KUSKUREN BAYA 1 TO 48

A natse yake murza stearing motarsa, lokacin daya shigo unguwar aguje su Anas dake tsaye a kofar gidan sukayi gurin motarsa suna murnar ganinsa, kanshi kawai ya girgiza yana murmushin sannan ya saita hancin motarsa get din gidan , kamil ya zundumawa mai gadi kira ganin zai ‘bata musu lokaci yasa suka shiga sauri saurin buɗe masa tafkeken get din gidan yana gama karasa shigowa ko gama daidaita tsayuwar motar bai yi ba suka hau kiciniyar bude motar suka fito dashi tare da d’aga shi sama suna ihun jin dadin sake ganinsa “Winner ooo winner Winner ooo winner ,Winner we don win ooo winner
Pata pata we go win forever winner suka nufi babban parlou’n gidan dashi suka zaunar dashi akan kujera mai zaman mutun uku , Anas ya karasa da sauri ya bude fridge ya d’auko masa power horse mai sanyi ya bude ya mika masa yana zama kusa dashi cike da tsananin murna jubi ya d’auko ruwa mai sanyi “,wayyo Allah nah jaguwa nasan kasha wahala ko da ganin yadda motarka tayi ” “babu wata wahala tunda gani a gabanku yanzu”
a tare sukayi dariyar jin dadi sannan sukace “Allah mun gode maka daka dawo mana da farincikinmu lafiya “shine abun godiya ya fada yana furzar da iska “gasky kai din na daban ne namijin duniya ,jaguwa ya ɗan lumshe idanunshi sannan ya gyara zamansa ya soma ƙoƙarin cire yar saman rigarsa Anas yayi saurin cire masa jubi ya dawo gabansa ya soma cire masa takalmin kafafunsa ya saura safa kallonsu kawai yake yana girgiza kai “kasan tun da ka bar gidan nan babu wanda ya sakawa cikinsa wani abu tsabar tashin hankali inji cewar jabir “
“uhmm bari jabir ban taba tsintar kaina cikin tashin hankali irin na yau ba wallahi da zarar na runtse idanuna sai inga kamar wani abu zai same shi anas ya fada yana shafa fuskar jaguwa ,ya ɗan juyo ya kalle shi yana haɗe rai “duk cikin murna dan ban maka kiss ba suka sa dariya gabadaya “yau fa akwai celebrate jubi ya fada yana dauko musu kwaban win ya jere a gabansu “kamar kuwa kun sani ,”ina zamu samowa jaguwa mai zafi data iya chilling fiyye da zahra ?
“ai babu wata mai zafi sosai data wuce zahra ita zan kira yanzu “zaro ido jaguwa yayi “lallai ku yanzu wannan shirmen ne a gabanku ni yadda zanga ammina nake tunani ba wannan shirmen ba “
“Ogbeni ejalo shaye jare Oti sele oppprr kpk Eyonla chuwale sir???????? se kinwa gbenusi no be atenu ” zaka gun ammi amman amman dole zahra zata yi aiki “
A hankali Anas ya kira su eku remo cikin minti goma suka karasao suka shiga fito da buhuhun kudadde da jaguwa yazo dasu suna shigowa dashi daya bayan daya , yayinda su Anas ke zaune suna mamaki yadda har ya iya rabo tanko gote da wadan nan makudan kudaden shi kadai , cikin minti da bai wuce goma ba sukaji mai gadi yana kwankwasa kofa jubi ne ya tashi ya tsaya daga bakin kofa ya bude , cikin yaren turanci mai gadi yace “akwai wani bako da yake ta zuwa gidan nan yau shine zuwansa na biyar baya samun nasarar ganin oga yana fama da matsalolin rayuwa ne gashi yana da yarinya mara lafiya mai kimanin shekara goma tana igondo general hospital ,likitoci sunki bata kulawa sakamakon rashin kuɗi , kafin jubi yace wani abu jaguwa yayi gyaran murya , juyowa jubi yayi a hankali ya dawo inda suke ya tsaya yana duban jaguwa nuna masa wata yar kamara jaka mai zip yayi da hannunsa “zuba masa adadin da zai cika jakar nan ka bashi “yesssss boss an gama Allah yaja da nisan kwana ,jakar ya cika da kudi yayi ziping dinsa ya mikawa mai gadi da hanzari mai gadi ya amsa jakar ya rungume ya juya ya nufi kofar waje ya mikawa mutumin , mutumin na ganin kudin gabad’aya ya rude ya gigice ya soma wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya,lallai baa rasa na allah koina kuma yadda aka bashi labari wannan matashin mai tsatsanin kirki da tausayi haka ne, take ya nemi mai gadi da yayi masa iso gurin mai gidan domin yi masa godiya , amman mai gadi yaki saboda sanin da yayi wa jaguwa baya son godiya ko kyauta yayi maka kace ka gode sai yace ka godewa Allah ,duk da ban samu ganinsa ba tabbas zan dangwama ina yiwa rayuwarsa addua domin allah ya buda masa kofofin farinciki kamar yadda yayi min , iri mutanen da ake so kenan masu taimako dan allah”
” karka damu ba kai ba duk wanda kaga yana bukatar taimako kana iya masa hanya wannna gidan gidan masu tallafawa rayuwa marasa shi ne da marasa galihu a haka nasan shi da zaka zo kofar gidan a duk safiyar allah zakayi mamakin yadda mutane suke shawagi kayi masa adduar kamar yadda ka kudurta domin shine zai zama tsani na rayuwarsa “mutumin ya sauke numfashi ya kama gabansa yana masa addua.
Duk yadda yake kallon buhubuhun kudaden dake gabansa hakan bai sanya shi jin farinciki ba, waɗan nan makudan kudadde daya amsa daga Tanko gote ba zai taɓa goge abinda yayi masa a shafukan rayuwarsa ,sannan bazasu taɓa maida masa jin dadin daya rasa a shekarun da suka gabata ba, fuskar ƙaramar kanwarsa ne ya shiga yi masa gezo a lokacin da numfashinta na karshe ke shirin barin gangar jikinta tana kallonsa hawaye na turereniyar zubowa daga kwarnin idanunta bakinta na amai jini ,yayinda mahaifinsa da mahaifinyarsa ke manne da jikin bangon daki sun dawo tamkar matattu a tsaye tsabar firgici da tashin hankalin halin da diyarsu ke ciki kukan zuci dana zahiri suke a wannan lokacin har rai yayi halinsa wanda sanadiyyar haka zuciyar mahaifinsa ya buga take shima yace ga garinku …….”
“Anas ya dafa kafad’ansa saboda yasan abinda yake tunani “ka manta da abinda ya faru, jiya ta wuce mu fuskanci yau samun waɗan kudadden kadai ya isa ya goge abinda ya faru a zuciyarka sannan waɗan nan kudade zasuyi maka abinda basu yi maka a da can baya ba “
“bazasu yi ba Anas rayuwar mahaifina data kanwata sun fi min waɗan nan kudadden mahimman … hatta mahaifiyata da zata san abinda ke gudana a rayuwata zata iya saka hannu cikin raba Tanko gote da duk wasu masu hali irin nasa daga duniya “me yasa bazaka ɗauke shi daga duniyar gaba-daya ba kowa ya huta ?inji cewar kamil , girgiza kai jaguwa yayi sannan ya fashe da wani kuka mai cin rai da ban tausayi yana tuna rayuwar da suka yi a baya shi da yan’uwansa rayuwar kunci da talauci da rashin galihu , a hankali komai ke dawo masa gabad’aya sukayi kanshi suna bashi baki da hakuri “