KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Anas na komawa ciki gida kira ya Isa office din jami’in tsoro na sirri “cikin sauri aka d’auki wayar ana dokin jin kyakkyawan labari daga bakin mai kira “hello ya’akayi IPO  an samu wani cigaba ne ?eh to an samu dan ya fita, yanzu haka naji babban amminsa yayi waya dashi yana kan titin akari isalo sai kuyi k’okarin kubi bayansa ku tsaya ta daidaita gurin idan Allah ya taimakemu sai ya dawo ta kan titin tunda shiga gidansa ya gagaremu sai mu kamashi a hanya yana cikin mota marcende baka 330 , Kai gskiya kamashi a gidansa zai yi wuya duk fa sanda nayi k’okarin tunkarar falonsa da bindiga dan arresting dinsa sai naga ilahirin gurin ya zame min kungurim daji da zarar babu bindiga ajikina sai na ga komai ya dawo daidai yadda yake a lisafinna iya bindigunsu kawai ke  shiga bangaren da suke  , eh nasan akwai katon sirri sosai a gidansa da shi karon Kansa wallahi nayita bibiyarsa akan sanin sirrinsa ban samu damar ganin komai ba yanzu dai  ayi k’okarin aje a tsaya agurin sir , okay shikenan sir Allah ya bada sa’a suka yi sallama .”

gudu jaguwa yake sosai akan titi isolo gbdy ya nemi natsuwarsa ya rasa ji yake kmr zuciyarsa zata kama da wuta haka ne ma yasa yaga kamar baya gudu tsaki yake taja akai akai duk jikinsa tsuma yake kwakwa luwarsa  ta  hargitse kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwar d’aya daga cikin ahlinsa , doguwar tafiya yayi ya k’araso daf  da unguwarsu
tun kafin ya k’araso ya soma Kiran number sadiq kaninsa  kira uku ya d’auka hankalinsa a matukar tashe “ka fito ka bude min get”  abinda ya fad’a kenan ya katse Kiran yana karasowa kofar gidansu sadiq har ya fito yana ƙoƙarin bude get da sauri ya bud’e murfin motar ya fito sadiq ya bashi hanya ya shiga ya maida get ya rufe “Lafiya father  kazo da tsakar daren nan? “lafiyar nan dai da sauki sadiq, ya fad’a yana dosar kofar part din ammi wacce tuni ta farka sakamakon jin muryarsa cikin bacci  dan window dakinta na daga tsakar gidan “Adnan ! ta kira sunansa a rud’e tana durowa daga kan bed dinta  ta fito tana k’okarin bud’e kofar tana sake Kiran sunansa ya amsa da” Na’am ammina Ina ganye magariyar da kika ta’ba nuna min ana yiwa gawa wanka dashi ? yana nan Lafiya kake nemansa da tsohon daren nan waye ya mutu ?ta tambayesa a rude “babu wanda ya mutu wani za’ayi amfani dashi domin karya sihiri ”   daga haka bata  sake  furta Komai ba ta juya ta koma cikin d’akinta da sauri sai lokacin sadiq ya sauke naunayen ajiyar zuciya Jin ba wani abu bane “suna tsaye ammi ta fito ta mika masa bakar ledar da gayen ke ciki ya amsa ya juya da sauri yana ce mata sai da safe “,Allah ya tashemu Lafiya Allah ya  tsareka ta fad’a tana kallon bayansa  “Ameen” ya amsa yana k’arasa fita daga gidan sadiq ya biyo bayansa ya kulle get .”

Wannan karon ba k’aramin gudun wasa yayi ba sai dai yana kawowa titin da mutun zai hau isalo road ya  karya stearing motarsa ya d’auki titin da zai Kai shi lawansi road adalilin faduwar gaba  daya  ji ya dirar masa  ,ya  Kai hannunsa d’aya  ya  kunna  wutar motar ta ciki ya Kalli zoben  hannunsa  nan yaga ya koma baki  daga ruwan zuman da yake iska ya furzar yana girgiza Kai ,gudu   yayi   sosai  cikin  kankanin lokaci  ya k’araso unguwar tun kafin ya k’araso get din gidan yake hon mai gadi ya bud’e masa ya shiga ya fito da mugun sauri daga cikin mota .
a falo ya wuce su anas suna ganinsa suka biyo bayansa Kai tsaye kitchen ya shiga suna kallonsa ya d’auki karamar roba ya tsiyaya ruwa aciki ya nufi  falonsa ya wuce bedroom dinsa kamar su biyosa sai Kuma suka tsaya cirko cirko suna zagaye falon, can suka ji ya kulle kofar nan suka fita d’aya byn daya ban da anas da ya nemi guri ya zauna zaman jiransa .”

Yayi duk abinda baba yace ya tofa acikin ruwan sannan yayi sama da jallabiyarsa ya hau kan gadon tana kwance tamkar matacciya sai dai zuwa yanzu babu wannan hayakin jikinsa na rawa ya sake Kiran layin baba yana dauka yace “baba babu wannan hayakin yanzu “okay to to shikenan ya fad’a a rud’e ya ajiye wayar ya tattarota zuwa jikinsa ya mannata a gefensa ya bud’e bakinta hakoranta sun cije guri d’aya ,a hankali ya dinga shafa mata ruwan maganin a fuska zuwa ilahirin jikinta yafi karfin awa d’aya yana bin jikinta da ruwa sannan tay atishawa mai karfi  sai dai idanunta a runtse suke ….

Naunayen ajiyar zuciya ya sauke idanunshi na kanta shi kad’ai yasan irin farinciki daya tsinci kanshi da numfashinta ya dawo gangar jikinta  ya rungumeta gam ajikinsa yana jin wani sanyin dadi na ratsashi ,
tausayinta  ne ya cigaba da ratsashi dan duk wani abinda ya sameta shine ya jawo mata, tana zaman zamanta tare da iyayenta ya daukota  “Allah sarki a she ba laifinki bane “a she tursasaki akayi? ” me yasa ? waye wanda yayi wannan aiki ?” me yarinyar mutane tayi muku kuka sa na zama silar rabata da budurcinta ? “shikenan Kunsa  na mayar daita bazawara alhalin bata cancanci hk ba ,kunsa nayi mata  tabon da har abada bazai gogu ba , wannan abu bai min dadi ba,” me yasa  tun tuni ban fahimci abinda ke tattare dake ba? wasu hawayen tausayin ta ne suka shiga zubo masa .”

da qunar zuciya ya sake  matsowa jikinta ya riko hannunta cikin nashi yana wani irin kuka  yana duban  jikinsa daya  kusanceta dashi “na Kusanceta da jikina “na zamo silar yi mata tabo a rayuwarta ..” me yasa  ban fahimceta ba na Kusanceta ? why why why Adnan !!! ? ya zabura ya mike tsaye tamkar mahaukaci yana hargagi ya shiga buga k’ansa da bagon d’akin yana nadamar abinda yayi mata “kafin kace me tunin jini ya balle a goshinsa ya shiga tsiyaya ya d’auki lokaci yana kukan nadama Yana kallon jikinsa yana tunanin cikin yan matansa wace wacce zata iya wannan  danyen   aikin  ? babu wacce  tazo  masa arai sai zahra ….”
ita kad’ai ce macen da zata iya komai akansa Kuma ita kad’ai ce ta gansa tare da tanweer ai kuwa babu shakka itace ,zata raina kanta a hannunsa ,
zan  bata  mamaki ,zai  mata abinda sai taji ta  tsaneshi a rayuwarta ya kai hannunsa  goshinsa  sakamakon dumin  da   yaji,  ya  kalla yatsansa  jini ya gani ya karasa ya d’auki tissue ya tsaya gaban mirrow ya goge sannan ya dawo ya d’auki rigarta yana kokarin saka mata nan ya ga digon  jini  had’e  da spam dinsa .
ya lumshe idanuwanshi qirjinsa na zafi abinda yafi tsanar mutane akanshi gashi shine ya aikata da kanshi ,cike da tashin hankali ya sauko  daga  kan bed din ya goge mata kasanta sannan ya zira mata riga ya  ɗauketa ya fito zuwa   falo   ya  wuce  anas zaune wanda ya zabga  tagumi yana ganinsa ya zabura  ya mike  ya biyosa  yana tambayarsa  jaguwa bai tsaya ba ya  nufi d’akinta  ya  shimfideta  akan   gado   idanunshi 
na  kanta  yana tsaye yana kallonta sai ga anas ya shigo d’akin cike da tashin hankali yana ganinsa ya janyo blanket ya lullu’beta yaja ya tsaya tare da rungume hannunwansa duka a qirjinsa cikin tsananin damuwa
anas    ya  zubawa tan Ido yana kallonta Ko cikakken minti biyar bai  yi ba sai ga jabir, jubi ,kamil sun shigo  .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button