KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Dan ranka na so dai ka rikeni idan ba haka ba meye aciki ? tayi maganar a matukar fusace ” ka mayar dani Inda ka d’auko ko ka fad’i wanda ya turaku gidanmu kawai a wuce gurin , ya runtse idanunshi yana nazari wasu abubuwa akanta .
ta dubeshi idanunta cike da ruwan hawaye “adnan ka d’auke ni a daren nan ka mayardani gidanmu dukkanin alamun sun nuna min iyayena na cikin tsananin damuwar rashina da…. ….”
“na sani Kuma zan mayar dake amman ba yau ba ki bani lokaci wallahi zan mayar dake akwai binciken da nake da zarar na gama zamammu tare zai zama tarihi “.
ta matso kusa dashi sosai har gwiwowinsu na gogan juna “naji amman dan Allah ka sanar dani Wanda ya tura ku gidanmu fashi ?ya girgiza mata Kai sannan yace “idan ma kika ji ko waye ba lallai ki yarda ba, Killa Kuma ma kiji kin tsanani kanki sannan tabbas wasu rigingimu zasu faru saboda kusancin dake tsakanin mahaifinki da wanda ya bamu aikin .” ta kamo hannunsa ta rike gam cikin wani yanayi “cikin dangin dad dina ne ko na mum dina ke son ganin bayan iyayena da ni kaina ? ya girgiza mata Kai alamun “a’a”to sanar dani dan Allah zan barwa cikina bazan ta’ba fad’awa kowa ba “.
Shiru yayi yana nazari akan lamarin ya fad’a mata ne ko ya shareta “abinda yasani tabbas idan batun
ya fito ya sa’bawa dokarsu domin a aikinsu babu wannan tsarin ,duk runtsi duk wuya ba’a tonawa juna asiri tunda tun farko da wajewa ake tsara komai ba’a juyawa juna baya.
ta katse masa tunani ta hanyar cewa “kana ganin zan iya tona maka asiri ne ?” Allah na dai fad’a ne amman bazan iya aikata hakan ba. “na sani dan fad’awa soyayya ba abu ne me sauki ba da har zaki tona asirin masoyinki I know you can’t do that to me tanweer bazaki iya fad’ar komai akaina ba saboda qaunar da kike min.”
ta lumshe tsumammun idanunta na second biyu tare da jan tsaki acikin zuciyarta dan muddin tayi a fili balai zai mata a hankali ta bud’e idanunta akan kyakkyawar fuskarsa “ba wannan story din na tambayeka ba ,ka ajiye batun wani soyayya dan a yanzu babu ita acikin raina buqatata ka min bayani wanda yasakaka aikin bana son jan aji da salo tayi mgnr tana murgud’a masa k’aramin bakinta .yayi murmushin gefen baki yace “to da gaske zaki rufa min asiri agurin iyayenki ? da sauri tace “me zai hana in bukatar hakan ya taso ?”
“sannan Ina fatan zaki fahimceni ?” ta gyada masa alamun zata fahimcesa, shiru tayi tana jiran ya faiyace mata Komai kawai taga ya zare hannunsa ya mike tsaye tare da zura hannuwansa duka cikin aljihunsa , a hankali ya juya mata baya yayi taku zuwa daf da kofar bayinta ya tsaya tare da waigowa yace “ni zaki yaudara ko ? ta girgiza masa Kai alamun “a’a “karya kike tanweer yaudarata zakiyi dan zuciyata bata yarda dake ba duk da d’arurar soyayyata dake cikin kwayar idanunki da zuciyarki kina son na fad’a miki wanda ya tura mu fashi gidanku sai ku taru ke da jami’an tsaro ku cutar damu ko ?
yana rufe baki yaji ta rungumesa tsam ta bayansa tana cewa “wallahi kaji na rantse maka bazan sheidawa kowa ba ,bazan zamo me Saka hannu gurin cutar da kai ba ,ya juyo daita gabansa suka fuskanci juna “dame zaki gamsar dani bayan tun farko kice da bakinki kika fad’a min zaki tona min asiri ?” ta tsugunna gwiwowinta biyu a kasa “,ka yarda dani Adnan na rantse maka bazan aikata hakan ba “. ya tako a hankali ya tsugunna a gabanta “na sani bazaki fad’a ba amman ni ba mahaukaci bane da zan fad’a miki wanda ya tura mu a aiki gidanku , babu wannan ajandar acikin aikinmu ko gaban alqali za’a Kai d’aya daga cikinmu da wahala ya fad’a ,kada ki damu ki bar son jin komai gida ne dai zan kaiki a duk sanda wa’adi ya kai ya fad’a yana janyota jikinsa ya makaleta tare da Kai bakinsa daidai kunnenta “ki K’ara natsuwa da jin dumin jikina .”
Tayi shiru zuciyarta na quna da tuttukin bakinciki ,duk abinda take tana yi ne dan ya fad’a mata wanda ya bashi aikin amman shine zai rainawa kansa hankali yace ita ya rainawa ?” cike da matsanacin bakinciki fixge jikinta tace ” kar Allah yasa ka fad’a kuma Allah ya Isa da rungumata da kayi ban yafe maka ba mugu kawai me zuciyar dutse duk irin rantsuwar dana yi maka bai sa ka yarda dani ba saboda muguwar zuciya irin taka .” cikin dariya ya sake janyota jikinsa sosai ya rungumeta tsam yana busa mata numfashinsa tare da cewa “kada ki damu da irin zuciyata dan babu abinda zai qareki dashi Allah ya Isa Kuma daman allah isashe ne ko baki ce ba , wayonki yayi matukar burgeni I love it keep it up yayi mata kiss a goshi sannan yace “zaki cigaba da zama da Adnan har zuwa sanda yaga damar maidake gidanku sannan kiyi k’okari ki rage wannan soyayyar da kike masa idan ma da hali ki cireta gbdy ya saketa ya koma jikin window ya tsaya yana kallon farfajiyar gidan kusan minti biyar yana tsaye sannan ya juyo “me zaki ce akawo miki kici ki sha magani ? babu abinda zanci ta fad’a a fusace tana dubansa hawaye na tsiyayowa akan quncinta “daman Kin saba kwana da yunwa idan shi kike ra’ayi fine ,I don’t care ya nufi kofar fita daga d’akin ya barta cikin tsananin damuwa da sake shiga tashin hankali .”
Yana fita number minister ya fara nema kira uku yayi kafin a d’auka ,hajiya zainab ce ta dauka cikin sanyayyiyar murya tace” hello yana jin sautin muryar ya fahimci mahaifiyar tanweer ce dan bazai manta da muryar ba da irin kuka da kururuwan da tayi a daren da zai taho da tanweer muryarsa a dikile ya soma magana cikin Isa ” Ina minister ?ta waiga a sukune ta Kalli Inda minister yake zaune aqasan tayis yayi tagumi da hannunsa d’aya cikin tsananin tashin hankali “wake magana ?ta tmby cike da faduwar gaba “babu buqatar sanin haka sai dai dalilin Kiran shine ki fad’awa mijinki idan yana kusa ” cewar ya dakatar da kawalayen daya tura haushi gari dan nemammamu wato jami’an tsaro idan ba haka ba zai zama sanadin rasa rayuwar diyarsa tanweer “.
nan take jikin hjy zainab ya kama rawa hawayen dake makale a kwarnin idanunta suka sauka akan quncinta , a hankali ta soma karanta hasbinallahu wa ni’imal wakil tana cigaba da sauraransa “ki fad’a masa ya janye if not you’ll lose your daughter ko Kuma musa ayi reping dinta mu yada a social media yana gama fad’ar haka yayi disconnecting din kira yana fesar da iska.
wani kuka hjy zainab ta fashe dashi ta zube kasa tana furta kalmar ” inna lillahi wa inna ilaihi rajiun da sauri minister ya matso kusa daita dan tunda ta d’auki wayar tana kallonsa shima ya tattara hankalinsa da natsuwarsa gurinta a rud’e yake tambayarta “menene zainab me akace miki a wayar da’aka kira ?” dan girman Allah ka kira office din commissioner yanzu yanzu ka sheida masa a tsaida jami’an tsaron nan bana son na rasa tanweer ,bana son wani mummunar abu ya faru daita iya abinda ta fad’a kenan ta zube jikinsa tana sake fashewa da wani sabon kuka numfashinta na sama da kasa. kamota yayi ya rungumeta yana shafa bayanta”is okay zainab babu abinda zai samu tanweer dinmu da izinin allah lafiya zata dawo garemu . yayinda ita Kuwa hjy zainab babu abinda take cewa sai “ka kira commissioner .”
Can bangaren jami’n tsaro kuwa suna Isa 1829 plaza dake gaban isalo a matukar harzuke suka firfito suka shiga ciki kmr d’azu wasu suka tsaya a waje Wanda suka shiga suka fara tambayar manager gurin, Kai tsaye aka nuna musu Inda yake nan da nan suka fara aika masa tambayoyi akan mutane da suka shigo plaza din a wanni da suka gabata “ai mutane dayawa sun shigo a yau din nan yalla’bai “ko zaka iya gane fuskokin wanda da suka shigo ya fad’a tare da nuna masa hoton jaguwa ?” gsky bazan iya ba amman tunda ga hoto bari mu qunna cctv camera mu duba ” take yayi rewarning cctv suka tsurawa tv din dake gurin kusa guda biyar idanunsu , idanun manager ne ya Kai kan motar jaguwa “yalla’bai ga wata mota nan ta tsaya a haraban plaza a awa biyu data gabata nan dukkaninsu suka bada attention dinsu suna duban motar suna sauraronsa ” mutun d’aya ne ya fito daga cikin motar fuskarsa rufe da face mask nima Kuma a wannan lokacin na fita Kuma tabbas naga wannan motar mai number 2548 bayan ya shigo nima na dawo Ina kallonsa yana daukar dogayen riguna na mata haka kawai naji hankalina bai kwanta dashi ba idanuna na kanshi har sanda ya biya kudin kayan ya wuce duk yadda akayi wannan mutumin ne duk da fuskarsa bata bayyana ba kamar yadda hotonsa yake suna tsaka da sauraronsa kiran commissioner ya shigo wayar dcp, ya d’auka cikin sauri yana cewa “hello sir “kuyi maza ku dawo akwai matsala “matsala Kuma sir ?
“Eh babba kuwa domin rayuwar yarinyar na cikin hatsari idan aka cigaba da bibiyarsu ga dukkanin alamun akwai wanda yake yiwa hukuma zagon kasa”. aikuwa yayi babban kuskure ya cuci alluma har ma da zaqaqarun yansanda masu k’okarin ganin an kawar da ta’addanci a kasa inji cewar dcp batare da bata lokaci ba dcp ya juya yana bawa yaransa umarni .”Tafiya kawai dcp yake baya ko gamin gabansa saboda takaici da bakinciki wai sai yaushe ne zasu yi nasara akan jaguwa ?sai yaushe zasu yi nasara akan shi Kawar dashi daga doron duniya da wannan tunani ya Isa gidansa.