KUSKUREN BAYA 1 TO 48

cikin kankanin lokaci ya k’araso gida Kai tsaye bangarensa ya wuce da tanweer ta tsaya tana dubansa “ki kwanta ki cigaba da baccinki nasan bai isheki ba “batun komawata gida fa ?”zan maidake amman ba yanzu ba ki bani lokaci tayi kicin kicin da ranta kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa “gsky nifa na gaji wallahi gida nake bukata idan baka yarda ka maidani ba zan bi ta kowani hanya na bar gidan nan “ki gwada ki kigani idan hakan abu ne me sauki yayi mgnr tare da yin shiru yana dubanta dan tuni idanunta sun cicciko da ruwan hawaye “ban San me yasa kake min haka ba ,idan km kasan kana da dalilin rikeni ka fad’a min nasan zaman da nake yi amman bawai ka rikeni ba alhalin ni din ba muharamarka bace ta k’arasa maganar tana jan numfashi da danne kukanta tabbas jikina na bani akwai sirrin da kake boye min meye shi Ina son sani ?”.Tayi taku daya biyu ta qaraso gabansa qirjinta na dokawa da matsanacin karfi ta cigaba da magana a natse zuciyarta na rawa “zuwa yanzu ya kamata ka sanar dani menene shi abinda kake k’okarin boyewa ” take jikinsa yayi sanyi kmr Wanda aka jefa cikin kankara “zuciyata ta fara jefo min abubuwa masu wuyar misaltuwa akanka sai dai na shirya jin koma menene ta k’arasa maganar tana kuka dan ta kasa rike kukanta .”
ya Kai hannuwansa duka yana qokarin zagaye kugunta ta zame jikinta ta koma bakin gado ta zauna ta kife Kanta akan cinyarta tana cigaba da kukanta ya k’araso ya janyo stood ya zauna a gabanta ya riko hannunta daya cikin nasa ta d’ago runannun idanunta ta zuba masa tana sauraron abinda zai ce sai daya furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya fara magana a natse kmr me koyon mgn “kunnewanki bazasu iya Jin dalili
ko sirrin dayasa nake rike dake a gidan ba , hankalinki bazai iya dauka ba wallahi zuciyarki zata buga idan kikaji mafi alkhairinsa ki bar wannan maganar “na bar wannan maganar saboda me byn kana rike da rayuwata ka tsareni ka hanani naje ga iyayena alhalin suna cikin damuwar rashina ta k’arasa maganar tana fixge hannuwanta ya sake riko hannuwanta da sauri “shikenan ki bani lokaci kad’an nasan dai bazaki sake d’aukar lakacin da kikayi tare dani ba a gidan nan “. ya qarasa mgn Yana goge mata hawayenta dake tsiyaya a idanunta tare da yin shiru yana kallonta itama shi take kallo zuciyarta na zafi “to shikenan amman kayi min alfarma ka bani waya Ina son Jin muryar iyayena ,Ina kwadayi jin muryarsu dan Allah karka ce a’a”.
” ya mike tsaye yana cewa “zanyi nazarin akan haka yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin ta kwanta sharaf akan makeken gadonsa tana kuka tana tunanin yadda zata bar gidan ta kowani hali .Kai tsaye d’akin ajiya makamansa ya nufa Inda ya iske abokansa da yaransa suna zaman jiransa a hankali ya shiga yi musu bayanin Inda kowannensu zai tsaya da zarar sun Isa airport ya d’auki sama da awa biyu yana musu bayanin har sanda karfe goma shabiyu ta buga ya d’ago yana duba agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunsa a natse ya d’auke kyawawan idanunshi ya d’aura akan Scorpio tare da bashi umarni “kaje ka siyowa tanweer abinci ya lumshe sexy eye’s na second biyu sannan ya Bude ya jiyo ya Kalli eku “Kai Kuma kaje ma’ajiyin kudi ka diba ka siyo kayan d’anye abinci da duk abinda kasan za’a bukata na abinci ka tabbatar ka siyo “okay boss “.
gbdy abokansa suka zuba masa Ido kawai suna kallonsa cike da tsananin mamakinsa ” kamil ne yayi karfin halin tambayarsa “me za’a yi da d’anye abinci Kuma ?””Wa wannan yarinyar ne ya bashi amsa atakaice yana furzar da iska , duk da yaki yarda da son yarinyar yake amman su sun fahimci matakin soyayyar da yakewa yarinyar , soyayya ce me zafi da wuyar bari, soyayya ce da mutun bai Isa ya iya barinta ba cikin dadin rai ” jaguwa amman dai ….” saurin d’agawa anas hannu yayi saboda yasan me zai fito daga bakinsa “ya zaka katseshi ka barshi yayi magana mana ?”.bazan barshi ba dan nasan maganarsa iska ce da shirme ya fad’a yana runtse idanuwanshi tare da shafa sumar kanshi . kamil yace “kenan mu din yan iskanka ne sannan mashiririta ? tsuke bakinsa yayi yana kallonsu d’aya byn daya yana girgiza musu Kai alamun a’a “haka ne mana jubi ya fad’a “ada Kai din mai son a fad’a maka gsky ne amman me yasa yanzu duk ka canza bafa ayi haka damu ba ,ba’ayi damu zamu d’auko yarinyar mutane mu ajiyeta ba meye ma amfanin rike musu yarinya idan kana son yarinyar why not ka fada mana mu san abunyi ?”no no jubi Sam babu wannan a raina ta ya ma zan d’aukarwa kaina soyayya soyayyar ma da diyar minster Sam Sam hakan ba me yiwu bane ?
“me yasa zaka fadi haka byn zuciya gareka kamar kowani halitta “kunga dan Allah ku bar maganar nan haka, bama zan iya wata soyayya ba a yanzu kawai dai Ina gudar mata sharrin wannan mutumin ne me Katon ciki ban San wani tuggu zai sake had’a mata ba Ina tausayinta Ina Jin kamar zai cutar daita ne Idan na mayar daita “,saboda zunzurutun qaunar da kake mata ba shiyasa kake Jin tausayinta “,oh my god jubril wai ya kuke min haka ne ?”idan Ina son yarinyar nan wallahi zan fad’a muku dan bamu Saba boyewa juna komai ba , ku yarda bana son yarinyar nan ” shiru sukayi suka cigaba da kallonsa ba dan sun yarda dashi ba har ya juya ya kusan kofar fitar sannan yace ” eku Scorpio “zaman munafurcin me kukeyi dan Allah ku tashe kuje kuyi abinda na sakaku bamu da lokaci ” da sauri suka mike suna shafa kansu .”
Cikin takun Isa da Jin shi wani ne ya nufi haraban gidan hannunsa d’aya soke cikin aljihun wandonsa eku da Scorpio suka fice da sauri suka nufi Inda ya aikesu , yana nan tsaye yaga fitowar tanweer tana karewa haraban gidan kallo fuskarta d’auke da murmushin jin dadi ba kamar d’azu ba , a kallon da yake mata ya lura hankalinta na kan shukokin gidan ne ,yana kallonta ta cigaba da takawa a hankali har ta Isa Inda shukokin suke tana shafawa a hankali tana lumshe idanu , a natse ta karya kwana tabi hannunta na hagu ,cike da natsuwa ya biyo bayanta , bata tsaya koina ba sai gurin fararen fure dake shuke cikin ruwa har lokacin fuskarta da murmushi , ya k’araso ya tsaya a bayanta yana sauke numfashi, saukar numfashinsa yasa ta juyo a tsorace har qirjinta na ta’ba nashi saurin d’auke numfashi yayi qirjinsa na tsananta bugu , ganin shine tsaye yasa ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta juya ta cigaba da kallon fararen fure muryarta a sanyaye tace ” ina son fararen fure ko zaka tsinko min? ta fad’a tana duban Inda yake tsaye har lokacin hannunsa na soke cikin aljihunsa ” kina son fure ne haka ? ya tmbyeta yana kare mata kallo tsab ” sosai Ina qaunar fararen fure arayuwata ya qara taku biyu yayi kusa daita sosai yana cewa “yarinyar da nake so itama tana matukar son fure ” qirjinta ne yayi wani irin bugawa da karfi , taji saukar maganarsa kamar saukar aradu ,zafi ta dinga ji a qirjinta tamkar ana diga mata ruwan dalma nan take ta nemi natsuwarta ta rasa idanunta na kan furen tace “wacece ita yarinyar da kake so ? ta tambayesa kwayar idanunta cikin nashi ,bai bata amsa ba duk da ya lura da canzawar da tayi a lokaci daya sakamakon jin yana son wata dariya taso subuce masa dan yadda ta had’e rai abun babu sauki kace shi din mijinta ne .