KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“me ka yiwa yarinyar mutane jaguwa ?’,me tace nayi mata yayi masa tambayar atakaice , cikin natsuwa ya raba ta grfenshi yayi gaba “ko bata faɗa min ba nasan kayi mata wani abu shiyasa ta fita cikin fushi da ɓacin rai dan Allah ka dinga sausauta yarinyar nan tana bala’in qaunarka “kace mata daga yau ta daina son adnan dan babu wani amfani da zai mata ya karasa maganar yana ci-gaba tafiya ” Anas ya biyosa da sauri “na rasa dalilinka nakin yarinyar nan bayan irinsu ne kawai zasu iya rayuwar aure da irinmu, ko kana tunanin akwai wata mace mai mutunci da daraja da zata iya da irin rayuwar da muke ?
Jaguwa ya tsaya cak tare da juyowa ya fuskanci Anas sannan ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa ya zubawa Anas idanunshi yana kare masa kallo tsaf “kai kake ganin haka amman lalacewata bata kai na auri mace kamar zahra ba, karka manta inda muka tsinto zahra da irin rayuwar da take duk gidan rawan fela kowa yasan wacece Zahra, nasan nima mai tarin zunubi ne agurin Allah amman ta nemi mijinta a gaba adnan baya sonta kuma bazai taba sonta a rayuwarsa ba kai gabad’aya ma babu wata soyayya a tsarin rayuwata “
“Wannan kuma karya ne dan da alamun ma a yanzu zuciyarka ta kamu da soyayyar diyar Minister of health dake cikin gidan nan “dariya jaguwa yayi wanda ya bayyana tsantsar kyawunsa sannan a hankali ya sake gyara tsayuwarsa ,fuskarsa cike da mamakin jin furucin Anas “,this is rubbish anas what are you try to say ? wannan maganar naka ba gaskiya bane abinda nake son ka sani zuciyar Adnan amad tayi nisa a kiyyaya babu wani mutun mai darajan da zan so kamar ahlina idan ma soyayya ce wannan yarinyar tayi min karama Anas , kuma idan duk duniya zasu taru akan na sota itama bazan sota ba “ya wuce ta gefensa ya soma tafiya da baya baya kamshin turarensa na tashi ya nufi dakin da tanweer take ya daura hannunsa akan handle din kofar ya murd’a ya shiga dakin Anas bai daina kallonsa ba har ya karasa shigewa dakin ya maida kofar ya rufe ..”
Cikin natsuwa yake kallon inda zaune take akan kujera ,juyar da kanta gefe tayi kamar bata ganshi ba , ya jingina jikinsa da bango dakin yana Kallonta ,sosai yaga ta rame akan ranar daya d’aukota sai dai fuskarta tana nan da kyawunta …”
ganin taki kallon inda yake yasa shi takowa a hankali ya tsaya a gabanta shiru taki dagowa ta kalleshi ya cire hannunsa daya acikin aljihun wandonsa tare da d’ago ha’barta ya tsura ma kwayar idanunta nashi idon yana Kallonta , da ido yayi mata alamar taci abinci ? bata fuska tayi cikin son nuna masa abinda yake son sani bai shafesa ba, furzar da iska yayi yana tabe bakinsa sannan ya cire hannunsa ya buɗe kwanon tangaran din dake ajiye akan table ,abincin na nan kamar yadda akawo shi ya waigo ya kalli inda take a hankali ya maida murfin ya rufe “you don’t eat ?why don’t you eat?” I don’t want to eat food in this situation “why ? ya tambayeta idanunshi na kanta kamar zai had’iyeta “I’m not hungry”bakya jin yunwa ? ya sake tambaya ta yatsina fuska cike da shagwa’ba.
“yarinya idan kika sake ɗaukar lokaci baki ci abinci ba zaki mutu just for nothing yayi maganar tare da zama a bakin gado ya fuskanceta “tun safe rabon da ki sanyawa cikinki wani abu hakan fa babu kyau “it’s not good for your health okay ? Ya kamata kici wani abu saboda taimakawa rayuwarki a matsayinki na likita kinsan yunwa na daya daga cikin abinda ke saurin kashe dan adam ko ba haka ba “?
shiru tayi taki cewa komai sannan taki kallon inda yake “you need to eat my friend so that you can survive ya karasa maganar a tsawace “go and eat I’m to talking to you ………..”
take jikinta ya dauki rawa gabanta ya shiga faduwa a hankali ta sake juya masa baya taki bin umarninsa kamar yadda ya bukata tana sheshekan kuka , gabad’aya hankalinta ya karkata zuwa gida tana son ganin iyayenta bata ga amfanin zamanta tare dashi ba alhalin jikinta na bata iyayenta na can cikin tashin hankali, wasu hawaye masu zafi suka gangaro mata a hankali ya sausauta muryarsa cikin tsigar rarrashi “you need to eat so that you can have strength because you don’t know the task ahead right? you need food to live plz duk yadda yayi mata magana da tsigar rarrashi amman sam taki ci sannan taki magana sai kuka take tana ciza lip’s dinta .
a can bangaren hajiya Zainab kuwa itama kukan take saboda jikinta na bata diyarta na cikin damuwa ,ta mike daga zaune da take ta shiga zagaye d’akinta zuwa babban parlou’n gidan ta wuce matar danuwan mijinta da suka kawo musu ziyara tare da yarinyar su zuwa haraban gidan tana baza idanunta gani take kamar zata ga diyarta daga sama matar danuwan Alh Abubakar da suke uwa daya uba daya ta biyo bayanta ta rungumeta ajikinta “kiyi hakuri inshallahu za’a ganta “jikina na bani tanweer tana cikin damuwa Allah kasa basu ma yarinyata wani abu me suke bukata daga garemu su kira mu su tambayi duk abinda suke so wallahi a shirye nake zan mallaka musu duk abinda nake dashi muddin zasu dawo min da farincikina …”
Tunda Hajiya zainab ta fito hankalin minister ya rabu gida biyu wani bangaren ya koma gurinta yayinda wani bangaren ke gurin d’an’uwansa da suke tare “Haba Abubakar taya irin wannan babban abun zaifaru ace bazaku sanar damu ba ‘yan uwa? Wannan wace irin rayuwace ta rashin zumunci kuka zab’a kai da zainab ?”. Matashin Dattijon yayi maganar cike da b’acin rai yana binsu da kallo,
kallo d’aya zaka ma dattijon matashin kaga kamanni sosai da suke da Alh.Abubakar sai dai Ko a fuska zaka fahimci ya girmemishi.
“Kayi hakuri yaya Walh tallahi kaga dagani har zainab bama cikin hayyacinmu tunda wannan tashi hankalin ya faru, gaba d’aya Zainab bataci baresha ni kaina Walh bazan iya cema when last nasa abu a cikin nan nawa ba” Alh.Abubakar yayi maganar cike da damuwa wacce kallo d’aya zaka fahimci damuwa a kan fuskarshi me tsanani dan duk yayi baki ya rame kamar ba Minister of Health ba.
“Allah sarki Ubangiji Allah ya fito mana da ita lafiya dan walh tashin hankali ya zama dole. To wai basu Kuma kiranku Ko suna buk’atar k’arin kud’iba?”. Yayi maganar cike da tausayin d’an uwansa.
Girgiza mishi kai Alh.Abubakar yayi. “Kod’aya walh! Ni da zasu kira Ko duka dukiyata ce saina had’a daita su dawo da munda Tanweer”. Ya k’arasa maganar cikin rawar murya wacce ke k’ara fitar da damuwar shi. “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un”. Alh.Usman yayi maganar cike da tausayawa nan ya shiga lallashin Kanin nasa tilo musamman ya jima bai ganshi ba kasancewar shi a Arewa yake da zama kaduna State da iyalansa hakan yasa bai sama labari ba sai da aka kwana biyu, yaji ciwo amma yanzu jin zantukan d’an uwansa yasa yaji jikinsa ya mai sanyi gaba d’aya a tare suka koma cikin parlou’n inda diyar Alh Usman rukkaya ke kwance akan kujera mai zaman mutun uku .