KUSKUREN BAYA 1 TO 48

a matukar wahale suka k’araso gida jaguwa yay saurin fitowa daga cikin mota ya k’arasa da sauri ya bud’e kofar shiga cikin ainihin falon gidan , su jubi suka kamo kamil suna tafiya dashi a hankali kafafunsa babu takalmi dan tuni sun cire masa tun acikin mota ,Kai tsaye suka nufi hanyar falon jaguwa na mussaman dashi suna masa sannu, a hankali suka kwantar dashi akan wani k’aramin madaidai gado wanda daman an tanadesa domin irin haka ,kamil ya runtse idanunshi saboda azabar ciwo , cike da hanzari jaguwa ya nufi Inda first aid box dinsa yake ya d’auko ya dawo da sauri , eku ya janyo masa kujera ya zauna a gaban kamil yana masa sannu .”
jin motsin shigowar motocinsu da maganar wasu daga cikin yaransa sama sama yasa tanweer lalla’bowa babu takalmi a ka’fafunta tai hanyar babban falon gidan tana bin bango tana qarasowa bakin kofar falon ta tsaya a hankali ta bud’e kofar ta shiga bata ga kowa a falon ba, kasa kasa take jiyo magangansu , kawai ta nufi wani dogon korido Inda take zaton daga nan sautinsu yake fitowa , a hankali ta tsinci kanta acikinsu kowannensu cikin tsananin tashin hankali , jaguwa zaune a gaban kamil cike da tausayawa yana k’okarin cire masa harsashi . binsa tayi da kallon mamaki qirjinta na wani irin bugawa da matsanacin karfi shafa idanunta tai hade da runtsesu na second biyu sannan ta bud’e tana sake sauke idanunta akanshi wanda zuwa lokacin har yay nasarar ciro bulet din yana kallo sannan ya saka acikin farantin silver dake rike a hannun jubi, yayinda sauran ke zaune cikin tsananin tashin hankali gbdy idanunsu ya rufe babu wanda hankalinsa ya Kai Inda take tsaye .”
naunaye ajiyar zuciya suka sauke lokacin da jaguwa ya cire wa kamil bulet ita Kuwa tanweer zuciyarta ta shiga rawa had’e da tsinkewa .”me zata gani yau ? daman likita ne shi ko kuwa mafarki take ? yes wannan ba mafarki take ba shine tagani zaune ya cire bulet a kafar abokinsa, kasa tayi da idanunta tana kallon bayansa nan idanunta ya hango bindiga pestol soke a abayan wandon jaguwa ,nan take ta sake fita daga haiyacinta “bindiga ….! ta furta a kasan ranta ” me Kuma yake yi da bindiga ? ya Allah karka sa abinda zuciyata ke hasashe akansa ya zama gaskiya dan bai cancanci haka ba ” wani kuka ya kufce mata ta juya da sauri tana shesheka wanda hakan yasa gbdy suka d’ago suka ganta tana sarsarfa , cike da matsanacin firgici suka tsura ma jaguwa Ido dan jin abinda zai ce bai yi magana ba haka zalika bai nuna alamun damuwa atattare dashi ba , ya mike tsaye yana
furzar da numfashi tare da yiwa kamil sannu” ka kwanta ka huta kafin akawo maka abinci ya gyada masa Kai yana cewa” na gode abokina Ina alfahari da Kai ,nima haka .”
jubi ya dube jaguwa yana cewa “wallahi ban ta’ba shiga tashin hankali ba irin na wannan lokacin na tsorata matuka na sadaukar zamu rasa kamil “ba kai kad’ai ba inji cewar anas tafiya jaguwa ya fara a hankali suka biyosa a baya har gurin shakatawarsa “da’ace sunyi nasara akanmu zamu iya rasa rayukanmu gbdy”. sai lokacin jaguwa ya motsa lip’s dinsa “ina ai sai dai idan tawa ta kare sannan zaku iya shiga wannan hali amman muddin Ina tsaye akan kafafuna babu wanda zai yi nasara bare har mu rasa rayuka ” ya karasa maganar tare da tsayawa cak ya rike karfen runfar dake kafe acikin gurin shakatawar , “hakika Nima na karaya inji cewar jabir ” Karku ta’ba rungumar Karaya arayuwarku duk halin da zamu shiga karku karaya saboda rashin samun nasara ba namu bane ,a duk lokacin da naga Kun Karaya sai naga kamar tun asalin ku din ba jaruman gaske bane, sannan baku ne jarum da mukayi gasar mutuwa dasu ba .”
murmushi sukayi gbdy suna sauke numfashi “uhm wannan fa ba kamar gasar mutuwa bace ,gasar mutuwa kowa yasan mun saida rayukanmu ne dan biyan bukatarmu wannan fa ?”bayan sai da rai har da tozarci zamu janyowa gangar jikinmu idan muka tsinci kanmu a hannun jami’an tsaro “.anas ya karasa maganar yana dafa kafad’ar jaguwa “yanzu dai barkanmu allah ya k’ara karemu .” ameen jaguwa ya fad’a acikin zuciyarsa. “ka zauna kana bukatar hutu, jaguwa ya zauna akan d’aya daga cikin kujerun gurin yana lumshe idanunshi ” me za’a kawo maka ka d’an sha ? ya girgiza masa Kai alamun bai bukatar komai , zama anas yayi kamar yadda sauran abokansa sukayi yana cewa “ya za’a yi da wannan yarinyar ta rigada taga komai , koma nace taji wasu abubuwa akanmu ? ,yana d’aya daga cikin abinda yasa kaga banason yarinyar nan agidan nan “.”me taji ?.”Ko me mu kace ?yay masa tambayar a dan kufule ” idan Kuma taji taji kenan shikenan daman abinda take bukatar sani kenan tasan su waye mu ” ya k’arasa maganar yana jan dogon tsaki tare da jin bakinciki da takaici, haka nan Kuma ya tsinci Kansa da Jin fad’uwar gaba mai tsanani “.
Koda tanweer ta koma d’aki ta kasa tsaye ta kasa zaune sai zariya take acikin d’akin ita kad’ai, ta saka wancan ta kwance , kwakwaluwarta ta shiga tunani mai zurfi, babu abinda zuciyarta bata kisama mata ba akansu , abu uku zuciyarta ta tsayu akansa shi din dan fashin ne ko Kuma jami’in sirri ,ko likita , idan ba haka ba me yake yi da bindiga ajikinsa ? ta kasa hakuri dan haka ta sake fitowa tai hanyar boys quarter nan fa hankalinta ya sake tashi ganin yadda yaran jaguwa ke fitowa da manya bindigu suna adanawa a maboyarsu ,mutuwar tsaye tayi har sanda suka kwashe komai suka d’auki katuwar jakar kudin da suka shigo dashi suka nufi hanyar Inda jaguwa yake tare da abokansa suna tautaunawa , cike da matsanacin tsoro ta biyo bayansu a tare suka k’araso ta ra’be jikin wata bishiya kasancewar yaran jaguwa suna gabanta yasa jaguwa da abokansa kasa ganinta .”