KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Taurin kai taurin kai mutun kamar mutanen farko duk abinda kaji ance ka barshi barinsa shine alkhairi duk kuma abinda zaka samu a duniya zaka bar shi jubi ya faɗa cike da taikaici da bakinciki taurin kan Jaguwa “wayyohlly Allah wallahi har na fara tausayawa yan’uwansa da halin da zasu shiga idan wani abu ya faru dashi kamil ya fada yana marairaice fuska , jabir yace ” wallahi tunda ya soma shirin aikin nan naji ajikina babu nasara “muyi masa addu’a kawai Allah ya dawo dashi lafiya domin shine karfin gwiwarmu bamu taba samun saɓanin ra’ayi ba sai a wannan lokacin inji cewar anas daya fi kowa shiga damuwa ” ameen suka had’a baki gurin fadar haka..
A hankali yake murza stearing yana tunanin yadda abubuwan zasu kasance gaba-daya ya gama tsara komai da yadda zai shiga ya fito har ya dauki titin da zai kai shi estate din ya karaso bakin get din estate din yayi parking ya ɗan dade sannan ya fito daga cikin motarsa yana gyara zaman suit d’insa kai tsaye gurin securitys din bakin get ya nufa suka gaisa a mutunce bazakace masa dan fashi ba bayan sun gaisa yace “ina son ganin Alhaji tanko gote ..
Daya daga cikin securitys ya leko daga cikin wani karamin daki yana dubansa ganinsa cikin shiga ta kamala ya koma ya zauna dayan yace “me ye sunanka na duba ko kana cikin list din masu son ganinsa ? Shiru yayi ya kasa magana yana ciza lip’s d’insa na kasa security ya sake kallonsa yana tambayarsa “uhm don’t worry bari na kirasa “better dan ba’a bawa Kowa damar shiga sai da izininsa wayarsa ya ciro kamar zai yi kira ya koma cikin motarsa ya zauna yana tunanin yadda zai shiga cikin sauki .
” Anas……..”
jabir ya kira sunansa yana zama a gefensa “na’am jabir Anas ya amsa jiki a sanyaye” everything will be fine naga duk ka damu tunda jaguwa ya bar gidan nan “dole na damu jabir ina jinsa tamkar danuwana bana son wani abu ya sameshi bana son na rasashi yayi mgnr kamar zai zubar da kwalla “jaguwa ba kamar sauran mutane bane , gabad’aya alamuransa akwai lisssfi ,yana da kaifin kwakwaluwa bazai bari mu rasa shi ba saboda yasan muna son shi “jabir nasan da haka nasan yana son mu duk duniya bashi da aminan da suka kai mu but bansan me yasa yayi irin wannan taurin kan ba ,nayi kokari fahimtar dashi nayi komai akan ya bar wannan aikin amman yaki ya kasa fahimtata jabir zuciyata na cike da tsoro yanzu idan wani abu ya sameshi adalilin tango gote ya zanyi da rayuwata ? “Anas kana tsoro da tausayinsa with reason nima zuciyata tana cikin damuwa amman abinda na lura dashi yana sane so yake mu rasa shi inji cewar kamil wallahi idan wani abu ya sameshi bazan taba yafe masa ba yayi maganar yana goge hawaye “ba haka bane kamil Anas ya fada shima hawaye ne cike da idanunshi “zai dawo zai dawo anas ya dinga maimaitawa zai dawo da kafafunsa domin shi din ba mutun bane kamar sauran mutane mutun ne mai matukar amfani ga rayuwar mutane yayi handling din matsaloli a rayuwar data gabata ina da tabbacin zai dawo da kafafunsa suka rungume juna suna kuka ..
Alhaji tanko gote zaune a cikin tangamemen parlou’n sa daya ji kayan more rayuwar duniya tare da manya abokansa kowane hannunsa rike da glass cup suna kurban ruwan win yayinda gabansu table ne dake dauke da kayan itatuwa kala dabam dabam,tun daga kan ginin gidan da tsarin da’aka bi dashi za ka san mamalakin gidan attajirin ne,gidan zagaye yaje da flowers sannan yafi Kowane gida dake cikin estate din kyau da tsaruwa .
shewa ne ke tashi acikin parlou’n “mutunen da zasu ce meye namu acikin lamuran kasar nan ina tunanin mutanen sun tabbata dakikai ne , domin daga kasar nan tamu har zuwa kashen ketari sunanmu ya zagaya sannan a san da zamanmu, maga Wanda ya isa yace meye namu acikin lamarin kasar nan bayan mune gwanati “wannan haka ne inji cewar Alhaji amadu dan iya wanda ke fuskantar alhj tanko gote “muna da tarin kudi muna da tarin mutane muna da hanyoyi daban daban akwai connection me muke so acikin kasar nan da bamu samu ba da har wasu zasu dinga cewa meye namu aciki ? “babu ma wanda ya isa domin mune gwanati kuma ko ana so ko ba’a so dole a dama damu kuma muyi abinda muke so “wannan gaskiya ne …
“waɗan kananun maganganun yasa nake gudun shiga siyasa Gara na tsaya iya haka tunda duk abinda nake nema ina samu sannan ina juya waɗan da nake so na bada umarni kuma abi inji cewar Alh Tanko gote suna cikin hirar wayar Alhaji tanko gote ya ɗauki kara ya mike sanye da bakin kaya wando da riga da hula ya ɗauki glass cup ya dauki wayarsa ya miko dogon coridor din gidansa sannan ya ɗauki wayar ya soma magana kasa kasa “ranka ya dade aka fada daga dayan bangaren na turo da kudaden yanzu haka yarona na bakin get din estste ” oooooo my god me yasa baka da fahimta ni da nace a wuce akai kudi banki shine zaka turo min yaro madadin ma ka kirani na turo body guad “am sorry sir gani nayi idan na turo kudin zaka fi maida hankali “haka ne kana da fahimta dan a daidai wannan lokacin ina tare da shi wanda zai saka hannu “to kagani sai ka bashi ayi agama komai dan so nake ya fito zuwa jibi dan Allah kasa a kashe wani a madadin falsa ..” shikenan a gama karkaji komai ” zan bada umarnin a shigo da yaron yanzu ya fada yana canza magana “you have to understand that you should know that what someone like us can do in this land be left ,ya maida wayar zuwa dayan kunnenshi tare da shiga karamin parlou’nsa ya bude window dining area “nasani ranka ya dade nasan zaka iya komai murmushi tanko gote yayi” ka kwantar da hankalinka komai zai tafi daidai cikin haka amaryarsa ta shigo tana taku day day ta nufi inda yake tsaye ta rike hannun daya daga cikin kujerun dake zagaye da dining yana ganinta yayi saurin “cewa I will call you later uhm alright “my dear ta matso jikinsa ya cire wayar a kunneshi yana rungumota jikinsa ya manna mata kiss tayi murmushi “darling har na fara kewarka da tunanin tsawon lokacin da zaka ɗauka idan ka tafi hong Kong dan Allah kar ka dade kamar sauran lokuta karka ɗauki lokaci mai tsawo bana son ka dade ka dawo da wuri duk yau sati ne fa da dawowarka “uhmmm gaskiya ne amman this time a round just 1 month zanyi na dawo nayi wata uku ban fita kowace kasa ba “really ? ya gyada mata kai “idan zan dawo zan biya ta itly “kai dan Allah tayi maganar a shagwa’be “dole na biya dan akwai abinda zai kai ni daga nan naga bilal ta soma tafiya tana farinciki yana biye daita abaya suka zauna akan farar kujera mai zaman mutun biyu har zai ajiye wayarsa ya tuna bai kira securitys ba ya soma ƙoƙarin kiransu kira ɗaya suka ɗauka “hello sir daga ɓangaren Tanko gote yayi shiru yana tsotsa keya yana ciza baki saboda bai tambayi sunan yaron da aka aiko gurinss ba iska ya furzar yaceb”akwai wani yaro yana ….
“Okay sir gashi nan ma “yauwa ku barshi ya shigo “okay sir ya katse kiran tare da janyo amaryarsa jikinsa “,zanyi missing din waɗan abubuwan ya kai hannu ya shafo qirjinta bata yi sanya a gwiwa ba ta kai hannunta ta soma wasa da sansar jikinsa kusan minti goma suna rungume da juna wayarsa ta sake ɗauka qara ya zareta ajikinsa yana ƙoƙarin d’aga wayar gabansa yayi wani irin muguwar faduwa yayi shiru rike da wayar ya kasa ɗauka babu abinda yake ji sai faduwar gaba.