KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

        “ni ne naja komai Kinga dole nayi  blamed kains akan   abinda ya faru idan  ban kira ba a wannan lokacin ba  this wouldn’t have happened to you , nayi diverting attention di’nki I am very so……”.”Oh my god  I.B!”ta sake  fada cike da bacin rai idannunta a rufe.

“I am s…”.
        “I know you are Kuma nayi accepting kaima kayi hakuri”. Ta faɗa lokacin data tashi tsaye tana binsa da kallo shima tashi yayi suka kalla juna murmushi ya sakar mata. Da sauri ta da’uke kanta tare da shooking d’in kanta  da murmushi me sauti.
         Jin sautin murmushinta yasa shima ya fad’ad’a nasa murmushi.

Taku tayi zuwa bakin window d’in shima cikin sauri yabi sahunta, yasa hannunsa biyu ya zagayeta dasu ya mannata a  jikinsa, Runtse idannunsa  yayi yana jin wani irin feelings d’inta, sam baisan  ya rasa ta a rayuwarsa.

Bangaren Tanweer kuwa  ajiyar zuciya ta sauke tare da runtse idannunta, tana matuk’ar tausaya ma d’an uwan nata da  irin son da yake mata tun bata san soba yake nuna kulawarsa akanta , ta rasa mai yasa har yau bata jin sonshi cikin ranta baya ga na ‘yan uwanta   duk da tasan yana masifar sonta da rawar jiki a Duk abunda ya shafi lamarinta tare da rumgumarta  amma ta kasa sakin jiki dashi gashi shi  kusan bai da aiki saina  nuna mata tsantsar so da kulawa a ko yaushe Amman  hakan baya sata taji irin abunda take jin  friends dinta na bata labari sai dai kawai ta biye masa, Sun jima a tsaye yana rungume da ita inda sabo ta saba da wannan hug din nasa wanda iya abunda yake iya samu  kenan agunta  bayan shi ba wani.

“Salamu Alai… !”.
      Momy tafad’a lokacin data turo kofar dakin  yanayin data gansu yasa tayi saurin kokarin komawa tare da jan ko’far da sauri Tanweer ta zame  jikinta daga rik’on da Ibrahim ya mata wanda shima tuni kunya ta gama rufe shi.”Please Momy wait!”. Ta fada lokacin data dan taka da sauri zuwa bakin ko’far tana kallon Momynta wacce ke kallonta cike ta tambayoyi ,ganin yadda take kamar tana Jin tsoron yin magana,  sun dauki minis a tsaye a haka tana jujjuya ka’farta ta rasa meyasa take jin tsoron yin magana akansa  duk da she don’t know him.

“Tanweer I am waiting!”. Momy ta fada lokacin data kalla Ibrahim wanda shima ya kasa kunne yake sauraran jin abunda ke zuciyar Masoyiyar tasa, wanda daga shi har Momy suna mamakin yadda take jimamin  yin tambayar bayan she is not the type to.

“Ahm Momy!”. Ta fada tana wasa da dan igiyar gaban shirt dinta.
        “Oh Tan! Tunda baki da abun cewa I will have to leave inada abunyi”. Momy ta fada lokacin data juya da sauri Tanweer ta riko hannunta cikin nata . “Please Mom!”. Ta fada tana tabe lips d’inta cike da shagwaba kamar Wata ‘yar karamar yarinya.

          Yanayin yadda tayi har saida yaba Ibrahim dariya me sauti wanda bai tsamanin fitowarshi ba sai gashi ya fito, d’an kallonshi Tanweer tayi ta maida dubanta ga Momy wacce ke murmushi, ganin yadda Tanweer ta juyo a fusace yasa tayi saurin rufe bakinta da hannunta.

“Momy!”. Ta Kuma kiran sunanta.
       “Yes my angel!”. Ta amsa itama cikin yanayin da  Tanweer d’in ta kirata  cikin zolaya ,d’an buga kafa Tanweer tayi a fusace ta  raba ta  gefen Momy ta wuce  tana bubbuga ka’fafunta , Kallon juna Momy sukai da Ibrahim  Momy tabi bayanta da sauri tana kiran sunanta shima jujjuyawa yayi  yabi bayansu.

Tanweer na fita falon Dadynta ta nufa Kai tsaye . Ko sallama batai ba ta danna Kai, hango shi tayi zaune da system a gabansa da alama akwai abunda yake important a wannan lokacin musamman Jin ana niyyar kiran Sallar Magrib amma bai tafi masallaci ba.
        “Dady! Dady!! Dady!!!”. Cike da shagwaba take kiran sunan yana amsawa ba tare da ya waigo inda take ba tama kanta mazauni gefe, Ganin bai kalleta ba yasa ta fashe mishi da kuka.
         Jin hakan ya k’ara  d’aga masa hankali ya  ajiye komai  ya nufi inda take zaune. “Subhanallah me ya samu   Babyna  take kuka? Please tell me waya taba mun ke? Waya sa hawayenki me tsada tsiyaya ki fadamun Ko  wayeshi a fad’in duniya!”. Ya karasa maganar cike da zafi, dan inda akwai abunda ya tsana a duniya to bai wuce hawayen Tanweer ba.

Shigowar su Momyne ya katse mushi abunda yake fad’i nan  take ya maida fad’an kansu, Tanweer har lokacin tana ji yana musu fad’a bata tanka ba sai da yayi me isarta tukunna ta d’ago. “Dady please I…inaso…”. Sai Kuma tayi shiru tare da sunkui da kanta k’asa.
 
Da sauri Dady ya koma inda take zaune. “Me kike so? Ki fadamun komeye shi a kawo miki!”. Ya fada yana hararar su Momy dake tsaye gefe guda.

         Girgiza kai Tanweer tayi da kyar ta bude ‘yan kananun lips d’inta. “Dama wanda na kad’e akace ban kad’e ba inason ganin shi  domin nasan lafiyarsa”. Ta fada cikin sanyin murya wanda ita kanta batasan tana da shiba, ta rasa me yasa tunda ta dawo hospital ta kasa samun  nutsuwa akansa  ta kasa cire kyawawan idannunsa daga zuciyarta.

“Tanweer yaron nan bashi ya kawo ki hospital ba, hasalima bai biyo suba ta Ina za’a nemosa Ko a samo  wanda ya sansa?”. Ya jero mata tambayoyi wanda yasa bugun zuciyarta k’ara gudu saboda tsoron ace bazata k’ara ganinsa ba.
        “But I am worried”. Ta furta hakan kamar zatai kuka.
         “Please Baby karki damu kanki kan wani wanda baki sani ba talakan banza da wofi he does not deserve your worries especially your tears my Tan”. Ibrahim ne ya jero mata wadan nan kalaman ganin duk tabi ta damu, tuna yadda ya shiga da’kinta ta jima bata sanda  shigar shiba, ya tabbatar tausayi kawai ke damunta ba wani abuba, sai dai sam baiga abunda zaisa ta damu kanta akan wani talakan banza ba.

Nan suma  mahaifinta sukaita lallashinta wannan daren da kyar ta iya cin abinci ta koma da’kinta Ko hira batai dasu ba, haka shima Ibrahim ganin mutuniyar tasa ba face tun wuri ya kama hanyarsa ya bar gidan,  juyi kawai take akan makeken gadonta  idan ta runtse idanunta babu abinda take gani sai kyakkyawar fuskarsa mai ɗauke da kamala da natsuwa da alamun ya karantu yadda ya kamata saboda yasan mahimmancin dan adam, kafin ta gama fita haiyacinta taga yadda ya rude akanta Sai dai tayi mamakin da akace ba dashi aka kaita  hospital ba, wani irin bugawa qirjinta yake da matsanancin karfi ,ta sake  runtse idanunta gam   bata son ganin komai sai shi mikewa tayi ta janyo system d’inta ta shiga yanar gizo.


Misali karfe daya saura
Kwance  minister yake    akan  makeken  gadonsa kirar  itly   yana lumlumshe  idanun alamun jin bacci yayinda    matarsa hajiya zainab ke kwance a gefensa , dif  yaga  wuta   ya ɗauke yayinda  duk wata na’ura  dake aiki a d’akin ya tsaya  cak ya daina aiki  gidan ya ɗauki  shiru, shiru yayi yana mamakin d’aukewa wuta abinda bai taɓa faruwa ba kenan tun kafin ya zamo minister har zuwa lokaci daya zamo minister gidansa bai taba rashin wuta ba ,yana cikin wannan mamakin
ya dinga jin  motsin durowar mutane  da yake dakinsa ta bangaren baya yake kuma daf da katangar gidan  , ya yunkura  ya  mike  zaune daga kwance da yake yana ƙoƙarin saukowa daga kan gadon hajiya Zainab tayi saurin  riko hannunsa cikin nata, a she idanunta biyu  jikinta na rawa tace “ina zaka ? “zan leka window ne  ina jin kamar motsin mutane , “ba kamar kana jin motsin mutane  bane, mutane ne da gaske Allah dai  yasa ba yan fashi bane  ?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button