KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“hatsabibin boka ne ni zan tabbatar da nayiwa kawarki abinda take bukata , zan biya mata bukatarta ta duniya, ya juya ya kalli zahra ” zakiyi nasara akan rabashi da yarinyar amman shi da wahala ki mallakesa kamar yadda kike so , domin kuwa wannan mutumi ya wuce da tunaninki yana da hatsarin tunkara domin kuwa akwai tsari mai karfi ajikinsa , kafafunsa yafi naki tsawo ,Inda ya taka har ki mutu kafafunki bazasu taka ba . “
“yanzu boka ya za’a yi kenan wallahi idan ban mallakesa ba zan iya mutuwa sannan babban burina na rabashi da yarinyar nan koda diyar talaka ce bare diyar mai kudi.
sai daya numfasa sannan yace ” na fada miki bazaki mallakesa ba sai dai ki rabashi da yarinyar ,Kuma aikin da za’a rabasu na bukatar budurwar wacce bata taba aikata zina ba Kuma an yi nasara domin kuwa yarinyar budurwa ce wani nmj bai taba amfani daita ba ,Ina tabbatar miki muddin ya kusancenta zaki iya rabasu zai dai ya saurareki amman ba zakiyi yadda kika ga dama dashi ba yana gama fad’ar haka yace “me kika gani ayi aikin ko abari? “
hankalinta a matukar tashe tace “yanzu boka babu wani mafuta sai wannan ?” wallahi Ina matukar kishin Adnan bazan so ya rabi wata mace ba byn ni “wannan ne kawai hanya mafi sauki Shima din ba shine zai Kai Kansa gareta ba itace zata Kai masa kanta , Kinga wannan saurayin naki akwai abubuwa da yawa akansa shiyasa ma ya rufe ma Kansa taurari dan kar mutane su san ko waye shi yana kaiwa nan yace ku tashi ku wuce “kafin sati biyu da kanki zaki kirani ki bani labarin cigaba da aka samu ta bud’e jakarta ta dibo kudi masu yawa zata ajiye a gabansa ya nuna mata gurin gunkinsa , nan taga wata tukuyar tsafi daskare da jini ta saka kudin ,jiki a sanyaye suka baro gurin boka zuciyar Zahra cike da matsanacin kishi “gsky banji dadin wannan aikin ba nifa banason ya kusance kowace mace byn ni , yanzu ance dole sai ya kusanci yarinyar nan Kuma gashi budurwa ce Kinsa amsar budurcin mace akwai tsayawa arai .
“ki kwantar da hankaliki Zahra kibi maganar boka Inda akwai wata mafutar byn wannan zai miki ,ke yanzu ma meye abun d’aga hankali dan ya kusancenta ke da zai dawo hannunki “wani zai dawo hannuna ko baki ji abinda bokan yace ba ? cewa fa yayi bazan mallakesa ba ni wallahi dama na hakura da aikin nan ta karasa maganar tana yastina fuska .”
“Dan Allah kawata ki cire kishin nan a ranki mude bukatarmu ta biya ya rabu da yarinyar shine abinda muke so , har suka k’araso tasha magana daya dai suke yi blessing na kokarin shawo kan Zahra , shiru zahra tai taki cewa komai zuciyarta na tuttukin bakinciki Adnan zai kusanci tanweer Kuma shi zai amshi budurcinta.
bangaren tanweer kuwa taki cin abinci, yadda ya kawo mata abincin jiya haka ya fitar dashi bata ci ba ,ai ko shima ya hau dokin zuciya yaki bin ta kanta bare ya rarrasheta .” duk yadda blessing ke Jan zahra da hira acikin mota ta kasa cewa komai har suka sauka a lagos kowacce ta kama gabanta gbdy Zahra ta kasa samun kwanciyar hankali sam bata ji zata iya wannan kasadar sai tayi kmr ta kira boka tace ta fasa aikin sai Kuma ta fasa .”
Zaune jaguwa yake cikin baban falonsa system ne a gabansa yana aiki eku ya shigo tare da rusunawa ya gaishesa ya amsa batare daya d’ago ba eku ya soma magana cike da ladabi “boss kamar ka manta da wancan mutumin ” Jaguwa ya d’ago ya kallesa a tsanake yana bukatar qarin bayani “wancan mutumin dakace mu dauko a Rita Lori hotel mu killace maka shi ” sai lokacin jaguwa ya tuna ya lumshe idanunshi “Yana Ina ne ?”yana boys quarter ya gyada Kanshi kawai ya cigaba da abinda yake eku bai wuce ba sai da jaguwa ya gama abinda yake ya mike yana tafiya kamar baya son taka kasa yayinda eku ke biye dashi har suka k’araso bakin kofar d’akin da alqali yake , eku yayi saurin bude masa kofar d’akin , alqali najin motsin mutane ya shiga zare Ido jaguwa ya tsura masa Ido ya rame sosai rama ta tashin hankali acikin kwana biyu da yayi wanda idan ka kallesa bazaka sake marmarin kallonsa ba duk ya fita haiyacinsa, zaune yake jugun hannunwansa da kafafunsa duk kulle su da handcuff kamar wanda yake prison a hankali jaguwa ya shiga Taku a hankali yana masa wani wulakantaccen kallo sannan ya tsaya a tsakiyar d’akin yana cewa”waye Kai menene yasa kake bibiyata ?alqali da bakinsa ya bushe sosai ya fara magana cikin wahala “babu dalilin da yasa na bibiyeka ya karasa maganar cikin tsananin tashin hankali .
“waye Kai ?”shiru alqali yayi ya kasa cewa komai jaguwa ya juya ya soma tafiya “Ina ganin azabar yunwar da’aka masa bai ishesa ba ka cigaba da barinsa babu ci babu sha har ya zamo sanadinsa ” alqali wanda muryarsa ta fara dashewa babu karfi a tattare dashi yace “kayiwa Allah kayi hakuri na tuba “jaguwa ya cigaba da tafiya batare da juyo ba “idan na fada maka bazaka kasheni ba ?”yayi masa bmbyr a gigice cak jaguwa ya tsaya tare da goya hannuwansa duka a baya ya juyo
ya tsura masa Ido alamun yana sauraronsa “ni ..ni …sai Kuma yayi shiru yaji tsoron sheida masa cewar shi din jami’in sirri ne ” kayi hakuri dan Allah ka tausaya min nayi kuskure bazan sake ba “runtse idanu jaguwa yayi ,ba dan baya son aikata kissa a rayuwarsa ba da babu shakka da sai ya shake wuyan wannan
mutumin da hanunsa har sai ya mutu
“kaga nayi kama da wanda za’a bibiyi rayuwarsa for the last time ka fad’a min wanda yasa ka bibiyeni? yayi masa tmbyr yana hade fuskarsa kmr hadari. shiru alqali yay ya kasa magana Dan Bai San abinda zai ce ba har kusan minti biyar Yana tsaye yana jiransa ,eku ya Ciro karamar pestol ya saita gefen brain dinsa “na baka minti biyu ka fadi Wanda ya sakaka kafin na tarwatsa brain dinka na aikaka lahira “wa ..wallahi babu kowa Ina tafiya ne na gansa tare da yarinyar minister of health da ake nema shine na dinga binsa a baya naga Inda zashi daita wallahi byn wannan babu Wanda ya aikoni .
“ka cigaba da ajiyarsa anan har sanda zai fadi gskiyar wanda ya aikosa sannan ka ciyar dashi da gari zalla da ruwa ,ruwan ma kwatan tea cup haka ma gari muddin yayi wata bai fadi Wanda ya aikosa ba ka tashesa aiki yana gama fad’ar haka ya fice daga daki haka ma eku ya nufi kofar fita kmr wani zautacce alqali ya rarrafa da gwiwawinsa yana k’okarin riko ka’fafun eku Amman Ina tuni ya fice ya maida kofar ya rufe cikin rashin tausayawa, hawayen danasani suka silalowa alqali ya fara zubar da hawaye yana adduar Neman mafuta “me yasa ka biyosa gashi ka jefa rayuwarka cikin hatsari kuka yake sosai kamar karamin yaro.”