KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Tunda ya soma magana zuciyarta ke bugu very fast ta kafe shi da idanunta ta cigaba da kallonsa ,a yau gbdy babu sauran burbushin tausayin data saba hangowa acikin kwayar idanunshi a duk lokacin da hargitse ya shiga tsakaninta da adnan , yau ce rana ta farko da anas yayi hannun riga daita . ka’fafunta ne suka kasa d’aukarta ta durkushe kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tana cewa “kasan kuwa yadda nake ji a zuciyata ? “maganganunka suna huda min zuciya, me yasa zaka nisantani da Adnan ? ya kalleta cike da matsanacin bakinciki dan gbdy ya fuskanci bata da niyyar saduda shi kuma a yau gbdy babu wannan tausayin da yake ji nata, da tayi silar rabashi da masoyinsa da yafi qauna akan komai a rayuwarsa gara ya yakiceta ta karfin tsiya sunyi hannun riga daita “amman kai kana ganin zan iya rabuwa da Adnan dan yace bai sona ?ko kana tunanin zan iya daina sonshi ne ? Me yasa zaka ce na manta da soyayyata ? “haba anas idan kayi min haka baka kyauta min ba ,yanzu adalci ne daka nuna kafi bukatar rabuwarmu dashi ?
ya gyada mata Kai alamar”eh! ” cikin firgici da tashin hankali ta shiga girgiza masa kanta sannan ta cigaba da magana “ada tunanina kana sona da Adnan ne a she duk ba haka bane karya ne baka qaunata dashi ? to bari kaji in fad’a maka maganganunka ba zai sa na fasa duk abinda nayi niyyar aiwatarwa ba ko da kuwa zan mutu .” ta k’arasa maganar tana sheshekar kuka “karki fasa zahra bazan baki hakuri ba kije kiyi duk abinda zakiyi amman Ina tabbatar miki wahalar banza zakiyi dan ba zaki yi nasara ba hasarar kudinki da lokacinki kawai zakiyi yana gama fad’ar haka yace ki tashi ki ‘bace min da gani yadda Adnan baya son ganinki nima hakan take gareni “.
Batace masa komai ba ta mike da kyar ka’fafunta na rawa ta juya ta soma tafiya hawaye masu zafi da ciwo na sake zubo mata akan quncinta , zuciyarta bata ta’ba karaya ba atun sanda jaguwa yake furta mata kalma bai sonta sai a yau da anas ya sake maimaita mata , duk da ba yau ta saba jin kalmar baya sonta daga bakinsa ba amman ciwon na yau daban ne a cikin zuciyarta sannan ya mugu mugun tsaya mata arai ya d’aga mata hankali ya dagula mata lissafin tsarin rayuwarta data shirya dashi , Kuma duk runtsi duk wuya sai tayi abinda zai furta mata Kalmar so da bakinsa , sai ya dawo yayi kuka da idanunshi yana rokon ta amshi soyayyarsa, ko zatayi yawo tsirara sai ta aureshi idan Kuma hakan bai samu ba zata saka rayuwarsa ta quntata . “
anas ya yabi bayanta da kallon bakinciki ,ya rasa wani irin naci ne irin nata , mutun ya nuna miki da Ido ya nuna miki da jikinsa har ya fito ya furta miki amman ki tsaya kina hauka akanshi, tsaki yaja ya juya ya shiga ciki falon zuciyarsa cike da takaicin abinda zahra tayi . Inda ya bar jaguwa anan ya iskeshi tsaye a tsakiyar falon rungume da duka hannuwansa a qirji sai faman cika yake yana batsewa .
jikin anas a sanyaye ya samu guri ya tsaya kusa dashi ya dafa kafad’arsa, jaguwa ya juyo ya kalleshi yana cije lip’s dinsa na kasa a hankali ya sake juya masa baya yana furzar numfashi kana yace “ka gama munafurcin ?wani irin bugu qirjin anas yayi da karfi ” a hankali sautin muryarsa ya fito yana cewa”idan zanyi munafurcin kowa bazanyi naka ba, idan zan cuci kowa bazan cuceka ba, kama daina min irin wad’an nan abubuwan dan wallahi suna Kona min rai da mugun tayar min da hankali “.
Jaguwa ya waigo ya fuskanci anas sosai yana sake furzar da iska mai zafi daga bakinsa “muddin kana son zuciyata ta cigaba da amincewa da Kai sannan na daina fad’ar haka akanka anas ya zama dole sai kayi hannun riga da zahra bana qaunarta bana qaunar ganinku tare muddin zaka kasance dani sai dai ka za’ba ko ni ko ita ? taku daya biyu yayi ya matsa daga kusa da anas yana tafiya a hankali still yana rungume da hannunwansa.
“jaguwa !
anas ya kira sunanshi cikin yanayi na firgici da tashin hankali , idanu kawai jaguwa ya tsura masa batare daya amsa masa ba” shakka babu duk duniya nafi sonka akan kowa, Ina qaunarka fiyye da ni kaina maganar zabi ma bata taso ba dan kasan waye zabina” yayi mgnr hawaye na ciccikowa a idanunshi “Kai ne zabina Adnan Ina sonka fiyye da kowa da komai nawa ” tautausan murmushi jaguwa ya sakar masa yana mai Jin sanyi acikin zuciyarsa , cike da farinciki ya mika masa hannunsa
da sauri anas ya mika masa nasa hannun suka rungume juna suna sakin numfashi atare , jabir , jubi ,kamil da suke zaune duk sukayi shiru suna dubansu dan ba wannan bane karon na farko da suke samun matsala a tsakaninsu kuma cikin kankanin lokaci suke daidaita kansu.
kuka sosai anas yake jaguwa na shafa bayansa kamar wani karamin yaro “is okay anas na sani , nasan kana qaunata da gsky kmr yadda nake qaunarka am really sorry for my active har cikin zuciyata nake jin qaunarka , Kai zinari ne acikin zuciyata Ina sonka anas “Nima Ina sonka kyakkyawan abokina had’e da qauna mai karfi , cikin kankanin lokaci komai ya daidaita a tsakaninsu suka samu guri suka zauna cikin sauran abokansa nan hira ta barke a tsakaninsu .
su jubi sun so kwarai su sake samun qarin haske akan maganar jaguwa ta d’azu akan yarinyar amman yaki bada dama amman duk da haka sai da kamil yayi magana Cike da kulawa kamil yace “anyi maka tambaya akan yarinyar nan ka wani share mutane ” to me yasa meka a goshi Kuma ? ko baku lura da goshinsa ba ?ya fad’a yana kallonsu d’aya byn daya ,kun san halin miskilancinsa ai ba lallai ya fad’a ba ni tun jiya na gani sanin halinsa yasa na share inji cewar jubi .
“ku manta da wannan maganar idan akwai wacce ta fita mahimmam ku kawo muyi kawai ” anas ya fad’a dan jaguwa wayarsa ya d’auka yana duba sakonin mutane , basu tashi a falon ba sai da suka tsara yadda tafiyarsu Ogun state zata kasance a gobe .
” Yadda suke tsara komai akan aikinsu haka Suma jami’an tsaro dana sirri suke shirya yadda zasu kamasu a yanzu ma Asst Commissioner of police ne ya kira layin d .c .p baba abare wato lawan numan byn ya d’auka suka gaisa ya fara magana cikin zafin rai ” wannan mutumin bai kamata a barshi har zuwa wannan lokacin batare da anka mashi ba , yayi mgn tare da yin shiru “eh to haka ne amman abinda nafi bukata a Kara saka Ido sosai akan duk wani motsinsa da shiga da fitarsa bama iya rayuwarsa ta fashi ba hatta rayuwarsa ta duniya ma sai na tabbatar da ta ru’bance idan yazo hannu , sun dauki lokaci mai tsawo suna tautaunawa akan jaguwa da yaransa kafin daga bisani suka yi sallama. “