KUSKUREN BAYA 1 TO 48

naunayen ajiyar zuciya ta sauke idanunta na sake cikowa da ruwan hawaye ta sake biyo bayansa tana furta”wayyohhhly Allah na shiga uku nah Allah ka taimakeni kar ya harbeni da bindigarsa yau “. bai tsaya akoina ba sai a lambun gidansa ya k’arasa Inda suke ajiye kayan shaye shayensu ta’ba sigari ya d’auka ya Kai bakinsa ya kunna ya fara zuka da karfi, yana tsaye yana zukar taba ta karaso jiki a sanyaye ta had’e hannunwata duka cikin juna , yaji alamun tsayuwarta amman still yaki juyowa zuciyarsa ban da bugawa babu abinda take .
Cikin tsananin tsoro da fargaba ta Kai hannunta kan kafad’arsa tana fixgo numfashi da kyar ta janyosa amman kamar dutse ta ta’ba dan ko gezau bai motsa ba ya cigaba da zukar tabarsa . hannuwanta duka tasa ta riko damtsen hannunsa zuwa jikinta ya fixge ya yar da sauran tabar hannunsa yayi taku d’aya zuwa uku ya tsaya ya rike kugunsa da duka hannuwansa yana furzar da iska shi kad’ai yasan irin halin tashin hankali da yake ciki “shi zata mara?” wannan shine karonta na biyu data kai hannunta fuskarsa tsaki yaja yana kokarin juyowa hannunsa na hagu tayi saurin matsoshi zata taresa ya kauce yana ƙoƙarin bin dama nan ma ta taresa a karshe yayi wani irin juyi ya sha gabanta ya soma tafiya cike da zuciya .
ta biyosa da sauri tana Kuka ,yadda yake sauri haka itama take d’aga ka’fafunta tana sheshekan kuka, dan zuwa wannan lokacin ta fara hango irin halin balai da zata tsinci kanta agurinsa muddin bata sauko dashi ba ,ta Kai hannunta ta ta’bashi tana Kiran sunansa “ad……. ” wani irin juyowa yayi tare da buga mata razananniyar tsawar data sata kamewa guri d’aya had’e da dafe qirjinta yayinda jikinta ke wani irin rawa, ta kasa kallonsa tsabar tsoran da firgicin data hango kwance acikin kwayar idanunshi ta sunkuyar da kanta kasa tana sheshekar kuka cike da tsananin tashin hankali .
“tayi data sani wannan marin da tai masa Ina ma adawo da abinda ya faru baya a seconin daya wuce wallahi da bata aikata hakan ba .
ya kafeta da tsumammun idanunshi kusan minti biyu idanunshi na yawo ajikinta yana hukuntata da idanunshi ganin bashi da niyyar cewa komai Kuma ta fahimci ko zasu kwana a haka bazai ce mata qala ba yasa tayi karfin halin matso da ka’fafunta, tayi taku biyu ta rungumesa ajikinta very tight tana wani irin kuka “kayi hakuri Adnan! kayi hakuri dan Allah”. k’okarin fixgeta ajikinsa yake ta kamkameshi gam tana wani irin kuka me ta’ba zuciya “dan Allah Adnan kayi hakuri, Ina me baka hakuri karkayi fushi dani “. ta k’arasa fad’ar haka tare da durkushewa a gabansa tana kallonsa hawaye na gangarowa akan quncinta “kayi hakuri karkayi fushi dani nasan nayi kuskure ta k’arasa maganar tana girgiza masa Kai alamun bazata sake ba ,” bansan me yasa na aikata maka hakan ba amman kayi hakuri bana cikin haiyacina ne kaji Adnan . wani irin wahalalle numfashi ya fesar yana jin wani sanyi na ratsa sansar jikinsa ko babu komai tasan tayi masa ba daidai ba tunda gashi duk ta rud’e ta fita haiyacinta tana kuka tana bashi hakuri ,gashi daman shi abinda ke saurin karyar masa da zuciya kenan kukan mace ,bare km nata wanda ya rasa dalilin da yasa baya qaunar jin sautinsu yana mugun d’aga masa hankali .
ya ciza lip’s dinsa na kasa da karfi yana dubanta, Ido cikin Ido suke kallon cikin kwayar idanun juna “dan Allah kayi magana kace ka yafe min bazan sake ba .” lumshe mata tsumammun idanunshi yayi yana sauke naunayen ajiyar zuciya Jiki a sanyaye ta mike ta kamo hannuwansa duka cikin nata suna fuskantar juna “.
a hankali ta kai hancinta daidai saitin nashi suna shakar numfashin juna a tare suka lumshe idanu zuciyoyinsu na sake amsar soyayyar junansu “am so sorry Adnan ” bai ce mata uffan ba dan haka ta cigaba da kuka sosai kamar ranta zai fita amman still jaguwa yaki magana.
fuskashi ta kamo ta rike da duka hannuwanta ta had’e fuskokinsu guri d’aya tana hawaye cikin kuka tace “,nayi nadama na rantse maka bazan sake ba kayi hakuri bansan qaddarar data kaini marinka ba “qaddara tanweer ? ya furta hakan numfashinsa na shigar mata hanci tayi saurin runtse idanunta, numfashi ya sauke da karfi , “qaddara ce tasa kika sauke yatsunki biyar a fuskata ?”tayi saurin gyada masa Kai tana marairaicewa ” “wannan shine Karo na biyu da hannunki ya sauka akan fuskata why tanweer?yayi maganar zuciyarsa na rawa . kife fuskarta tayi a tsakiyar qirjinsa ta saki wani sabon kuka me tsuma zuciya” an dokeni a makaranta sojaji a lokacin baya bisa gaskiyata adalilin na d’auki matakin abinda akayiwa kanwata bayan wannan ban sake shan duka a hannun kowa ba sai ke yarinya karama dake” ya k’arasa maganar yana fesar da numfashi had’e da kawar da fuskarsa gefe baya jin zai yafe mata wannan marin cikin sauki .
rungumesa tsam ta sake yi ajikinta tayi masa riko me karfi tare da lumshe idanunta .
wani irin yanayi me yuwar misaltuwa ya tsinci Kansa ciki ya dinga sauke ajiyar zuciya akai akai , lufewa tayi sosai ajikinsa tana sheshekar kuka “,kayi hakuri dan Allah ” sosai ta rungumesa shima abinda yake son yi kenan ya rungumeta sai dai bazai iya ba dan bacin rai bazai barshi ya aikata hakan ba ,har sanda anas ya k’araso ya tsaya akansu rungume da hannuwansa duka a qirji basu sani ba .”
murmushi yayi tare da yin gyaran murya “jaguwa Ina matukar farinciki yau ” anas ya fada , jaguwa ya bud’e idanunshi da sauri sakamakon jin sautin anas cikin sauri tanweer ta sake shi tare da sunkuyar da kanta kasa cikin tsananin Jin kunya .
had’e rai jaguwa yayi tamkar bai ta’ba dariya ba arayuwarsa “me ye ka wani had’e rai kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa? ai tun d’azu nake biye daku, ka barni cikin damuwa kai Kuma kana nan kana ta Shan shagalin ko?” gaskiya hakan yayi matukar burgeni da sauri tanweer ta juya cike da matsanacin kunya ta bar gurin.”
jaguwa ya juya zai bar gurin anas ya riko hannunsa “haba kai kuwa abokina Ina zaka Kuma ?wani mugun kallo yayi masa sannan ya yatsina face dinsa yace “zanje nayi wani aiki ne ya fad’a yana kokarin fixge hanunsa ya sake rikosa “ni zaka rai…..”
“enough anas banason abinda kake min maganarka na bata min rai wallahi, idan baka daina ba zamu samu matsala “to mu samu mana in dai akan wannan ne wallahi na yarda mu samu taya ga gaskiya Ina gani amman kake waskewa ,lokacin da aka rasa yarinyar nan dawowa kayi tamkar wani zautacce mahaukaci ,hankalinka ya tashi ,bama ni ba kowa a gidan nan yasan son yarinyar nan kake wata muguwar shaka ya yayiwa anas a fusace yace “don’t ever say it again ko me ya tuna yayi saurin sakin wuyan anas yana duban hannunsa daya damki wuyansa dashi kamar zaiyi kuka .
wani irin kallo anas yake masa cikin rashin tsoro da fargaba ya cigaba da magana idan da sabo ya saba da halinsa “wallahi ka natsu da kyau ka saurari zuciyarka wani bakon alamari na shirin faruwa da kai Adnan idan ka kasa fahimta yanzu nan gaba zaka gane son yarinyar nan kake “wallahi bana son…”
“Wallahi kana son yarinyar nan anas ya katse shi ta hanyar fad’ar haka “ya Isa banson ji komai daga bakinka Kuma ka daina min maganar , sannan ka daina damun kanka akan Ina Sonta dan babu komai acikin nan ya fad’a yana nuna masa saitin zuciyarsa “adnan!”
“Allah ka yarda ka fad’a son tanweer ya sake fad’a tare da Kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa dake faman bugawa da karfi, bafa yau na sanka ba ka yarda ko karka yarda wannan zuciyar ta kamo da matsanacin qaunar tanweer jaguwa yaja dogon tsaki kana ya juya yana tafiya anas na biye dashi atare suka shiga falon ya fad’a cikin d’aya daga cikin kujerun falon yana sakin numfashi”ad…!
“Na had’aka da daraja Allah ka barni haka ni wannan yarinyar ma wallahi sai naci ubanta kafin ta bar gidan zata San ta mareni “ka …”shiiiiii bafa na son Jin komai daga bakinka kaje kawai “tsaye anas yayi yana kallonsa ga gaskiya a zahiri amman yaki yarda, jaguwa ya runtse idanunshi yana jin wani irin abu na taso masa akan yarinyar yana tokare masa kahon zuciyarsa …”
Ya dade zaune har kusan karfe biyu na dare kafin daga bisani bacci ya d’aukesa sai goshin asuba ya tashi ya koma d’akinsa Bai koma bacci ba ya shige bayi yayi wanka ya dauro alwala ya fito ya Isa Inda daddumar sallarsa yake shimfide ya tadda sallah ,sai da yayi sallah asuba ya koma bacci ya dade yana bacci kasancewar weekend ce .”