KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Tana ganin shigar sa ta mike ta zube saman gado tana sauke ajiyar zuciya , wanka tsarki ya fara yi sannan ya haɗa ruwan dumi ya zuba turaruka wanka kala kala masu sanyi kamshi dan kawar da kamshin turaren zahra a jikinsa sannan ya shiga cikin ruwan ,jin dumin ruwan ya ɗan sanya shi jin natsuwa a cikin zuciyarsa , a hankali zuciyarsa ke masa faɗa “me yasa adnan ka biyewa yarinyar nan kai daya kamata ka mata mugun duka har sai ta fita haiyacinta shine ka bige da biye mata? girgiza kànshi yayi a filli yace “duk sharrin wannan dan iskan ne amman zan san abun yi dan dole na yakice zahra daga rayuwata domin samun kwanciyar hankali.”
Kusan minti talatin ya ɗauka a bawon wanka yana cuta jikinsa sannan ya fito yana taku da kyar kugunsa d’aure da towel yayinda hannunsa ke rike da wani karamin white towel yana goge sansar jikinsa ,cike da karuwanci tabi jikinsa da wani mayataccen kallo sannan ta tsurawa kan nipple’s dinsa ido ita tana son su suna matukar mata kyau da ɗaukar hankalinta, lumshe idanunta tayi a daidai lokacin da ya juya mata baya ya ci-gaba da goge jikinsa muryarsa a sanyaye yace “kwanciyar me kike yi ya kamata ki tashi ki shirya ki wuce “?
“Anan zan kwana ta bashi amsa tana gyara kwancinyarta a fusace ya juyo yana mata wani irin kallo “ki tashi ki kama gabanki ya fada yana sake juya mata baya ya ɗauki body lotion yana shafawa jikinsa bayan ya gama ya dauki kwalban turare ya shiga fesawa jikinsa da bayan kunneshi ,ita kuwa murmushi tayi tace “haba adnan wai me yasa kake min haka ?”me yasa kake son guje min?
” kaki ka tsaya mu fahimci juna kullum da zarar mun gama sex ka dinga Allah Allah na barka , nifa har ga Allah nake sonka kuma da aure ” ta karasa maganar kamar zata yi kuka “
Shiru yayi mata yaki cewa komai ya cigaba da abinda yake ta sauko daga kan gadon ta tsaya a bayansa har lokacin babu komai sanye ajikinta tana kokarin haɗe jikinta da nashi
ta kai hannunta jikinsa tana kokarin kifesu a qirjinshi dan murza kan nipple’s dinsa yayi saurin juyowa tare da tsareta da kyawawan idanunshi yana mata gargadin abinda take son aikatawa bata damu da irin kallon da yake mata ba ta kai yatsanta kan nipple’s dinsa zata soma zagayewa taji ya ɗauketa da wasu maruka guda biyu ajere tasa tasa ..
Saurin dafe kuncinta tayi tana fidda numfashi da kyar gabad’aya marin ya dimautata ya gigiceta da kyar ta samu ta sauke numfashi da karfin gaske idanunta na kanshi “minti biyu kawai na baki ki tattara abinda kika san naki ne a dakin nan ki bar min gida kar na sake ganin kafafunki ya karasa maganar a fusace sannan ya soma daga zara zaran yatsun kafafunsa ya isa gaban wordrobe dinsa ya bude ciro wasu kananan kaya bakake wando masu taushi da kyau ya soma shirya kanshi.
jikinta a sanyaye ta dauki rigarta ta saka tana kallonsa har ya gama shirinsa tsaf bandir din yan dubu dubu guda biyar taga ya dauko ya watsa mata “kije dan Allah ki bar rayuwata bana son damuwa idan ina bukatarki zan nemeki da kaina “naji zan tafi amman dan Allah ka dinga ɗaukar kirana ..”
“Bazan miki alkawari ba saboda ina da abubuwan yi idan bukatar ɗauka yayi zanyi “bata ce masa uffan ba ta dauki jakarta batare da ta dauki kudin ba a dan zafafe yace “kudin fa”?
Ta juyo kamar zatayi kuka “bana bukatar su dan nafi bukatarka dasu …”tana gama fadar haka ta sake juyowa idanunta cike da ruwan hawaye, ta bude kofar d’akin zata fita hannunsa ya kai ya shako wuyanta ya dawo daita cikin bala’in da tashin hankali ya amshi jakar hannunta ya kwashe dukan kudin ya zuba mata cikin jakarta , tayi shiru kawai tana kallonsa kamar ta daura hannunta bisa kanta ta fashe da kuka , yanayinta ya bashi tausayi sosai kamar ya lalla’bata su rabu lafiya sai kuma yaga hakan bai dace ba kamar wata dama zai sake bata..”
Muryarta a raunane tace “meye laifina adnan da kake wulakantani ? “shin laifi ne dan zuciyata ta soka ? ta k’arasa maganar wasu zafafan hawaye na zubowa a saman face d’inta, girgiza mata kai yayi yana furzar da iska sannan ya motsa lip’s d’insa a hankali “laifinki daya zahra da kike takurawa rayuwata alhalin kinsan ni din mutun ne da bana son damuwa ” sannan baki da wani sauran mutunci da darajan da zan soki zahra ,gaskiya ɗaya ce wallahi zahra bana sonki koda kuwa akwai budget din soyayya arayuwata bare babu mafi mahimmanci abu arayuwata shine ahlina “
ba iya soyayya kawai zata iya da zuciyar jaguwa ba Bare lalacewata bata kai na amincewa auren mace irinki ba ,”zahra da ƙaruwar gida da karuwar waje akwai bambamci idan aure kike bukata me zai hana ki koma gaban iyayenki ki tuba Allah zai duba lamarinki ya baki wanda yafini wanda zai soki da d’aukacin rayuwarsa amman batu na soyayya ko aure tsakanin zahra da adnan babu…..”
“To mu’amular fa ?”idan bazaka aureni ba ka barni na rayuwa da kai shi kadai zai sanyaya zuciyata sannan zai sa na dangwama cikin farinciki “shima bazan yi alkawari ba dan ita kanta zinar ina son na daina shiyasa kika ga ina gujewa haduwata dake ,ta durkushe a gabansa “karka min haka adnan karka juya min baya ka taimakeni ka taimaki rayuwata wallahi bazan iya rayuwa babu kake “enough Zahra ya fada a tsawace “Haba me kike son nace miki kinga tashi tashi dan Allah yadda taga ya soma birkicewa yasa ta tashi da sauri tana fuskantar shi ido cikin ido yake kallonta”Ni ne na samo having sex dake ? “Ko ni ne na baki ticket din fitowa yawon duniya ?”ko ni nace dole sai kin soni ? yayi mata duka a lokaci tayi shiru hawaye na gangaro mata “kin yi shiru ki bude baki ki bani amsa yayi maganar yana zaro mata ido tayi saurin girgiza masa kai”okay tunda kinsan bani bane me yasa zaki ce kar na miki haka kar na juya miki baya ?”daga yau Karki sake tunkarata da batun soyayya bare wani aure okay ?”oya out idan kika sake tunkarata sai ballaki idiot Kawai ..
Tana gama jin abinda ya faɗa ta juya da sauri ta fito daga d’akin tana goge hawayen idanunta a bakin kofar suka kusan ci karo da Anas ,da sauri ta wuce shi ya biyo bayanta yana kiranta “zahra! zahra !! amman ina taki tsayawa ta wuce tana kuka yayi saurin biyota ya sha gabanta “plz Ki tsaya ki saurareni menene? ” me yayi miki kike kuka plz tell me ko akwai abinda zan iya yi ” muryata cike da kuka tace “tabbas nayi kuskuren afkawa cikin soyayyar adnan “
“Wani irin mutun ne shi nayi iyakar kokarina akan soyayyarsa amman sam yaki fahimtata na rasa yadda zanyi adnan ya fahimci irin matsanancin soyayyar da nake masa gabad’aya zuciyata ta kasa hakura dashi ka faɗa min me ya kamata nayi ya aure ni ? duk Sanda zamu kasance tare sai ɓacin rai ya biyo baya” why !why!! ? Ka faɗa min abinda ya kamata nayi ?”Ni kaina babu wannan tsarin arayuwata ban shiryawa aure a yanzu ba amma na rasa dalilin da yasa na nacewa mutumin da bai ɗauki kowa da mahimmci ba ? gabadaya ta fita haiyacinta sai maganganu take faɗa masu taba zuciya “kiyi hakuri muje muyi magana aciki “babu inda zani dan nasan kona koma wani sabon bakinciki zai kunsa min , kawai ka barni na tafi abuna ajiyar zuciya ya sauke tare da matsawa gefe ya bata hanya dan ta wuce kamar yadda ta bukata dan shima yasan ko ya maidaita sabon bala’i za’a yi a hankali ya juyo ya nufa cikin gidan
Yana ƙoƙarin tura kofar dakin jaguwa ya fito yana ciccin magani tamkar wani jinin saurata.