KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Suna zaune sai ga zahra ta shigo cikin doguwar riga marun colour tana karairaya tana gama tsayuwa a tsakiyar falon onexpecting taji jaguwa ya mike  ya ɗauketa da wani gigitacen mari da sauri ta dafe daidai Inda ya mareta tana dubansa “ki fita rayuwata  Zahra , ki tsaya matsayinki”  zahra  tace “me yayi zafi haka Adnan ? “dazu anas ya kirani yake fad’a min abinda kake zargina akai amman ka sani ……
“wani marin ya K’ara kifa mata sai data ga taurari masu duhu “amman kasan me din ubanki ?”me zaki fad’a min na yarda dake maci Amana kawai,  daga karunwaci kin koma bin bokaye saboda ke katuwar jahila ce wannan ya zamo Karonki na farko ya Kuma zamo na karshe babu ruwanki da yarinyar nan wallahi muddin wani abu ya sameta sai na kasheki da hannuna , wai ma meye hadinki daita? ni kike wa kwakwa ni Kuma nace banayi ko dole ne  sai na aureki ?ya tambayeta yana sake tsare girar kasa da sama. “duk ta rud’e sai wani gumi take fitarwa cike da matsanacin firgici tace “ka yarda wallahi babu hannuna ci…ciki ” ta k’arasa maganar tana in Ina gani yadda yake mata mugun kallo yasa ta soma neman hanyar guduwa dan kallon  fuskarsa kad’ai ya Isa ya tsorota mutu da sa mutun ya shiga hankalinsa sam sam babu alamun wasa atare dashi kafa yasa mata sai gata ta zube kasa bisa gwiwowinta tana kallonsa cikin muryar kuka tace “ni kad’ai kake bi bare kayi tunanin nice na aikata abinda kake zargina? Ina Jin tsoron Allah Adnan bazan iya ……”shiiiiiiiii ! banason Jin komai d’aga bakin makira irinki .”
“Zahra!
ya kira sunanta muryarsa a tsarke ta zuba masa Ido tana amsawa da” Na’am “babu tsoron Allah”n daya halicceki acikin zuciyarki dan hk nasan zaki iya aikata komai akan cikar burinki ,masu kyakkyawan zuciya da tsoron Allah su suke tsoron aikata mugunta ke Kuma baki da ko daya aciki “yayi shiru yana numfasawa sannan ya cigaba da mgn “daga yau idan kika sake shiga harkata zan mugun baki mamaki kuma dan Allah karki cire hannunki akaina da duk wacce zaki ganni idan Kuma kinki yiwa kanki kiyamul lail zaki hadu da cuuttuka ,sannan zan ganar dake da yaren da zaki gane yana kaiwa nan yace ” ki tashi ki bani guri bana son ganin wannnan fuskar taki “.

“naji zan tafi amman kayi hakuri kayi bincike sosai akai muddin aka tabbatar maka  Ina d’aya daga cikin wad’an da suka aikata wannan laifin ka min hukuncin da yafi wannan “wani bincike zanyi bayan nasan babu me shegen naci a rayuwata kamarki ?ya matsota sosai ya cafki makoshinta idanunta suka yo waje “ki fad’a min gsky kece kikayi mata asiri ?ta shiga girgiza Kai alamun a’a “bazaki fad’a gsky ba ? girgiza masa Kai ta sake yi  anas ya taso ya rikesa karka yi kisan Kai Adnan “ka rabu daita  karka kashe yar mutane “kace mata ta fad’a min gsky da bakinta
“me yasa  tayi wa yarinyar mutane  asirin data kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra’ayi ba? ya fad’a yana filinging daita sauran kad’an kanta ya bugi bango anas yayi saurin riketa  yana bawa jaguwa hakuri .wani sanyayyayen numfashi Zahra  ta sauke da kyar tana jin dadi aranta burinta ya  cika tunda ya kusanceta rabuwarsu tazo duk nacinsa dole su rabu  ,abokansa kuwa da Ido suka bisa suna mamakin jin furuncinsa ,me yasa kika yiwa yarinyar mutane  asirin da ta kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra’ayi ba?  suka tambayi zukansu suna dubansa  fuskokinsu d’auke da qarin bayani .

“Anas kaji abinda yake fad’a , dan jarabansa ya ciyosa ya kwana  da  yarinyar mutane shine zai d’aura laifina akaina , kasani babu  hannuna  acikin wannan aika aikan  ” ,jaguwa  juya mata baya  ya tsuke fuska alamun bai son jin komai daga bakinta muryarsa a tsawace yace “anas ka sallameta daman  Kaine kake gayyatota  zuwa gidan nan ” da sauri anas  ya riko hannunta ya nufi kofar fita daita “anas ka sakeni na fahimtar dashi gaskiya “bazai ta’ba fahimtarki ba kije kawai dan Allah nima daga yau karki sake kirana na yanke muamula dake bazan Kara kiranki ba banason na samu matsala da abokina, aminina ,farincikin rayuwata .
fixge hannunta tayi daga cikin nashi adaidai lokacin da suka fito zuwa haraban gidan ta tsaya a hassale tana  dubansa “ka dade baka daina kirana ba ,bazan  kiraka ba shima bazan kirasa ba Amman na rantse sai Adnan ya dawo ya nemeni da kansa ka rubuta ka ajiye a Inda bazai goge ba …”

Mmn sudais????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

PAID BOOK
FREE PAGE
 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️16

“Kenan   da   gaske  kin aikata  abinda   yake   zarginki   akan shi  ?” idanunta  da suka  rikid’e sukayi  jazur  ta cigaba da  kallon   anas  wanda yake  tsaye  a  gabanta yana  huci kamar zaki  dasu “eh  na  aikata  Kuma   bazan  tsaya  iya  nan ba  ta  fad’a a matukar fusace  ”  zan   d’aura  daga   Inda  na fara , zan tabbatar  da na  azabtar da   yarinyar  nan   da azaba  mafi   muni   , ba  dai  duk akanta   ya mareni  ba?”  ya mareni  akanta anas , ya ci  mutuncina   akanta  ya wulakantani a rita lori akanta ,wallahi   ya   kwana da sanin   zan fanshe  duk abinda yayi min  akanta   ‘zan  mata  azaban   da  rad’ad’insa  yafi  zafin  dalma ,  zan   rikirkita  mata  rayuwa  zan…..”saurin   dakatar  da  ita  yayi ta  hanyar  buga  mata wata razananniyar  tsawa  yana cewa  “enough !
“karki  fara  zahra  dan bazaki   ci  riba  ba , wad’an  da  ma  suka fiki  sunyi  sun   hakura  sun barshi  dan ba zasu iya ja dashi  ba   domin shi din  dokin  tsere ne  bazaki iya  karawa  dashi ba ,shi  guguwa  ne idan ya  tashi  zai  tashi da rayuwarki  , zai  juya  rayuwarki  daga sama  zuwa  kasa ki rasa gane  kanki ……”ya k’arasa maganar  yana nuna da yatsansa .

“Zahra !

Ya  kira sunanta cikin tsananin  ‘bacin rai ” ki tsaya   daga  Inda kike idan   ba  haka ba  ki shiryawa   gudun  tsere da  mutuwarki  , dan akan  ki ta’ba wannan  yarinyar  gara kin  rungumi mutuwa  da hannuwanki.” Adnan  yace   bai sonki ya nuna  azahirin   bai sonki, tunda  ba  tare aka halliceki   da   soyayyarsa ba  ya kamata    ki  hakura ki rabu dashi ki  tsira da rayuwarki  dan  akan  yarinyar nan  ba zai raga  miki  ba  zai iya  destroyed  din rayuwarki,  ki  manta da kin ta’ba muamula da Adnan a rayuwarki  “. wannan  shine  abinda  zan  fad’a  miki   idan  Kinga dama ki d’auka ki  cire hannunki  akan  mugun nufinki  ki zauna  lafiya idan kinga dama ki cigaba kece zaki kare rayuwarki a  nadama  “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button