta shafi kwakwaluwa amman likitocin dake sintiri akanta sun tabbatar da cewa zata samu lafiya amman hakan baisa mumy ta gasganta haka ba gani take kamar kullum matsalarta qaruwa take.”
Mumy ta mike daga kan sallaya ta qaraso ta tsaya a bakin gadon da take kwance tana sharar bacci ta kai hannunta tana kanta tana tofa mata duk wata adduar da tazo bakinta har hular kanta ya zame ta cigaba da shafa sumar kanta tana jin babu dadi aranta ina ma ana daukewa bawa wata lalura wallahi data daukewa diyarta wannan ciwon ta huta .”
Ta runtse idanunta saukar ruwan hawaye taji akan kuncinta ,tayi kuka sosai lokaci guda wayarta dake ajiye a durowa marasa lafiya ta fara ringing wanda hakan ne ya tsaida kukan da take , ta kalli wayar daga inda take tsaye da kamar bazata dauka ba sai kuma tayi tunani ta dauka ko kiran mai mahimanci ne dan haka ta qarasa inda wayar take ta dauka ta kara a kunne tare da sallama .”yanzu barrister kana ganin babu abinda zaka iya akai kenan .”?
“Gaskiya babu dan duk wani abu da zamuyi ya kau domin yanzu haka ma babban minister da kanshi ya bukaci ganinsa, kuma shi ba zai saurari komai daga lauyoyi masu zaman kansu ba tunda ga sheidu nan kowa ya gasganta shi me laifi ne bayan mutanen daaka samu a gidansa har da maka mai da kwayoyi da hodar iblis duk da jami’an tsaro basu sanar damu komai ba amman mu yanzu a tunaninmu prison zaa canza masa mai tsaro kafin a bukaci lauyansa .”barrister ya dauki lokaci mai tsawo yana yiwa mumy bayani kafin daga bisani sukayi sallama naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke ko babu komai tasan yana raye kuma duk yadda zatayi zatayi iya kokarinta sai dai idan abun yafi qarfinta tasan shima mijinta bazai bar abun haka ba tunda yaga irin halin da diyarsu take ciki .”