KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bai jima da kwanciya ba aka soma knocking kofar falonsa , yana daga kwance ya bawa mai yin knocking ɗin izinin shigowa eku ne ya shigo cikin falon hanunsa riƙe da farar leda, cike da girmamawa ya rusunawa ogan nasa a natse Jaguwa ya mike zaune ya zura silifas ya amsa ledar yana masa godiya eku ya juya ya fice daga falon.mikewa tsaye yayi ya fito ya shiga ɗakin tan batare da yayi knocking ba kamar yadda ya saba koda yaushe zai shiga Kai tsaye ne , sai kawai ya tura ƙofar ya shiga ciki, tun sanda ya kawota gidan yake jin haushi Kansa da bautan da yake mata amman a yau din jin zuciyarsa yake fessss akanta zai iya mata komai ciki kuwa har da zama bawanta .
Tana kwance akan gado ta kwanta ruf da ciki, bacci ta keyi har lokacin hankalinta a kwance, murmushin gefen baki yayi kamar tana ganinsa haɗe da aje ledar hannunsa” sarkin rigima da rashin kunya ya fad’a a ransa , har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya yana kallonta tun daga yatsun kafaunta har zuwa kanta komai nata abun burgewa ne , ahankali ya taka zuwa inda take kwance, tafin kafansa d’aya yasa ya ɗan shafa tsakiyar kafarta .
azabure ta farka ta zauna tana murza idanunta dan har lokacin Jan da sukayi bai baje ba , sake kallonta yayi, “Ki tashi kije kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah , ke fa na lura sallah bata dameki ba dan zaki iya wuni bakiyi sallah ba ki kuma kwana bakya damuwa” yayi mgnr yana mai tsareta da sexy eye’s dinsa.”
Tsura masa idanunta tayi tana kallonsa tana Jin haushin abinda yake mata sai ya fad’awa mutun mgn yayi kmr bashi yayi maganar ba, saboda yanda yake fizgo mgnr da kyar Kallon agogon d’akin tayi yanzu ne ma hud’u ta wuce muryarta a raunane tace “gara ni ko banyi sallahr akan lokaci ba zan rama Kai fa ?meye amfanin sallahrka akan lokacin tunda kana aikata aikin haram, wad’amuhu haramun ,washarabahu haramun wa guziya bil haramun wa’anna …..”ki min shiru anan stupid ” ya fad’a a tsawace , ana tausayinki bakya tausayawa kanki “nace ka tausaya min ne? ko nace ka cigaba da rikeni dole ? Ko nace dole sai ka zau…..”Idan kin sake furta wata kalma anan sai na tattakaki idan km kin mutsa bismillah kiyi ” yana gama faɗan haka ya fice daga cikin ɗakin ransa a bace, gsky yayi mugun sakewa yarinyar dayawa shiyasa ta rainashi .
Saukowa tayi ta shiga bayi tai alwala ta fito tayi sallah tana idarwa ta mike ta Isa gaban mirrow ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, robobin take away ne acikin har guda uku, ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, kad’an taci dan zazzzabi take ji sosai bata jin dadin bakinta ta sha ruwa kad’an .
kamar ta koma ta kwanta ta tsinci kanta da fitowa, kanta babu dankwali ta fito zuwa falo da kyar take taka ka’fafunta , yana tsaye agaban tv ya bawa cikin falon baya yana ƙoƙarin danna code din bude wayarsa , jin motsin mutun a falon yasa batare da ya juyoba yace. “waye ? “Waye byn wacce ka sato ka ajiye a gidanka ita ce ta fito ta sha iska tayi mgnr da kyar tana kokarin zama akan kujera “shekaru sun ja wallahi ya kamata ka tuba ka daina harkar fashi ,nasan da mahaifiyarka tasan wannan aikin kake yi da bata yi alfahari da Kai ba a karshe kashe kanta zatayi dan bakinciki .”
A matukar fusace ya nufo Inda take tamkar wani mayunwanci zaki ya damki wuyanta yana Shirin danne makoshinta ya fasa saboda zafin daya ratsa tafin hannunsa ya tsura mata Ido kawai yana kallonta “ka shaki ne mana ai ni yanzu a shirye nake da mutuwa gara min mutuwa akan cigaba da zama da Kai ,a farkon had’uwa ta da Kai naji duk duniya Kai mutumin kirki ne ,Kai ne mutumin da zuciya da gangar jikina suka mace akansa saboda a tunanin zuciyarka me kyau ce a she ba haka bane mugun ciwo ne daskare a zuciyarka wannan mummunar sana’artaka yafi min komai zafi acikin zuciyata wanda adalilin haka yanzu babu kyakkyawan zaton da soyayyarka acikin zuciyata sai zallar tsana ,na tsaneka tsanar da zan iya ganin bayanka ka rubuta ka ajiye muddin na bar gidan nan sai nasa ka shiga ha…….”
“karya ne ” ya fad’a a tsawace yana nuna ta da yatsansa “karya ne baki Isa ba , baki Isa kisa akamani ba how could you tell someone tanweer ?” you can’t do that , bazaki iya ba sannan jaguwa ba zai kamu ba cikin sauki ba sai dai wani mutun dabam, da zan kamu da ban Kai iyanzu ba” yayi mgnr yana furza mata iska a fuskarta tayi saurin runtse idanunta gabanta na faduwa , ya juya mata baya tare da rike kugunsa da hannu d’aya ya fara zagaye falon zuciyarsa na tafarfasa can ya juyo a matukar fusace “and kikace me byn zaki sa na shiga hannu ?” Kin tsaneni tsanar da zaki iya ganin bayana Shima karya ne zuciyarki bazata iya rabuwa da soyayyata ba yadda kika furta cewar kina sona haka zaki tabbata da sona a karshe ciwon sona ne zai kasheki saboda Ina ranki ,na shigeki shigar da bazaki iya cireni a ranki ba ,zaki je gidan wani da tarin soyayyata gangar jikinki za’a Kai gidan wani zuciyarki kuwa tana nan …..”ya nuna qirjinta daidai saitin zuciyarta .
wani irin sarawa kanta ya dinga yi da karfi kmr zai ra’be gida biyu tayi matukar firgita da Jin mgnr shi , ta d’auka zai tsorata da maganarta sai dai taga sa’banin haka atattare dashi sam shi din ba matsoraci bane zuciyarsa a dake take ,kallonsa tayi tare da ciza lips dinta batare data sake yunkurin cewa komai ba “ki tashi ki ‘bace min da gani banason ganin wannan banzar fuskarki, karki qara kuskuren zuwa Inda nake sannan duk abinda kikaga Ina yi miki karki d’auka so ne , ba so bane tanweer dan ko digo d’aya na sonki babu shi acikin zuciyata bakya cikin irin tsarin matan da zan so , idan Kuma kin koma gaban iyayenki dan Allah karki fasa idar da nufinki akaina kiyi Ina jiranki wani irin zafi da ciwo kai ne me karfi yayi mata diran makiya gbdy jikinta ya sake d’aukar zafi tayi karfin halin dafe kanta cike da sanyi jiki ta mike ta nufi hanyar komawa d’aki sai da tayi da tasanin fitowarta .”
da kyar ta dinga d’aga ka’fafunta da
idanu ya bi bayanta yana kallonta rai a ‘bace har ta bace wa ganinsa sannan ya d’auke idanunshi yana fesar da iska zuciyarsa ban da zafi babu abinda take sai faman tsaki yake ja da karfi ya fad’a kan kujera ya runtse idanunshi tare dafe goshinsa cikin haka abokansa suka shigo suka samu guri suka zauna ganinsa haka yasa suka fara tmbyrsa abinda ke damunsa shiru yayi yaki cewa komai sai tsaki yake ja anas ya dafa kafadarsa “meye damuwarka Kuma ? Still shiru yayi yana ciza lip’s dinsa jabir da jubi suka tashi suka fita dan sun San tunda yayi haka ba magana zai yi ba “ya kamata ka rage damuwar nan jaguwa nasan duk damuwarka bata wuce akan yarinyar nan ba “Ina matukar tausayin yarinyar nan anas amman ita burinta bai wuce taga bayana ba
yayi mgnr a fusace idanunshi sun yi jajur “kayi hakuri nasan da haka nasan kana tausayinta da qau….” wani irin kallo yayi masa wanda yasa anas ya hadiye abinda zai fad’a “na sha fad’a maka ka daina cewa Ina son yarinyar nan amman tunda haka kake tunani ka zuba Ido zan baka mamaki”