KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Wai waye wannna jaguwa din ne ? waye km ?.gbdy sai da tanko gote ya kira sunayensu d’aya bayan d’aya ka amsa min tambayata boka ” ya san sunansu ne a bakin wasu daga cikin mufukan’ yansanda da sukayi attacking dinsu a wancan satin “. shiru bokansa yayi yana dube dube acikin kasa ,abubuwa da yawa ya gani akan jaguwa km abun ya balain tsoratar dashi dan har wani gumi ya had’a da kyar yayi jarumtar yin magana “wannan yaron da Jamar’sa rikakkun y’an fashi da makami ne da suka ga gari kowa acikin garin nan yana da karfin da zai iya karawa da kowa acikin garin nan ,haka yana da karfin da zai iya shiga duk Inda yaso yayi sata batare da an dakatar dashi ba , yafi karfin kowa duk yadda kake tunanin yan fashi sun zarta tunaninka basa ji basa gani akan aikinsu sai dai abinda na gani a dubana shi jaguwa yana fanshinsa ne akan masu kudi da azzaluman kasar nan , yana da hatsarin fuskanta it’s not easy to be known as the CEO of armerobber’s association .
wannan ya wuce da tunaninka ranka shi dade karka bata lokacinka gurin sanin ko shi waye ko matakin d’auka akanshi tunda har ya barka da ranka da lafiyarka sai mu godewa Allah domin shifa satarsa me dalili ne Kuma ya dade acikin harkar Kuma shi kad’ai yasan abinda ya taka wanda yasa ya gagari kasa da kasa har da jami’an tsaro suka kasa kamashi tanko gote ya numfasa kana yace “zan so yayi aiki a karkashina domin irinsa nake nema “bazai had’a Kai da Kai ba dan baya zalinci burinsa ya taimakawa talakawa marasa galihu Kai Kuma burinka ka danne hakin mutane da talakawa “wai boka ya kake min magana haka ne ? ” kayi wani Abu da zai kawo kanshi gareni “babu abinda zan iyayi domin duba taurarinsa ma kawai zai iya sa mutun cikin tashin hankali, kaima idan baka cire hannunka akansa ba zaka iya rasa komai naka jin abinda boka yace yasa tanko gote shiga damuwa bai sake cewa komai ba ya kakkabe bababan rigarsa ya baro gurin boka da zumar zai nemi had’in kan jaguwa ta kowani hali “.
Jaguwa na zaune tare da abokinsa da yaransa a gurin shakatawarsa gabansu kwalban giya ne yayinda kowannensu hannunsa ke rike da karan sigari har jaguwa suna tautaunawa akan sabon aikin da zasu fita zuwa garin Ogun state sai ga me gadinsa ya rusuna ya gaishesa tare da cewa “ga wannan dattijon daya zo neman taimakonka ya dawo ranka shi dade” “shi da nace ya dawo karshen sati amman dai shigo dashi kawai ” mai gadi ya juya da sauri jaguwa ya kashe sigarin hannunsa dan yana matukar jin kunyar wani yaga yana shan sigari eku tattara gurin nan kafin azo da dattijon nan take yabi umarninsa .ko cikakken minti biyar ba’a yi ba sai ga me gadi ya dawo tare da mutumin da yaronsa wanda bai wuce shekara talatin ba dattinjo na kokarin rusunawa
jaguwa ya tsaidashi yana nuna masa gurin zama “ka zauna baba dattijon ya zauna a Inda ya nuna masa yana rawar jiki, gbdy su jubi suka gaishesa ya amsa yana Saka musu albarka “d’ana ga yarona nazo dashi “jaguwa ya waigo ya kalli Inda yaron yake tsaye cikin wasu kod’ad’un kaya marasa fasali da sauri matashin saurayin ya dan rusuna ya gaishesa ya amsa da Kai tare da cewa ” ya sunanka sannan wani course ka karanta ? ” sunana aliyu Ahmed abinda na karanta lissafi wato accounting .ya bashi amsa cike da girmama.
shiru jaguwa yayi yana nazarin yaro kafin daga baya yace “shikenan zaka zauna damu ka zama dan aikenmu kafin lokacin da zan samo maka aiki inshallahu , dattijon najin haka ya fara hawaye yana godiya ” na gode na gode Allah yayi maka albarka “karka damu baba mu daman aikinmu kenan taimakawa marasa shi ,aiki kuwa ka fara hasasho ganinsa cikin jerin ma’akatan banking kasar nan yana gama fad’ar haka yasa aka dibo kudi masu yawa aka bawa dattijon “baba ga wannan kudin kaje dashi kayi bukatunka dasu, sosai dattinjo ya zube yana godiya kafin daga baya yay sallama dasu ya wuce ya bar d’ansa .”
D’akin taro ne dake cike da manyan jami’an tsoro kowannensu sanye da kankinsu na aiki police, yayinda gabansu ruwan roba ne mai sanyi da abun magana a hankali cp ya fara magana cikin tsadaddan turancinsa “
Daga ashirin da biyar ga watan daya na wannan shekarar ta 2021 zuwa ga karshen shekarar shadaya da muke ciki an samu farmarki ta’addanci a qalla ashirin da biyar a cikin garin nan, duk da k’okarin da jami’an tsoro keyi akan suga sun kama wadan nan yan fashi abun ya faskara wanda ni a nawa tunanin ina ganin akwai manyan kasan nan dake mara musu baya, taya zamu samu nasarar kama wannan mutumin dake jagoransu wanda shi ke shirya komai na ta’addanci ? cp ya karasa maganar yana kallon hoton jaguwa dake ajiye akan makeken table din gabansa .” yanzu haka wannan shine tantiri na biyu da ake nema acikin kasar nan idan kuma acikin garin nan ne shine na daya , jaguwa kenan duk wani sata da’ake wa manyan kasar nan da yan siyasa da hannunsa aciki abun mamaki yadda wasu daga cikinmu suke bashi kariya ta hanyar sanar masa da halin da’ake aciki, a offishin hukumar tsoro kuma suna yi masa duk wani alfarma daidai da wani mai fada aji a kasar nan “.
shi din dan ta’addanci ne kuma dan fashi da makami ne Kuma gashi yanzu yayi garkuwa da diyar minister shi din mutun ne me tsananin kyautatawa jama’a da tsananin tsoro allah da tausayi duk inda akace taimako zai bada yana da tsananin tausayin marasa shi sannan baya son zalinci yana daukarwa wadan da aka zalinta fansa idan gwanati taki yin komai, sai dai duk da hakan shi din babban me laifi ne agurin hukumar kasar nan yana zaune a unguwar magodo no 20 duk da ba nan kadai bane maboyarsa yana da gidaje dabam dabam , wadan nan bayanai da inda zaa samesu duka gasu nan a rubuce IPO investigation police officer ne ya rubutosu “. taya zamu samu nasarar kamasu ? ya karasa maganar yana daukar file din gabansa ya tsura masa ido .”
Cp na yin shiru mataimakinsa ya fara magana a natse batare daya tashi ba ” wannan duk me sauki ne sir tunda a halin yanzu maikacinmu ya Dade da shiga jikinsa dan haka duk halin da suke ciki zai zo mana cikin sauki, kaga kamasu bazai mana wahala ba duk wuya duk runtse sai mun ga bayansa domin bazamu marawa taaddancin da suke ma kasar nan baya ba, zamu bukaci ganin an kamashi cikin kankanin lokaci ya karasa maganar yana duban wanda ya turawa jaguwa jami’in sirri “dcp baba abare wanda aka kira da haka yace “yes sir ” ka tabbatar kasa ya shiga jikinsa sosai ta yadda zaa tattara duk wani mahimman bayanai akansa ya gabatar mana dasu da wuri “yes sir kace masa ya kiyaye da kyau domin shi din mutun ne mai hatsari sosai “inshallahu sir zanyi kokarin kuma zamuyi nasara kamar sauran lokutan baya a hankali suka cigaba da tautaunawa akan yadda zasu samu nasarar kama jaguwa da yaransa daga karshe cp ya sallamesu, kowanne ya kama gabansa.”