KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

dakata dan Allah malam ni babu abinda nayi daita “to me amfanin rike musu yarinya da kayi  ?  “Ka ….
kit ya katse kiran yana dafe goshinsa tare da rike kugunsa da daya hannunsa  wani kiran ne ya shigo ya sake katsewa ya kashe wayar gaba-daya ya koma d’akin  yana Kallonta idanunta a lumshe alamun tana  jin bacci rabawa yayi jikinta ya kwanta  tare da  matseta   ganin haka yasanya shi gaggawar birkitota suka fuskanci juna  eye’s dinsu suka haɗu zuciyarsu yayi mummunar bugawa a tare laulausan tafin  hannunsa  taji yana yawo ajikinta  tun tana jin abinda yake  har bacci yayi nasarar  d’aukarta amman stil tana jinsa  , gabad’aya ya gigice irin gigicewar da bai taba yi akan kowace mace  ba, duk tunaninsa ya kau burinsa kawai ya samu biyan bukata sai dai  bazai iya  aikata komai daita ba…….

sama da awa biyu ya ɗauka yana romacing din  jikinta daren da yake jin  kasancewarsa  na  musamman  gareshi dan kuwa ji yake tamkar yana tare da matarsa ce  ina ma  zai iya daya yaki zuciyarsa ya  aureta kamar yadda ta bukata dan  yasan zai samu dukkanin wani kulawa daga gareta ,zata shayar dashi soyayya  ,a hankali  har ya samu natsuwa ya kwantar daita a saman faffadan kirjinsa yana sauke numfashi   …
hannunsa ya daura saman gashinta  yana shafawa  zuwa gadon bayanta haɗe da  kissing foring head d’inta  “acikin zuciyar tanweer kuwa addu’a take da Allah ya tsaida shi iya haka batare da ya kusanceta ba , Allah kasa wannan bawa naka ya aureni  dan zan sha  soyayya shi din na daban ne i love you adnan ta furta haka acikin ranta , rufe musu jiki yayi yana sake lumshe kyawawan idanunshi har bacci yayi nasarar daukarsa…..


A hankali ya bude  kyawawan idanunshi ya  daura akan  ƙaramin agogon dake ajiye akan abun gado,  karfe  takwas ya gani har  ta wuce da wasu yan mintuna tsaki yaja saboda ya makara idan akwai abinda ya tsana bai wuce makara gurin sallah ba , ya  kwantar daita tare da lullu’beta da bargo ya mirgina ya sauko  ya janyo towel ya d’aura ajikinsa cike da natsuwa ya  shiga   bathorrom , bathtube ya shiga ya tsaya ya soma sakarwa jikinsa ruwa, wankar tsarki yayi tukuna  domin tsaftace jikinsa sannan yayi wanka soso da sabulu bai dade ba   ya fito yana goge jikinsa yana kallon fuskarta da gashin kanta mai tsantse da sheki komai nata mai kyau  ya furta hakan a kasan ranshi ..

Jallabiya ya ciro wani design din yasa ya  karasa kibabben gurin sallarsa ya soma gabatar da sallah gabansa na faduwa , yana matukar fargaba da tsoron mahalincisa a duk sanda zai yi sallah sai yaji gaba-daya komai ya kwance masa ,yasan abinda yake aikatawa bai da kyau har yana jin tamkar ibadar da yake ma ba’a amsa ,yayinda take zuciyarsa ta kawar masa da wasi wasin data shiga ya dinga yi mata naci da karfafa gwiwar da   ana amsa har ya idar zuciyarsa rawa take ya  mike ya dawo inda take kwance tana sauke numfashi hannuwansa duka ya kai jikinta ya d’agota ta zube jikinsa ta lafe tare da turo masa karamin bakinta gaba , bakinsa ya kai cikin kunneta “ki tashi kiyi sallah lokaci ya tafi  mika tayi ajikinsa wanda ya haddasa masa jin wani irin shock , “uhm zanyi  zuwa anjima bacci nake ji jikina duk ciwo yake min ,gefen kunneta ya  ciza da dan karfi ta saki qara tana sake  shigewa jikinsa “dole ki tashi kiyi sallah me kika yi da kika gaji  ya k’arasa maganar yana busa mata iskan bakinsa take tsigar jikinta suka mike sake turo masa  bakinta  tayi tana kokarin buɗe bakinta taji yayi sama daita ya shige bathorrom daita ya sakata  a bathtube “ba’a lattin sallah a gidana oya kiyi alwala ya juya ya koma d’aki bayan kamar minti uku ya dawo hannunsa rike da jallabiya ya ajiye mata ya sake fita ..

Jiki a mace ta fito tana kallon inda yake zaune rigingine da gado ta isa inda taga dadduma ta tada sallah bayan ta idar    ta koma dayan bangaren da yake ta zauna “good morning ?”morning ya faɗa atakaice batare daya kalleta ba “ya kamata na koma gida ina so..
“zaki tafi nan da wasu awani dan zamanki bashi da  wani amfani , ya fada yana mik’ewa akan  katifa    bata sake cewa komai ba  ta zame ta kwanta tana runtse idanunta “komai cikin gadara da isa da nuna rashin kulawa ta fadi haka a kasan ranta …….

ya mike ya fita daga dakin zuwa  wani dakin , yayi shirin fita operation dinsa tsaf ya shirya cikin bakaken kaya  riga da wonda na suit  ya ɗauki bindigarsa pistor guda  har guda biyu ya soke ajikinsa yabi jikinsa da turare mai sanyi  kamshi  sannan ya  fito zuwa babban  parlou’n gidan  yana d’aura agogo a tsintsiyar hannunsa turus yayi ganin jabir kamil jubi da Anas zaune suna   tautaunawa akansa  ganinsa yasa  suka mike  suna kallonsa , kallonsu shima  yayi daya bayan daya yana tabe baki  sannan yace “ku kuma fa ? “a tare  suka bude baki mun zo ne akan wannan fitartaka  bama son ka fita aikin nan dan Allah ka hakura  ,”me yasa bakwa gajiya da magana ɗaya nifa wannan ba sabon abu bane agurina,”,Koda yaushe kana jayayya damu akan ra’ayinka  amman  akan  wannan   dole  mu fi karfin ka “karfin wa ? ya furta   yana musu wani irin  kallon kasan ido
“Duk ma abinda zakuce kuce but I must   face tanko gote zasu sake magana ya dakatarsu har zai  fita yaji jikinsa yayi masa  wani iri a hankali ya juya ya koma ciki ,kai tsaye d’akin  da tanweer take ya shiga ya hawo har saman  gado  ya shige jikinta yana kissing din bayan wuyanta jinta yake kamar matarsa ya zira harshensa cikin kunneta sannan ya kamo hannunta cikin  nashi “zani wani aiki mai mahimmanci da zarar na dawo zan kai ki gidanku  ajiyar zuciya ta sauke tana juyo ta zuba masa ido batare da tace komai ba shima bai sake furta komai ba wani iri suka ji ajikinsu a lokacin da kwayar idanunsu suka tsarke cikin juna ,bai sake cewa  komai ba ya fice tabi bayansa da kallo kamar ta hanashi fitar duk da batasan inda zashi ba , har lokacin su Anas   suna  tsaye ya nufi haraban gidan suka biyo bayansa   suna masa magana amman ko tari bai yi bare su saka rai zai amsa musu   , kai tsaye dakin ajiye makamansa ya nufa ya dibi harsashi da kudi masu yawa ya ɗauki keyn motarsa city ya  fito still suna biye dashi ya karasa inda aka tanada domin ajiye motocinsa  ya danna key din hannunsa ya bude  kofa mazaunin direba  ya shiga ya tayar mai gadi na ganin hancin motarsa ya bude masa, ya cilla motarsa waje  .

mutanen dake tsaye jiran fitowarsa suka mike tsaye ,kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tsaya   batare daya kashe motar ba ,yayi warning glass din motar ya  ciro bandir din kudi yan dubu day day ya soma  raba musu kamar yadda ya saba suka dinga  amsa suna zuba masa ruwan addu’a da samun nasara  yana kada kai ,sai  daya sallamesu sannan ya dauki hanyar zuwa donping estate   ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button