KUSKUREN BAYA 1 TO 48

ranta a ‘bace ta soma tafiya zuwa wani bangaren “ke Ina zaki ?itama banza tayi masa kamar yadda yayi mata “ba dake nake magana ba kina jina ? still banza ta masa ” ki koma ciki kar na sake ganin kafafunki kin fito haraban gidan nan bare nan. “dan me yasa bazan fito ba ? ta fad’a a fusace tana Jin wani irin zafi mara misaltuwa sannan ta juyo ta fuskancesa fuskarta a had’e tamakr ba itace take murmushi a sakwanin da suka wuce ba , ta rasa dalilin wannan so da take masa , soyayyarsa me karfi ce agareta ,bata ta’ba sanin tana da kishin irin haka ba sai yanzu daya furta yana son wata ba ita ba yace baya son zahra sannan baya sonta to wacece wannan daya furta da bakinsa ? Ido cikin Ido suke kallon cikin kwayar idanun juna kamar ta rufesa da duka ko zata samu sausauci ,k’okarin danne kishin tayi ta sanyawa jikinta jarumta “ko bazanje koina ba ka barni na dinga fitowa Ina ganin fararen fure tayi mgnr kmr zatayi kuka ,bai ce mata Komai ba ya riko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita bai tsaya a koina ba sai d’akinta ya bud’e kofar ya turata “iya nan na yarda kiyi rayuwa aciki ko falon gidan nan ban yarda ki fito ba idan Kuma kikayi kuskuren fitowa zaki ga abinda zan miki ya k’arasa maganar tare da ya janye kofar ya rufe garam , ita duk wannan abun da yayi bai dameta ba akan zance budurwa da yayi mata shi yafi komai ta’ba zuciyarta da d’aga mata hankali, tsaki taja yafi sau goma ajere ” Allah! Allah !! ka tsi ….” shiru tayi ta kasa tsine masa shi da budurwar da yake so ta koma karshen gado ta zauna tare da zuba tagumi .”
ya shiga d’akinsa ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka ya tsaya shiru cikin bathtube ruwa na tsiyaya a sansar jikinsa yana tunanin maganar abokansa akan yarinyar “duk suna min kallon d’an soyayya alhalin ba haka bane acikin zuciyarsa ,” taimako ai ba soyayya ce? ya tambayi kanshi ya d’an dade ruwa na sauka ajikinsa sannan ya fito kugunsa d’aure da farin towel wanda bai wuce cinyoyarsa ba byn ya goge jikinsa
ya shafa body lotion yayi cumb din sumar kanshi ya soma shirya kansa cikin Kanana kaya riga blue wanda a gabansa aka rubuta polo 1967 yayinda wondon da canvers din kafafunsa suka kasance ja ,kansa sanye da facing cap ja kmr yadda rigar jikinsa yake , tsintsiyar hannunsa d’aure da agogon rolex ya rufe idanunshi da glass baki ya feshe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kamshi, sosai kyawunsa ya bayyana ya soke hannunsa daya cikin aljihun wandonsa kamar Koda yaushe ya nufi kofar fita, falon ya dawo Inda ya iske scopio ya dawo bai tsaya bata lokaci ba ya karbi farar ledar hannunsa ya juya zuwa d’akin da tanweer take .”
tana Jin shigowarsa amman taki d’agowa daga kwance da take dan wani irin haushinsa take ji ,ya ajiye ledar akan bedside yana cewa “ga abinci nan ki tashi kici sannan zanje wani aiki me mahimmanci zan dan dade kafin na dawo batare data d’ago ba tace “a dawo Lafiya amman dan Allah ka bani waya “. “ki daina damun kanki ba waya ba gidan ma zaki bari gbdy idan lokaci yayi ya juya ya fara tafiya cikin hanzarin wannan karon d’akin dake gefen d’akinsa ya shiga ya jima sosai dan kusan awa d’aya yayi sautin muryar scopio ya fito dashi “boss komai ya kammala “okay kana iya tafiya ya fad’a d’akin tanweer yana cewa ” nasa a kawo komai na kayan abinci muje kiga kitchen din “. banza tayi masa taki cewa komai hakazalika taki tashi hatta abincin da ya kawo bata ci ba ya zuba mata Ido har kusan minti biyar kome ta tuna tayi zumbur ta mike tsaye tana dubansa yayi gaba ta biyosa a baya har cikin had’ad’d’en kitchen din .”
a hankali ya dinga nuna mata komai daki daki kitchen din very Niet kamar mace ce ke amfani dashi babu abinda babu na kayan abinci komai gashin nan ajiye yasa an kawo,” ki duba ko akwai abinda bai miki ba a canza akawo miki wanda kike so “. idanunta da suka canza kala sukayi jazir tsabar kishi ta d’ago ta sauke su akan fuskar jaguwa dake tsaye a gabanta yana kare mata kallo ,Shep dinta yafi komai daukar hankalinsa irin matan nan ne masu shep din cocakola “dan tani da baka tanadin wad’an nan abubuwa ba dan ba sune abinda nafi bukata ba bukatata na ..” “.shiiiii ya d’aura yatsansa akan lips dinta yayi kusa kusa daita har suna iya jiyo numfashin juna wani irin tsalle zuciyoyinsu yayi wanda har sai da hakan ya haifar musu da tsayuwar numfashi , take jikinta ya soma kyarma rungumeta ajikinsa yayi tsam yana busa mata numfashinsa .
tuni zuciyarta ta karye hawayen kishinsa da kewar gida ya soma zuba bisa kuncinta ya rungumeta sosai ajikinsa kamar zai mata numfashi yana shafa gadon bayanta .
wani irin haushi ne da bata ta’ba jin irinsa ba ya diran mata a kahon zuciya ,kullum yana ikararin baya sonta amman ya iya nesanta kanshi daita yana son maidata yar iskar karfi da yaji ta soma mutsu mutsun kwatar jikinta domin zuwa wannan lokacin zuciyarta ban da zafin kishinsa babu komai aciki ,ganin yaki sakinta yasa ta soma dukan qirjinsa da iyakacin karfinta amman yaki sakinta ya kamkameta tsam yana son yaga karshen karfinta “Kai dai wallahi mugu ne Kuma azalumi inshallahu yadda kake quntata min wallahi Kai ma sai Allah ya quntatawa kannenka “. cak ya saketa yana furzar da numfashin mai zafi daga bakinsa idan akwai abinda ya tsana bai wuce a ta’ba kannensa ko aibantasu da mugun abu ba . ta zube kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tare da Kiran sunan iyayenta , muryarsa a tsarke yace”tan ….”bata d’ago ta kallesa ba “karki sake sako kannena cikin shirmenki idan kina son ki zageni kiyi amman kannena karki sake .”
“Dan Allah malam ka min shiru daga yanzu muddin baka maidani ga iyayena ba wallahi na dinga ma kannenka mugayen fata kenan , ada na dauka ka taimakeni ne sai dai a yanzu taunina ya Kashi dabam dabam tare da tambayoyi masu wuyar amsawa “waye Kai Adnan ? Ka fad’a min waye Kai Ina son sani kai din waye ?cikin sauri ya juya ya bar kitchen din zuciyarsa na rawa bai ta’ba Jin tsoron wani yasan sana’arsa ba ko sanin ko shi waye sai yau , bazai iya sheida mata shi din waye ba , zai barta a matsayinsa na me taimakonta bazai ta’ba yarda tasan ko shi waye ba yana tafiya yana jan tsaki ji yake kmr zuciyarsa zata buga .
ya rufe kofar falon ya fita zuwa haraban gidan , tuni su kamil ,anas, jubi, da jabir da sauran yaransa sun hallara har wasu ma sun shiga mota sun zauna shi kadai suke jira yana daf da karasowa eku ya bud’e masa gidan baya ya shiga yana cewa “hope kowannenku yayi shiri me kyau? ” sosai suka bashi amsa motarsu na kokarin fita daga gidan Idanunsa ya sauka akan wani dattijo zaune a gindin bishiyar dake gefen gidansa nan take yace wa eku “stop ! “.eku ya tsaya nan take mutumin ya mike tsaye yana kallon motocin jaguwa masu shegen kyau da daukar hankali da hannu ya yafito me gadi ya k’araso da d’an saurinsa ya tsaya yana rusunwa “wacan mutumin fa me yake yi anan ? “wallahi oga gurinka yazo wai yana son ganinka tun jiya byn fitarka yazo nace baka nan shine dazu byn dawowarka sai gashi ya dawo na shiga domin nasar maka sky yace Kuna meeting shine na dawo na sheida masa ya dawo Koda karshen sati ne amman yace lallai sai ya ganka .”