KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“anas! Jaguwa ya kira sunansa gbdy yarinyar nan bata da manners “gaban anas ya fadi sakamakon ganin tanweer a tsaye a bayan jaguwa rungume da hannuwanta anas ya Kai hannunsa zai nuna masa bayansa jaguwa ya buge masa hannun “Kaine ka kawo maganar dan haka ka bari na gama kafin ka shigo da wata “sam sam yarinyar bata da tarbiya iyayenta basu koyar daita yadda ake girmama babba ba da kace mata cas zatace maka kul , ko da yake taya zatayi tarbiya haihuwa tayis reinon tayis tashin turai kasan baza’a sameta da cikakkiyar tarbiya amman Misali ace da gaske zan yi soyayya da wata mace da itace farko kodan disvarging dinta da nayi amman bazanyi ba yana gama fad’ar haka ya juya da niyyar barin gurin turus yayi zuciyarsa na karkarwa sakamakon idanunsu da suka tsarke cikin juna.”
Mmn sudais????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
????️20
…..juyowa yayi ya Kalli anas dake tsaye a bayansa yana tmbyrsa da kwayar Idanunshi dake cike da matsanacin firgici ko taji abinda ya fad’a , shima da kwayar Idanunshi ya bashi amsa alamun taji komai daya fad’a a yanzu .” ya subhanallah ya furta a kasan makoshinsa yana mai sake juyowa Inda take tsaye , tana nan tsaye kmr wacce aka dasata agurin sai dai zuwa wannan lokacin babu komai acikin kwayar idanunta sai tsananin firgici dake tattare da tashin hankali .
Muryarta na rawa tace “me naji ka furtawa abokinka yanzu ? “mafarki nake
ko kuwa karya ne ? “
taku d’aya ta K’ara tana sake cewa “kace karya kunnuwana suka jiyo min ba gaskiya ba ?” shiru yayi yana kallonta zuciyarsa na wani irin rawa dan gbdy ya gama rikicewa bai so taji abinda ya shiga tsakaninsu ba “ka fad’a min gaskiya Adnan da gaske kayi disvarging dina ? ta fad’a tana wani irin sheshekar kuka kmr ranta zai bar gangar jikinta “idan gaske ne kayi disvarging dina a yaushe kenan kayi da ni ban san da zaman hakan ba ?” still shiru yayi qirjinsa na cigaba da bugawa da karfin gaske , sai dai wannan karon yayi k’okarin Kai hannunsa jikinta domin kamota , tayi saurin buge masa hannu “dan Allah ka fad’a min cewar karya ne ba gaskiya bane dan zuciyata bazata iya d’aukar wannan sabon tashin hankalin ba ?”.
ta k’arasa maganar tana cakumar wuyar rigarsa da hannuwanta duka ta matse masa wuya gam da iyakacin karfinta tana fidda zazzafan numfashi .”
anas na ganin haka ya lalla’ba sun sun ya gudu ya barsu su karata , dan bai san ta yadda zai shawo kan matsalar ba , shi da yayi silar amsar budurcinta sai yasan duk yadda zai yi ya shawo kanta .” Ka fad’a min cewar karya ne Adnan bakayi komai dani ba? dan Allah karka ce min kayi disvarging dina….” wannan kalmar kawai
take fad’a tana sake maimaitawa . rungumeta yayi tsam ajikinsa yana sakin numfashi babu shiri ta sakar masa wuya saboda ba karamin runguma yayi mata ba , ya Kai bakinsa daidai saitin kunnenta ya soma rad’a mata mgn cikin sanyayyiyar muryarshi me kashe gabobin jiki “da gaske ne tanweer amman kece silar Komai daya faru ,kece da kanki kika kawo min kanki batare da nayi niyyar aikata hakan ba”.
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta furta cikin tsanani tashin hankali, zamewa tayi ajikinsa ta kwalla wata razananniyar qara mai sauti da tasa gbdy gidan ya amsa tana ihu ta zube kasa warwas tana kuka da birgima da sauri ya durkusa gabanta ya rikota gam jikinsa na rawa tamkar mazari yace “wallahi ba da son raina nayi ba kece kika bukaci hakan “.
“ni ….!
Ta furta a tsawace tana watsa masa wani mugun kallo ,ya gyada mata Kai alamun “eh !
“na shiga uku na lalace ni surayya Adnan ka cuceni taya zaka min haka? “taya ma zan kawo maka kaina wallahi ban san na aikata hakan ba karya kake min wallahi bazan ta’ba aikata hakan ba saboda Ina qaunar budurcina fiyye da komai dake cikin duniyar nan” .
kuka tanweer take sosai kamar ranta zai fita ya bar gangar jikinta ta mike tsaye ta soma tafiya cikin tsananin tashin hankali tsabar gigicewa hanyar special room dinsa ta nufa har tayi taku uku ya biyota da hanzari ya fixgota da karfi ya sake mannata a faffadan qirjinsa “am really sorry for…..” ai bata bari ya karasa ba ta shiga dukan qirjinsa da iyakacin karfinta tana tsine masa tana mai sake fashewa da wani kuka . kamkameta yayi sosai ajikinsa duk ya rud’e ya gigice sai zufa yake fitarwa “ka sakar min jiki bana son kusancinmu tare , tsanarsa take son yi irin tsanar da bata ta’ba wani halitta ba amman tsanar taki sauka acikin zuciyarta .”
Muryarta cike da kuka tace “a tunanina na tsira daga kaidinka a she ban tsira ba ,” me yasa kamin haka Adnan ? wallahi nasan bana haiyacina bancin haka babu abinda zai sa na baka kaina , Kuma ko duk duniya zasu taru akaina bazan taba yarda da nice na kawo maka kaina ba sai dai idan wani abu ka bani na sha har kayi nasarar akaina “.
shiru yayi kawai yana sauraronta yana tunanin yadda zai ku’butar da kanshi agurinta take ya tuna da cctv na bangarensa dan haka yay gauggawar zareta ajikinsa ya riko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita nan fa ta turje tana cewa “babu Inda zani ka rabu dani wata hadaddiyar tsawa ya buga mata yana cewa “muje !
iya abinda bakinsa ya iya fad’a kenan ya cigaba da tafiya bai tsaya akoina ba sai a d’akinsa ya zaunar daita tana wani irin kuka me ta’ba zuciya .”