KUSKUREN BAYA 1 TO 48

yayinda a hankali motar jaguwa ke sharara gudu akan titin onipan a natse ya d’an juyo gefen da tanweer ke zaune shiru sanye da doguwar riga pinky colour ta yane kanta da mayafi baki haka ka’fafunta sanye suke cikin baby shoe baki masu matukar kyau tsintsiyar hannunta d’aure da agogo fata baki duk jaguwa ne ya bata su a wannin da suka gaba tare da yi mata albishir din maidata gidan iyayenta , kayan sun amshi jikinta sosai kamar dan ita aka yisu .
a hankali itama ta juyo cike da natsuwa fuskarta d’auke da murmushin jin dadi zata gida taga iyayenta cikin sa’a shima ya Kalli Inda take idanunsu ya tsarke cikin juna wani irin bugawa qirjinsu yayi , alokaci d’aya sukai shiru tare da tsurawa juna idanu gbdy suka kasa d’auke idanunsu .
a cikin zuciyarsa yake yabawa kyawunta “hakika tsarki ya tabbata ga ubangiji daya halicci wannan yarinyar , kallo d’aya zaka mata kasan kyakkyawa ce ajin farko .”
a natse ya d’auke kyawawan idanunshi acikin nata sakamakon ganin yadda ta kafe shi da nata idanunta da suka wadatu da zararan gashi Ido gashi ko kifta su bata yi shi kuma mutun ne da bai fiyye son kallo ba bare kallo irin nata dake saukar masa da kasala tare da sha’awa me tsayawa arai , dan nan take kallonta kesa yanayin mutun ya sauya batare daya shiryawa hakan ba.” kasa d’auke idanunta tayi daga kallonsa saboda baiwar kyau da Allah yayi masa ta sha jin mutane na yabawa kyawunta haka zalika idan ta Kalli kanta a mirrow tana tabbatar da abinda mutane ke yawon fad’a akan tsarin jiki da kyawunta sai dai ko kusa bata kai shi komai ba , dan idan tana gabansa raina komai nata take domin gani take ya fita komai bama za’a a had’a ba .
muryarsa a kasalance ta fito kmr baya son yin magana “ki daina yiwa namiji irin wannan kallon domin duk macen dake kallon nmj haka yana nuna alamun bata da cikakken tarbiya ,mace da kunya da kauda Kai aka santa ” ya qarasa maganar yana jan dogon tsaki dake ‘batawa duk wanda akayi dominsa rai , runtse idanunta tayi gam tana zance zuci “nice mara tarbiya sannan mara kunya ?”tayiwa kanta tambayar ranta na quna da tuttukin bakincikin daya maye gurbin farincikin dake kwance a fuskarta , idan akwai abinda ta tsana a rayuwarta bai wuce wulakanci irin wannan ba , kusan second biyu tayi idanunta na runtse kamar bataji abinda yace ba , cikin natsuwa taje d’aura laulausan tafin hannunta saman kushin din kujera domin gyara zamanta taji ya sauka akan laulausan hannunshi nan take yaji qirjinsa ya cigaba da bugawar da yake , itama qirjinta ya shiga dukan uku uku dan wani irin zirrrrrrrrr taji lokacin da hannunta ya sauka a nasa .
ya sauke wani zazzafan ajiyar zuciya da numfashi alokaci d’aya ,
a hankali tayi karfin halin d’auke hannunta dake saman nashi a dalilin jikinta dake kyarma ta soma magana cikin fushi da bacin rai “karka sake furta min wannan kalmar domin kuwa kallon nmj bashi ke nuna rashin tarbiya ko rashin kunya ba dan haka bana son sake jin kalmar gareni domin ni din macece me tarbiya da kima idan Kai baka ganin kimata akwai dayawa masu gani ta k’arasa maganar hawaye na gangarowa akan quncinta ,ta sake kawar da idanunta sosai tana goge hawayenta dake tsiyaya “wani kallon banza ya watsa mata mai hade da harara ” lallai yarinyar nan ma ta sameshi yadda ya kamata ,shi take maidawa magana ?ai duk laifinka ne da baka gyara mata zama ba ka tsaya kana tattalinta, yarinyar da yaka mata ka wulakantata ta hanyar keta mata haddi tunda abinda yasa ka d’aukota kenan ” zuciyarsa ta fad’a masa
haka numfashi ya fesar yana jin zafin acikin zuciyarsa , sam bai ji d’acin Kalmar daya fad’a mata ba, dan haka yayi tunani sake musguna mata jikinsa a sanyaye ya Kai bakinsa daidai saitin kunnenta yana sake watsa mata kallon bazan tayi saurin gocewa tana furzar da numfashi tare da hura hanci sannan taki waigowa ta Kalli Inda yake bare taga kallon banzar da yake mata zafin da zuciyar ke yi yasa wasu hawaye masu zafi da ciwon sake zubo mata ita daya kamata ya farantawa adalilin zata tafi ta barshi tafiyar da ba lallai su Kara haduwa ba kamar yadda ya sha fad’a mata .”
ya matso kusa daita Sosai yana busa mata iskar bakinsa , bakinciki da takaici yasa tayi saurin janye jikinta daga nashi tana kallon gefen titi ,shiru yayi yana kallon gefen fuskarta numfashi ma da kyar take fesarwa bai san yadda akayi ba ya sake matsowa sosai ya d’aura kanshi a saman kafad’arta ,shiru tayi taki motsi sannan taki waigowa, jin shiru taki motsawa ya tabbatar masa da lallai fushi tayi dashi tsintar Kansa yayi da rashin jin dadin yanayinta can Kuma ya furzar da iska had’e da jan dogon tsaki “me yasa zan ji babu dadi araina dan tayi fushi dani ?ya jefawa kwakwaluwarsa tambayar ” Kiran daya shigo wayarsa ya katse masa zance zucin da yake bare ya samu amsa daga wankakkiyar zuciyarsa , ya lalu’bo wayarsa daga cikin aljihun wandonsa ya mannata a kunnensa batare daya duba me Kiran ba.
jin sautin muryar amminsa ce yasa shi barin jikinta da hanzarinsa dan yana expecting jin dadd’adan labari daga bakinta dan jiya da sukayi waya yake sheida mata ya kamata ace yaron dake son shefiqa ya turo iyayensa ayi maganar aure ,a lokacin ammi ta tabbatar masa da zatayiwa shafiqa din magana , ai kuwa abinda yake expecting ji shi ta fara fad’a masa yasa wayar a hands free ya d’aura wayar a kafad’arsa ya jingina jikinsa sosai a kujera.”