KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“sweety kina ina ?” Ina gida kwance wallahi Ina hutawata ” bazaki fito bane ma yau ? cikin Marairaicewa murya Zahra tace “da wahala na fito Ina son na cigaba da kame kaina a gida dan ta haka ne kawai burina zai cika akan Adnan idan ya daina ganina a guraren shakawata ko hotel hotel may be zai yi kewata har ya nemini ,ni Kuma ta haka zan bijiro masa da lallai sai dai muyi aure “wani dogon tsaki helen taja “Kinga ki raba mutane da zance wani Adnan mutumin nan ba aurenki zai yi ba sau nawa yana fad’a miki bazai aureki ba amman da yake ke karamin brain gareki kin kasa ganewa? “me Kuma ya kawo wannan maganar sweety ? kin kirani ne dan ki ta’ba zuciyata ko me ? Ko d’aya na kiraki ne dan na fahimtar dake wani abu me mahimmam na tura miki Sako ta what’s app dinki ki shiga ki duba idan km zaki iya zuwa Rita Lori hotel yanzu kina iya zuwa ki ganewa idanunki komai tana gama fad’ar haka ta katse Kiran .
zahra tayi shiru sororo da waya a hannunta tana tunanin maganar Helen what’s app dinta ta shiga nan idanunta suka ci karo da mugun Abu domin kuwa adana dinta ne rungume da wata yarinya da bata san kowacece ba , ta sake bude wani hoto su din ne yarinyar na tsaye a gabansa shi km yana rike da kugunta wani irin abu taji yayi mata diran makiya a qirjinta nan take ta fara jin zafi a zuciyarta tasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta adalilin bugawar da take .
take gumi ya shiga karyo mata ciwon daya dade yana damun zuciyarta ya sake taso mata ya mamaye kahon zuciyarta , wannan alamarin akwai ciwo, ciwon da mikinsa ke azabtar da zuciya da gangar jikinta ,ciwon da kullum yake qara girma acikin zuciyarta, tunda ta fara son Adnan ta tsani ganinsa da kowace mace sannan Kuma zuciyarta ke cikin tashin hankali , ta zabura ta mike ta sauya kaya riga fara sol iya gwiwarta ta sakala jaka fara , haka ma takalimi fari ta fito cikin sauri tana Uber ,cikin kankanin lokaci mai Uber ya k’araso dan yana kusa daita, ta shiga gidan baya ta kame zuciyarta na wani irin zafi da ciwon da batasan ranar dainashi ba “why Adnan? me na
rasa ? “me kake so ajikin mace da bani dashi ?.me wannan yarinyar ta fini dan Allah karka bari bakincikinka ya kasheni Ina sonka fiyye da komai ta k’arasa maganar tana goge hawayenta ..”
tana gama karasowa Rita Lori ta sallami me Uber sannan ta kira layin Helen kira daya ta d’auka tayi mata kwatance gurin da suke zaune .”ta k’araso ciki hankalinta a matukar tashe tana baza idanu taga ta Inda jaguwa yake da yarinyar dan idanunta babu abinda suke son da burin gani agurin kamar tagansa aiko cikin sa’a idanunta ya sauka akansa makale da tanweer kamar zai mata numfashi ita Kuma ta d’aura kanta a saman kafad’arsa saboda baccin data soma ji ga sanyi gurin dake ratsa jikinta ta shige masa sosai har suna iya jiyo numfashin juna tuni idanun Zahra suka kawo ruwa wani tunani yazo mata ko dai yayi aure ne ?” kai impossible ace Adnan dinta yayi aure Kuma ko yayi aure bazai ta’ba zuwa da matarsa gurin nan ba sai dai idan sabuwar karuwa yayi wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke ,hankalin zahra yayi kololuwar tashi gadan gadan ta nufi Inda suke zaune tana gama Isa gurin tasa kafarta d’aya ta take kafar tanweer qara ta saki mara sauti tana furta ” subhanallah tare da runtse tsamammun idanunta dake cike da mayen bacci ,a hankali jaguwa yabi inuwar da ya gani tsaye akansu itama tanweer ta d’ago domin taga abinda ya take mata kafa kafin tanweer ta gama kare mata kallo har zahra ta cakumi wuyan rigarta da iyakacin karfinta “dan ubanki me kike yi tare da mijin da zan aura ? nan da nan jikin tanweer ya d’auki rawa wata razananniyar tsawa zahra ta buga mata wanda yasa jikin tanweer ya sake d’aukar qyarma zuciyarta ta karye hawaye ya soma sintiri bisa kuncinta muryarta na rawa tace “ki…kiyi hakuri wallahi babu komai a tsakaninmu kawai tai …”
“Shut up useless kawai hakurin uwarki zanyi ko da yake da ganin nasan kema sabuwar shigowa karuwanci ce bancin haka da Koda millioyoyin kudi ba zaki Kalli Inda Adnan yake ba bare har ki yarda ya daukeki “inna lillahi karuwa? ta furta kalmar a matukar firgice .
cikin tsananin faduwar gaba jaguwa ya lumshe sexy eye’s dinsa na second biyu sannan ya bude su fess yana mai jin bakinciki mara misaltuwa sam bai ji dadin Kalmar data fadawa tanweer ba murya qasa qasa yace ” ke wacce irin mahaukaciya ce daga zuwanki kin fara wa mutane hauka saboda ke din mara mutunci ce ki saketa kafin na tashi na targadaki yanzu yayi maganar yana janye idanunshi akanta tsayuwa zahra ta gyara sannan ta maida dubanta ga jaguwa tana kira sunansa kusan minti biyar tana Kiran sunansa batare da ta saki wuyan tanweer ba ranta ya Kai koluluwar baci wato cin mutuncinsa gareta yayi yawan da zai mata a gaban sabuwar karuwarsa yana jinta yaki amsa mata yayi kamar bai san da tsayuwarta ba “Adana !!!! ta qara Kiran sunansa a fusace wannan karon idanuwansa a lumshe ya mike ya ɗauketa da wasu maruka har biyu ajire da sauri ta saki wuyan tanweer zuciyarta na bugu da karfi “ka mareni adnan ?na mareki idan kika sake wata magana ko kiran yarinyar nan da karuwa sai na ballaki sannan minti biyu kawai na baki ki ‘bacewa idanuna banason ganinki .
tai shiru ta kasa aiwatar da hakan “haba wannan naci na menene haka ki bar rayuwata ko dole sai munyi rayuwa tare ? ya fad’a yana kafe tanweer da sexy eye’s dinsa wayanda kallonsu kadai ke haddasa mata shiga wani hali zahra ta girgiza masa Kai alamun bazata iya rabuwa dashi ba “bazan iya ba Adnan ta furta qirjinta na dokawa da matsanacin karfi” kiyi kokarin ki iya dan nafi bukatar haka Ina son ki bar rayuwata ki manta kin taba haduwa da Adnan arayuwarki yana gama fad’ar haka ya riko hannun tanweer ya soma tafiya daita a hankali .”