KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Yan fashi ya maimaita abinda tace cike da mamaki ?ta gyada masa kai kawai batare da ta sake cewa wani abu ba illa jikinta dake kyarma tsabar tsoro “okay Ki kwantar da hankalinki gidan nan akwai tsaro mai tsanani bana tunanin akwai damar da zai kawo yan fashi gidan nan , Ki tsaya anan ina zuwa ya karasa saukowa daga saman gadon qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi ,da sauri ta sauko ta biyo bayansa ,a hankali ya qarasa bakin window dakinsa ya tsaya yana kallon haraban gidan inda idanunshi ya hango masa wasu mutane sanye da bakaken kaya fuskarsu rufe da face marks kowanensu rike da bindiga mutun ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin katse wutar data bawa haraban gidan zuwa gurin securitys da wasu bangaren , juyowa yayi da sauri hankalinsa a matukar tashe suka ci karo da hajiya zainab dake tsaye a bayansa “,wayyo Allah yarinyata ta furta haɗe da yi hanyar fita, yayi saurin kamota jikinsa ya rungumeta tsam dan yasan halinta da mugun tsoro “,dan Allah ki natsu ya zaunar daita ya dauki wayarsa yana ƙoƙarin kiran number’s din police bai Kai ga samunsu ba yaji an banko kofar dakinsa da karfin gaske wiki wiki sukayi da idanu ,kamil ya harske dakin da wata ƙatuwar fitila mai mugun haske zaka ɗauka wutan lantarki ce jabir ya saita kan Alhaji Abubakar da bakin bindiga yayinda Anas ya saita kan hajiya zainab” move to the parlou’n ya furta yana tasa keyarsu , babu mutsu suka runtse idanunsu gam saboda tsabar tsoro a babban parlou’n gidan suka iske jaguwa zaune akan kujera mai zaman mutun ɗaya ya daura ƙafarsa daya kan daya yana girgizawa hankalinsa a kwance tamkar shine mai gidan, tun kafin su karaso inda yake zaune Jibril yasa bakin bindiga zai dagi keyarsu jaguwa ya dakatar dashi da hannunsa durkushewa ministar da hajiya Zainab sukayi bisa gwiwowinsu tare da kife kansu a kasa suna rawar jiki sai dai gabadaya hankalinsu naga kofar dakin tanweer.
Securitys dake on duty suka taso ganin wutan gidan ya dauke gabadaya suna tafiya da tochligt a hannunsu suna mamaki yadda wutan gidan ya dauke gabadaya ,suna gama karasowa gurin mahadar wutan suka ji anyi kansu da bakin bindiga take suka d’aga hannuwansu sama “ku durkusa bama son ganin fuskokiku babu shiri suka yi sujjada …
a hankali jaguwa dake zaune ya dubi Anas yana masa alama da hannunsa take ya fahimci abinda yake nufi dan haka ya soma motsa lip’s d’insa ” kayi kokarin kira police ko ?
da sauri hajiya zainab tayi sigil tace “,a’a..bamu kira police ba tayi maganar tana kallon mijinta ” well wannan ba damuwarmu bane nasan kunsan abinda ya kawomu adaidai wannan lokacin, muna bukatar bayyanansu a gabanmu yanzu yanzu bama bukatar bata lokaci”minister ya da’n d’ago ya kalli jaguwa lura da yayi shine ogansu yace “wallahi babu kudi a gidan nan shiru jaguwa yayi yana kallonsa batare daya sake yin magana ba sai Anas ne yace “babu kudi kace ? minister ya gyada masa kai yana marairaicewa “seach everywhere ka fito min da duk abinda ke cikin gidan nan take Anas da wasu mutun biyu cikin yaran jaguwa suka shiga duduba dakunan dake parlou’n hakan yasa minister yayi saurin cewa “, kuyi hakuri karku taɓa min lafiyar iyalina nasan kudi ne ya kawoku zan baku duk abinda kuke so muddin zaku barmu nida iyalinna ,gyaran murya jaguwa yayi take suka dawo inda yake jikin minister na rawa ya nufi dakin da yake ajiyar kudinsa Anas na biye dashi ghana most go uku suka fito dashi na kudi wani irin tsawa jaguwa ya bugawa minister” lallai ka cika mahainci wanda bai san darajar mahalincinsa ba ,kace babu pepa a gidan nan ? a rikice yace kayi hakuri wannan tsawar yasa tanwer dake kwance a d’akinta tana bacci ta farka a kidime ta zauna akan gadonta kafin daga baya ta sauko ta tsaya a bakin kofar dakin tana leke, hannuwanta duka tasa ta rufe idanunta jikinta na wani irin rawa saboda ganin bindigu dan parlou’n da haske sam bazakace ba wuta bane “anas …..
Jaguwa ya kira sunansa “Yesssss boss d’auko min wacan yarinyar dake lekenmu ya nuna kofar d’akin da hannunsa kai tsaye ya nufi d’akin , tana ganinsa ta saka wata razananniyar ƙara haɗe da mannewa ajikin bangon d’akin Anas ya karawa tochligt din dake rike a hannunsa haske tare da tsura mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta mai tsananin kyau da ɗaukar hankali kafin daga baya ya kai hannu zai damkota ta buge masa hannu tana kuka “don’t don’t ever touch me ta faɗa tana sake mannewa da bango duk yadda anas yaso ya fito daita taki yarda sai buge masa hannu take, ya sake kai hannunsa a zuciye yaji an rike tsintsiyar hannunsa ya juyo a hankali idanunsa ya sauka akan jaguwa “boss gardama take ko na dauketa da wuta ? girgiza masa kai yayi “kasan bana son haka “angama boss ya mika masa hannu dan amsar tochligt din hannunsa babu mutsu ya mika masa, da hannu jaguwa ya nuna masa kofar fita kana ya haske mata fuska da tochligt…
Dam……….. qirjinsa yayi wata irin bugawa da matsanancin karfi sakamakon ganin fuskarta ..
Duk ilahirin jikinta rawa yake , sai dai hakan bai hanata d’ago kyawawan Idanunta dan ganin mutumin dake tsaye agabanta ba wanda taji an kira da boss , take idanunsu ya tsarke cikin juna duk da face marks din dake fuskarsa hakan bai hanata ganin kwayar idanunsa mai zagaye da zara zaran gashi ido ba, runtse idanunta tayi tana nuna masa hanyar fita da hannunta murmushi ne ya bayyana akan labbansa cikin natsuwa ya kara taku biyu zuwa inda take makale da bango ……
DARLING’S????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
WRITING BY
BAGUDO& MIMI’S QUEEN
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
????️03
Matsawa tayi gefe da sauri jikinta na wani irin kyarma yanayin bugun zuciyarta bai saisaita ba , yanayin tsoratanta kuwa ya wuce tunanin mai karatu da kyar take fitar da numfashi qirjinta na kasa da sama ,murmushi ne ya sake bayyana akan kyakkyawar fuskarsa mai cike da annuri , cike da natsuwa da jin kai da izza ya matsota kamar zai shige jikinta batare daya sani ba , haka nan ya tsinci kanshi da kai hannunsa ya d’ago ha’barta ya tsurawa fuskarta kwayar idanunshi masu matukar kyau da haske cikin nata yana kallon kyakkywawar fuskarta da kwayar idanunta har jikinsu na gugan juna, wani irin kamshi ne na musamman ke tashi a sansar jikinsa tamkar wanda yayi wanka da ruwan turare , hakan yasa ta kasa kawar da idannunta daga nasa …
Sosai ya tsura mata kyawawan idanunshi yana kallon fuskarta, tunda yake rayuwa bai taɓa ganin halittar data masa kyau ba tamkar hallitar dake tsaye a gabansa , tun daga kan tsiraran lips d’inta, dara daran idannunta, hancinta komai nata ya tsaru ga ‘yan yatsunta zara-zara da take nuna masa hanya fita dashi , gaba d’ayabaya ya soma fita hayyacinsa ban da kallon halittar jikinta babu abinda yake ,a hankali idannunsa suka sauka akan saman qirjinta dake cike bam da dukiyar fulanin masu matukar kyau da haske a zahiri yake hango rabin nonuwanta da suka bulluko waje sakamakon rigar baccin dake sanye ajikinta masu matukar kyau ne da budaden wuya dan rigar ta zamo zuwa kafad’anta kamar up shoder ” ya Salam !’. ya furta a kasan makoshi yana lumshe sexy eye’s dinsa .