KUSKUREN BAYA 1 TO 48

shiru jaguwa yayi yana nazari sannan ya dan Kalli Inda dattijon mutumin yake tsaye cikin kod’ad’un kaya marasa fasali yana cigaba da nazarinsa ,a hankali ya fito ya soma tafiya har ya k’araso garesa , dattijon na ganinsa ya shiga rawar jikin “barka da fitowa ranka ya dade “barkanmu baba ya kwanan iyalin ?” Alhamdulillah duk muna Lafiya ,
jaguwa ya kad’a Kai sannan yace ” baba fatan dai lfy kake son ganina ?”dattijon ya marairaice murya kmr zai yi kuka sannan ya fara mgn muryarsa na rawa gwanin tausayi “daman matsalace ke tafe dani gareka a wajen mutane na samu labarin irin taimakon da kake yiwa mutane “. jaguwa na jin haka ya sauke numfashi yana dubansa a tsanake ” Ina Jinka baba wacce irin matsalar ce ?”daman akan yarona ne shekararsa biyar kenan da kammala karatunsa na degree sai dai yadda kasar nan tamu ta dawo yasa har yanzu yake gida zaune, duk Inda yaje apply din aiki sai ace sai ya biya kamin dubu dari biyar kudin office kafin a daukeshi gashi bashi da hanyar da zai samu kudin, ni ya kamata na biya masa ya samun aikin to ni din ma babu dan na abinci ma da kyar muke samu, dan Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeka ka samo masa aiki ko Kuma ka yarda ya kasance a karkashinka ya karasa maganar yana zubar da hawaye .”
jaguwa yayi shiru yana sauraronsa har sanda ya dasa aya “karkayi kuka baba inshallahu zan yi iyakar kokarina yanzu dai Ina kan hanya ne zani wani aiki amman ka dawo zuwa karshen sati da yaron inshallahu matsalarka tazo karshe dattijon ya soma k’okarin durkusawa jaguwa domin yi masa godiya, jaguwa yay saurin sa duka hannuwansa ya taresa “haba baba karka min haka mana ” na gode d’ana Allah ya albarkaci rayuwarka , Allah yasa ka gama da duniya lafiya ,Allah ya jikan iyayenka idan sun rigamu gidan gsky, idan Kuma suna raye Allah ya Kara musu Lafiya mai amfani na gode na gode daman da gaske ana samun mutane irinka ?karka damu baba ya k’arasa maganar yana tsaida dattijon bisa kafafunsa ya Ciro dubu goma a aljihun wandonsa ya mika masa “ga wannan kayi kudin mota yana gama mikasa ya juya ya shiga mota suka bawa motacinsu wuta suka bar unguwar ,da sauri dattijon ya Ciro wata rubabbiyar wayarsa ya shiga neman number d’ansa domin yi masa albishiri .”
Bangaren minister of health kuwa gbdy hankalinsa yaki kwanciya kullum yana manne da hjy zainab yana rarrashi wacce kuka ya zame mata abincin ruhinta , yanzu ma zaune yake kusa daita yana aikin daya saba tare da babban amininsa alhj Tahir dake k’okarin shawo kanta “kada kiyi fushi da hukuncin Allah zainab wannan abu daya faru gbdy bai mana dadi ba sai dai bawa baya wuce qaddararsa Allah ya rigada ya qaddaro surayya zata fad’a cikin wannan tashin hankali bamu Isa mu canza mata qaddararta ba, fatan mu dai Allah yasa bata cikin tsanani cikin muryar kuka tace “na kasa jurewa dady dake hk take kiransa kmr yadda Ib ke kiransa ” yau da mutuwa tanweer tayi na binneta da zan fi samun natsuwar zuciya amman Ina raye tanweer tana hannun ‘yan fashin da ko labarinsu ba’a samu ba , taya kuke tunanin hankalina zai kwanta ?”. Suma kiramu muji me suke bukata daga garemu sunki ta k’arasa maganar tana kallon saman falon hawaye masu zafin gaske na gangaro mata wanda zafinsu da rad’ad’insu ya wuce tunanin mai karatu .
“wannan haka ne amman duk da haka addua zamu taru muyi allah ya bayyanata cikin koshin lfy “amen ta furta a kasan makoshi tana cewa ya jikin Ib kuwa? kullum Ina sa ranar zanzo na dubasa mutanen dake shige da fice agidan nan zuwa jaje ke hanani fita ammn inshallahu zan samu lokaci na leko na dubashi .
“to jikinsa dai da sauki zamu ce Allah dai ya iya mana da iyawarsa dan rayuwar Ibrahim na daf da fuskantar matsala da Kuma qalubalin rayuwa ya kasa jurewa rashin tanweer “Allah sarki ib yana qaunar tanweer kmr yadda yake qaunar rayuwarsa inshallahu zata dawo har ma suyi aure ta k’arasa maganar tana sake matso ruwan hawaye sun dade suna tautauna wa akarshe minister ya kira cp yaji halin da’a ake ciki ,byn cp ya d’auki Kiran suka gaisa “wai ya ake ciki ne da batun yarinyata shirun fa yayi yawa zuciyata ta fara tsinkewa Ina Jin kamar Allah ya d’auki raina na huta ? na kasa jurewa rashin diyata da rashin kwanciyar hankalin matata “.naunayen ajiyar zuciya cp ya sauke sannan ya fara magana a natse”mun baza mutanen mu cikin gari yanzu haka mun fara samun improvement akan lamarin “to alhamdulillah Allah ya taimaka yasa aga yarinyata cikin koshin lfy “karka damu inshallahu komai yazo karshe ka kara mana lokaci kad’an “na gode na gode ” sukayi sallama minister ya fuskanci hjy zainab tare da yi mata albashiri da abinda cp ya fad’a masa nan take farinciki ya mamaye zuciyarta shi kuwa alhj Tahir cikinsa ne ya duri ruwa gabansa ya shiga fad’uwa hankalinsa yayi kololuwar tashi .
babu shiri yayi musu sallama ya shiga motarsa direbansa ya ja suka kama hanyar zuwa gida ,yasan ya taro wa kanshi match tunda yayi sanadin da’aka d’auke tanweer wayarsa ya Ciro yanata Kiran number jaguwa ana ce masa akashe take har ya k’araso gida bai samesa ba , ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa yasan muddin su jaguwa sukazo hannu kashinsa ya bushe domin asirinsa ya tono .”
fitowa yayi da sauri daga cikin motar bai tsaya jiran direbansa ya fito ya bude masa ba kmr zai tuntsura ya shiga cikin gidansa gumi na karyo masa ta koina a sansar jikinsa kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya rage kayan jikinsa ya shiga zariya yana neman mafuta , yana tsaye hjy baseera ta shigo tana binsa da kallon mamaki dan ta kwana biyu bata gansa cikin yanayi irin haka ba “wai Lafiya ka shigo kamar wani kububuwa me km ya faru ? tsaki yaja yace “babu komai . “To daga Ina kake yanzu “?. daga gidan minister nake ya bata amsa yana fifita da hannunsa dan wani irin azababben zafi yake ji ta koina tana Jin haka na gane komai ta kama gabanta zata fita ya d’auki remut din ac yana kokarin qara karfinta tare da cewa “ya kuma zaki wuce ki barni ga dan iska kin samu kin tmbyeni na baki amsa kawai zaki juya ki kama gabanki “oh to ni me zanyi maka ?” zata sake magana ya d’aga mata hannu”jeki kawai bananason jin komai tunda babu abinda zakiyi shasha kawai ya fad’a a matukar fusace yana juya mata baya.
tabe baki tayi a ranta tace “ai Kai ne Sha Sha ,mutumin banza kawai da bai san ciwon kanshi ba aurenka ko hasara duk a tunaninka ban San halin da kake ciki bane byn na san komai a juri zuwa rafi dai wata rana tulun zai fashe juya tayi ta barshi tsaye yaji da damuwarsa .ta nufi gurin d’anta ta bashi maganin karfin jiki dan ta sha alwashin bazata sake yarda da tsarin mijinta ba hk kawai ta rasa tilon d’anta a banza, gbdy magungunan da yasa nazifi ya rubuta masa an siyo sai dai bata bashi ya sha ba wasu dabam ta bashi jikin ne dai nashi yaki daidai saboda an rigada an karya masa garkuwar jiki ” .