KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“yaron nan gali wai zai turo iyayensa ranar lahadi tare da saka rana gbdy ” murmushi jaguwa ya saki na farinciki yana cewa ” Allah ya nuna mana ranar lafiya so nake na aurar dasu gbdy kafin nawa auren . “a’a ban yarda da wannan tsarin ba ,idan ma son samu ne a had’a auren da naka ba qaramin farinciki zanyi ba “shinkenan ammina yadda kikace haka za’a yi bani da za’bin da ya wuce naki zanyi k’okari naga anyi auren da nawa sai dai ki qara addua akan wanda kike min Allah yasa na samu me sona tsakani da Allah “zaka samu da iKon allah dan baka da makusar da wata diya mace zata kika ni dai fatana kayi kokari ka cika min alkawarina Ina son kyakkyawar suruka me nagarta idan son samu ne wacce ta fika kyau”. wani narkakken murmushi ya saki kamar yana gabanta kana yace “kin samu kin gama ammina dan sai na kawo miki irin matan hurul’ain dan irinta kike bukata ta zama surukarki ya k’arasa maganar yana dariya tare da matsowa ya kamo yatsun hannun tanweer ya rike gam cikin nashi yana massaging a hankali , itama ammi dariya take sosai tana sake tabbatar masa da hakan take so , ita Kuwa tanweer gbdy ranta a dagule yake sbd haushin abinda yayi mata da Kuma haushin maganarsa da mahaifiyarsa dan duk tana ji abinda mahaifiyarsa ke fada masa sannan tana Jin amsar da yake Bata cike da fushi ta soma k’okarin zare hannunta cikin nashi tana sauke wahalalle numfashi sai dai ta kasa kwatar hannunta dan haka tayita jan tsaki babu kaukautawa ganin hk yasa yayi sallama da ammi tun kafin ta tunhumeshi ,ya katse Kiran yana cewa “ki daina wahalar da kanki bake ba ko namiji dan’uwana na rike bai Isa ya kwace ba bare ke ” ko kina tunani ni din irin lusaran samarinkanki ne da zaki gwada karfi dani ..?”ya karasa tmyr yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa.”
danne abinda taji ya tsaya mata arai tayi tana zance zuci” shi take mutuwar so amman shi burinsa kullum ya cusguna mata tare da nuna mata ita din ba kowa bace , tunda suka had’u yake kyautata mata ta hanyar bata kulawa sai dai a fahimtarta bashi da burin daya wuce ya ‘bata mata rai ta hanyar fada mata baqaqen maganganu . tasan ba lallai ta zamo test dinsa ba amman at least itama tana da daidai nata kyau sama sama ta dinga fidda numfashi tana danne damuwarta “dan Allah direba ka taka motar nan da sauri Ina son d’aura kwayar idanuna akan iyayena wad’anda suka zamo min bango abun ma jingina kuma farincikina nasan suma nice farincikinsu rashina baqaramin babban tashin hankali bane garesu suna can suna mararina”
“shiiiii…….” munafurcin banza kawai kina dai son kije kiga wad’an can rubabbun samarin naki barin wancan me murya gangarin da bata dadin saurara “ya Allah ta furta dan sai lokacin ta fahimci a fili tayi maganar , muryarta qasa qasa tace “kafa san irin maganar da zaka dinga fad’a min dan ni din ba motar haya bace bare kayi tunanin Ina tara kwashe kwashen samari Ko da yake yau ne final kasancewata da kai zaka mayardani gidanmu na gode da taimako ta k’arasa maganar tana murgad’a masa ‘karamin bakinta “karki gode min ki godewa Allah sannan na fiki jin dadin zan rabu dake na huta da ganin wannan fuskartaki .
muryarta a raunane tace ” aikin banza kawai Nima daga yau ai bazaka sake ganin ko me kama dani bane tayi mgnr tana jan dogon tsaki shiru yayi yana ciza gefen lips dinsa can kuma ya murtuke fuskarsa yace “wannan shine Karonki na farko Kuma Ina son ya zamo Karo na karshe karki yarda ki sake min tsaki a rayuwarki , ko ni sa’anki ne da zaki dinga ja min tsaki yayi tmbyr yana murd’e mata hannu qara ta saki mara sauti tare da cewa “a’a kayi hakuri hannuna zafi bai mata magana ba ya sausauta rikon da yayiwa hannun tare da bud’e tafin hannun ya tsurawa tsakiyar hannunta kyawar Idanunshi yana kallo , a hankali ya d’aura dayan hannunsa ciki ya fara mata tafiyar tsutsa wani irin tsalle hade da bugawa zuciyar tanweer yayi take tsigar jikinta suka mike kasa cewa komai tayi illa numfashin da take saukewa da kyar tare da jin wani sauyi na dabam a sansar jikinta. Shima wani irin abu yake ji yana masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa wani tunani yayi gara ya sake musguna mata kafin su rabu ,wayarsa ya d’auka ya soma danne danne bayan kmr second biyu ya kira sunan eku remo dake tukasu .”eku ka duba wayarka na tura maka sako eku yace “noted boss ya tura wa su anas dake bayansa Sako kamar yadda ya turawa eku sannan ya koma ya jingina bayansa ya runtse idanunshi ..”
motar bata tsaya a koina ba sai gaban katon get din Rita Lori hotel dake onipan , get din already a bud’e yake kamar Koda yaushe security’s ne tam ciki da wajen hotel din saboda manya masu kudi da kusoshin gwanati dake zuwa da manya manyan yan fashi da makami , gurin fitowa daga ciki hotel din dabam haka zalika gurin shiga dabam , eku ya sanya hancin motarsa cikin Rita Lori, d’aya daga cikin security’s din gurin ya mike da sauri ya zare karfen da sakale Wanda ke bawa mutun damar shiga, eku ya samu guri ya soma k’okarin parking adaidai lokacin da motar alqali danasu anas ya shigo
haraban hotel ne dake da bangare dabam dabam dan shakatawa sam tanweer bata fahimci Inda suke ba saboda ranta dake ‘bace .
a natse jaguwa ya fito ya zagayo bangaren da take zaune ya bud’ mata kofa “fito ko “.ya fad’a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa
ta yunkura a hankali ta fito tana jiran ta ganta a haraban gidansu kawai ta ganta a Rita Lori hotel a hankali ta dinga bin gurin da kallo qirjinta na dokawa da matsanacin karfi tana son gano Inda take bata Ankara ba taji ya riko tsintsiyar hannunta ya fara tafiya daita zuwa cikin had’ad’d’en club din dake ciki, banda sautin kidi da waka baka Jin sautin komai “Ina ne nan ka kawoni ? tayi masa tambayar muryarta a tsarke “gurin shakatawa yayi maganar a dake yana cigaba da tafiya daita yayinda har lokacin hannunta na cikin nashi jikinta na rawa taja ta tsaya qirjinta na wani irin bugu fiyye da kaida juyowa yayi ya tsaida idanunshi a kanta take ya fahimci damuwar data shiga adalilin ganinta a Inda suke “gida mukayi da Kai zaka Kai ni me yasa zaka kawoni nan ?shiru yayi kawai yana bin qaramin bakinta da kallo yana jin kmr ya rungumota jikinsa ya hau sotsan lips dinta .” ni gaskiya gida nake son zuwa ba nan ba ka Kai gidanmu tayi maganar kamar zatayi kuka dan tuni hawaye sun gama cika mata Ido kafin kace me hawaye sun shiga turereniyar zubowa har da shesheka hankalinsa ya tashi dan hk cikin tsarkewar murya yace “Kinga dan Allah ki kwantar da hankalinki bazan cutar dake ba Kuma bazan bar kowa ya cutar dake ba domin ba haka yasa na d’aukoki ba dan haka ki natsu ki kwantar da hankalinki ya dan yi shiru dan jin me zatace itama shiru tayi saboda jin maganrsa ” kennan idan ta fahimci maganarsa shine d’an fashin daya d’aukota daga gaban iyayenta ? wani irin bugu gabanta ya sake yi da karfi kafin daga bisani qirjinta ya shiga dukan uku uku da numfashinta dake k’okarin tsayawa hankalinta yayi matukar tashi ta dinga maimaita kalmarsa ta karshe daya furta .”