KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

 gudu  motocinsu  suke  sosai akan titi tare da jiniya ,kowacce mota ta gansu  sai  ta  kauce ta basu  hanya  ,irin  gudun da  sukayi  yasa  cikin kankanin  lokaci suka k’araso 1829 suka  faka  motocinsu suka  firfito cikin sauri  wasu suka nufi   babban get  din   plaza  din , yayinda wasu suka  tsaya abakin kofar motocinsu  rike da  bindugu   suna mazurai kamar  wasu  zakuna ,mutane kuwa tuni suka fara bawa kafarsu iska kar tsautsayi   ya  rutsa dasu  .
a hankali  police  suka kusa cikin plaza din  ,bincike  suka  fara yi kafin  daga  baya suka bukaci  ganawa da manager   gurin  , Kai  tsaye  aka Kai su Inda yake , tun kafin su fito da Id card  dinsu ya  fahimce su din su waye ,  nan take ya rikice  yana  kallonsu .Jimi’an  tsaro  ne suka nuna masa I’d card  “akwai wani mai laifi daya shigo plaza dina a mintunan da suka gabanta ko zamu iya ganin cctv camera dinku ?muryarsa na rawa yace babu matsala yalla’bai  ya juya ya soma  lalu’bo daukar yau dan Daman a qunne yake , a hankali suke kallo har ya kawo zuwa sanda suka shigo babu wanda ya shigo  me irin  fuskar  da  suke  nema  tare da yarinyar dan haka suka juya  cikin sauri  suka shishiga motocinsu suka nufi wani  branch  din dake ikotun .”

Jaguwa  na isowa gida yayi parking yana ƙoƙarin bud’e mota  domin ya  fito  da sauri tanweer ta rike shi gam  ajikinta   “dan Allah kada ka sake shigar dani cikin  gidan  nan  “ya  waigo a natse  sai dai a fusace yake   kallota sai daya d’auki second biyar yana kallon  sannan  yace “wai meke damun tunaninki  ne ?”me ya samu  gidan  nan   da kike son barinsa bayan rayuwarki ake k’okarin karewa ?
Tayi shiru tana kallonsa  da nazarin maganarsa kullum maganarsa kenan rayuwarta yake son karewa “ka fad’a min waye wanda yake son d’aukar rayuwata da har kake k’okarin karewa  ?  tayi   masa tambayar jikinta na rawa tare da  sheshekan kuka.”ganin  yadda ta rikice  yasa  ya kamo hannunta  ya  rike  cikin nashi  gam suna jin dumin juna   “ki  natsu zan  fad’a miki amman ba yanzu ba “ni dai ka fad’a min ko waye shine samun kwanciyar hankalina  da samun natsuwar zuciyata, Idan ma
ta kama  zan hakura da gidanmu  na cigaba da zama da Kai ,”ko Kuma ka siyo min sabon layi ka had’a min  waya sannan  ka fad’a  min ko waye  sai na fad’awa mahaifina  a d’auki  mataki   akansa , wallahi nayi  maka alkwarin  bazan  fad’awa  kowa ba .”

Yayi  d’an murmushin gefen baki  wanda  ya  bayyana  ainihin  sirrin kyawun  da Allah yayi masa “Ina  ce  kince  zaki  tona  min  asiri  byn kin bar gidan nan ? “tayi saurin  girgiza masa  Kai alamun a’a “bazan yi ba na maka wannan alkwarin duk runtsi duk wuya bazan aikata hakan gareka ba muddin ka fad’a min  “.
“kada ki damu idan kin shirya  fad’awa  duniya  kiyi   karki   fasa , idan kin koma  gida ki tara gbdy ‘yan jaridan garin nan ki sheida  musu cewar Adnan dan fashi ne abinda nayi Imani dashi   Allah  bazai  basu  nasara akaina  ba ,  mahaifiyata tana tsaye  a  kaina da adduointa haka mutane  da dama suna min addua , duk da Ina  aikata  zunubai   Allah zai   tsareni   daga sharrin duk wani  jami’n  tsaron  albarkancin  adduar mahaifiya data mutanen kirki  .”
shiru tayi tana  kallonsa hawaye na gangaro mata cike da sanyin jiki  ta zare hannuwanta dake  cikin  nasa  ta soma k’okarin zare jikinta daga garesa  ,yana  kallonta tayi baya da kujeran da take zaune ta  maida jikinta ta kwanta  tana mai runtse idanunta ,  yatsun hannunta ya kamo  bai san yadda akayi ba ya tura cikin bakinsa  ya  fara tsotsa , wani iri ta dinga ji a sansar jikinta kmr ana zarar ranta , tayi k’okari cirewa ya rike yatsun  da  karfi  yana cigaba da tsotsa kamar ya samu sweet  sai daya tsotsa son ranshi sannan ya cire bakinsa ya ciro hanky ya goge mata hancinta dake digar  jini  yana cewa “ki kwantar da hankalinki zan  fad’a miki ko waye amman  ba yau ba   “. yana  gama fad’ar haka ya sakar  mata  hannu ya    bud’e  murfin motar ya   fito ya  zagayo  bangarenta da  take  ya  bud’e mata  ta fito  jiki a sanyaye,  ya d’auki ledar maganin  da aka  basu   ta dubeshi fuska da hawaye  .
bai tsaya bi ta kanta ba ya riko    hannunta  ta turje  alamun bazata ba ya juyo ya watsa mata  idanunshi fuskarsa a d’aure  “karki  min  taurin kai ” ya  fada tare da sake  juyawa  suka shiga cikin  gidan bakinsa d’auke da  addua (bismillahi  walajna
wa  bismillahi  kharajna wa’allahi rabana tawakkalna ) tana jinjinawa  girman  iliminsa,  gashi tantiri  gashi  malami   ta  fad’a  acikin  ranta .

Kai tsaye d’akinta  ya shiga daita  ya  kamota ya  zaunar daita abakin gado ya janyo  kujerar  madubi ya zauna yana  bin  d’akin da Kallo duk ta hargitsa   d’akin ko d’azu daya shigo yaso yayi magana yanayinta yasa ya share    ya  girgiza Kansa  sannan ya  fuskanceta  ,baya  jin dadin yadda  take d’aga  hankalinta  akan gida ,
shi  bashi  da niyyar  cutar daita , ko abinda ya faru daren  shekaranjiya ma  ba yin  Kansa  bane itace sila ,  tillastawarta ce    ta  janyo  hakan ta faru   ban cin haka babu abinda zai kai shi aikata zina daita.
“tan …!
Ya kira sunanta cikin kasalalliyar muryarsa yana  sake  kamo  hannunta tare  da kafeta da  tsumammun idanunshi  masu  kashe mata sansar  jiki , d’ago idanunta tayi ta zuba masa tana sauraronsa tare da jin wani iri a sansar  jikinta duk sanda zata kalleshi sai taji wannan yanayi wanda babu tantama na qunar da take masa ne . “wanda  ya  tura mu fashi gidanku  bashi da  hannun  cikin zamanki  tare damu , rikeki da nayi Kuma nayi amfani da maganar da mukayi  dashi  a  karshen maganarmu  cewa “yayi  yana da wasu  target  akanki  a dawo dake  ya aiwatar da nufinsa  wannan  shine dalilin da yasa  na rikeki  ba dan raina na so ba “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button