KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Wani gigitacen mari ya wanka mata yana huci ta dafe kuncinta daidai Inda hannunsa ya sauka tana dubansa Ido fal da hawaye “akan na fad’a maka gaskiya shine ka mareni ?” to karya ne baka sata ,baka bin mata , baka…”a tsawace yace ” Kada ki sake fad’a min maganar banza idan kika sake fad’a min maganar banza wallahi zanyi miki abinda har ki mutu ba zaki manta dani ba ko ubanki bai Isa ya Kalli idona ya fad’a min maganar da kika fad’a min ba bareki” .
tayi shiru tana kallonsa ta kasa cewa komai kafin daga bisani tayi kasa da muryarta “,Allah ka saka min ” ya sake d’aga hannu zai sauke mata wani marin tayi saurin kaucewa ta dube shi Ido cikin Ido “da gatana da komai amman ka d’aukoni ka rabani da gatana ka maidani jaka to wallahi na barka da Allah duk abinda ka min ka jira sakamako ” tana gama fad’ar haka ta juya zata bar d’akin ya biyota ya shakota “,Ina zaki ki dawo ki gama tsine min “,ni ka sakar min wuya ,bazan saka ba muddin kina son zaman Lafiyarki a gidan nan ki iya bakinki akan abubuwana dan wannan halin naki yana d’aya daga cikin abinda yasa na tsaneki yanzu sam baki da kunya “.
“naji kaima ka daina abinda zai sa na dinga maka rashin kunya , da kyar ta sanya gbdy karfinta ta kwaci kanta tana haki fixgota yayi ya maka akan gado yana mata wani irin kallo mai firgitarwa bayan second biyu ya sawa kofar key ya d’auki towel din data fito dashi ya wuce ya shiga bayi yana jan tsaki .
tanweer ta dafe kanta tana jijigawa “na shiga uku ni tanweer wani irin iftilai ne haka ya fad’a min ? yawon zagin ubana da yake yana mugun bata min rai kusan yafi duk wani wulakanci da yake mata ,da kyar ta rarrashi kanta ta kwanta tana tunani adadin kwanakinta a gidan a lisafinta ta share wata biyu kenan zata shiga na uku a hannunsa tana kwance lamo
ya fito kungunsa d’aure da towel yana goge jikinsa da alamun wanka yayi gajeren wondo ya d’auka ya saka ya kwanta kusa daita tana ganin haka tayi saurin ta matsawa daga kusa dashi dan har lokacin warin wiwi bai bar jikinsa ba .”
ganin abinda tayi yasa haushi ya kamashi cikin fushi ya fixgota jikinsa da karfi ta sake janyewa
ya sake rikota sosai “ke kin isa na kwanta kusa dake ki tashi ? “dame kike takama dashi ? ta bud’e idanunta sosai “bana takama da komai Amman gaskiya ka daina taba min jiki dan ni ba matarka bace sannan ba karuwa bace da zaka dinga had’a jikinka da nawa bazan iya irin wannan rayuwar ba, kawai ka kyaleni idan bazaka maidani gidanmu ba zan hakura na zauna amman bazan iya wannan shirmen da haukan ba wallahi idan baka farga ka tuba ba ka jira mako..” “ya Isa ! ya isheki haka jaguwa ya fad’a a fusace “ke ni zaki gayawa maganar banza akan abinda isana ya bani dama ba”.tayi saurin tashi daga jikinsa ta zauna tana dubansa tace “ban fahimceka ba ? menene Isan naka ya baka ba ? Yayi mata kallon banza kana yace “ke mana ni gani nake kin zama mallakina duk da bana sonki kuma dole nayi abinda na gada dama dake “.ranta ya dugunzuma a fusace tace “wallahi karya ne , wiwin da kasha ya fada maka karya baka Isa kayi abinda kaga dama dani ba, Kuma daga yau ka daina taba koina a jikina har sanda zan bar gidan nan tunda bana Uba.. …”
Ji tayi ya zabga mata mari a fusace tare da durowa daga kan gadon Yana dubanta” Ina gargadinki da ki iya bakinki da furta min duk Kalmar da kika ga dama domin idan ba haka zan miki rashin mutunci dan ni ko kusa ban d’auki mace a komai ba illa abun bukatata ki sani Ina da halin da zan aje irinki guda hamsim idan naso dan ma Kinga na barki haka batare da na aikata wani abun asha dake ba shine zaki kawowa mutane salo ?
“to ni Ina ruwana idan kaga dama ka cika gidan nan makil da karuwai wannan matsalarka ce ni dai karka tabani “.
Ya Isa Inda ya ajiye wayoyinsa ya d’auki daya daga ciki ya duba lamba pretty ya kira ya sa a handsfree ringing biyu muryata ta fito tana cewa “Allah ya taimaki jaguwa uban gidana , jaguwa yace “pretty kina Ina ? Ta lankwashe murya kmr tana gabansa tace “Ina gidansu ogechi yanxu muka shigo gida “kuzo ku duka bai gama maganar ba tanweer ta k’araso ta fixge waya hankalinta a matukar tashe da abinda ke Shirin faruwa, a gabanta zai kira karuwarsa wannan wacce irin rayuwa ce ? “Wacce irin rayuwa ya saka kanshi “ita da wasa tace ya cika gidan da karuwai shine zai kirasu wayyo Allah na shiga uku ” akansa an kirata da Kalmar karuwa ,yanzu km zai gayyato karuwai zuwa gidan “to me zai hana ka maidani ka samu damar yin iskancinka da tushe tunda shine a gabanka ? tayi maganar a matukar tsorace dan tunda ya fara da maruka tasan duka ma bazai masa wuya ba.
ta juya cikin sauri ta bar d’akin zuwa bayi tare da fashewa da kuka “a she zata tsinci kanta cikin makauniyar soyayya irin haka , hakika so bai mata adalci ba daya rasa Inda zai Kai soyayyarta sai gurin mutumin da bai san darajan mace ba bata San tsawon lokacin data dauka ba a zaune a toilet tana ayyana abubuwa da dama akan rayuwarta ” bazata taba yarda tsoransa yayi tasiri a zuciyarta ba muddin soyayyar da take masa ta gaskiya ce ya dace tayi komai dan ta rabashi da irin rayuwar da yake, zata rabashi da kowacce karuwa acikin rayuwarsa ta yunkura da kyar ta mike ta fito haniya ta dinga Jiyo sama sama aranta tace “sun zo kenan ? ta fito ta nufo babban falon gidan Inda tafi tunanin suke ta iske mata zaune kusan tsirara domin kowaccesu daga ita sai pant da bra shi Kuma jaguwa yana nan sanye da gajeren wando ajikinsa , hayakin taba kawai ke tashi da kwalayen taba burjiki akan tebul din gabansu Sam basu lura da fitowarta ba har sai data karaso har gabansu ta kira sunansa da fusatacciyar murya “Adnan !” duk sukayi hanzarin suka tsaya cak suka bude idanunsu suna dubanta Shima din idanunshi ya zuba mata cikin mamaki da fushi yace “me ya fito dake ?
“Ko nace ki fito ne “a fusace tace ban sani ba wato kana tunanin zaka kawo karuwai cikin gidan nan alhalin Ina cikinsa in amince wallahi tallahi baka Isa ba , bazai yiwu ba sai dai kayi daya cikin biyu ka mayardani gidanmu ko ka bani damar na fita a gidan nan na kama gabana amman muddin Ina cikin gidan nan an daina alfasha da kawo yan iska kana badala dasu sai dai kaje waje kayi iskancinka ta k’arasa maganar tana fashewa da kuka “,wallahi bazan yarda ba ya zama dole su bar gidan nan kuma a yanzu …”