KUSKUREN BAYA 1 TO 48

camerar part dinsa ya kunna yayi rewarning d’aga Inda ta shigo masa ya juyo da tv Inda take “ki bud’e idanunki da kyau ki Kalli komai daya faru “shiru tayi tare da tsaida kukanta shi kuma ya koma jikin bangon d’akin ya tsaya rungume da hannunwansa duka a saman faffadan qirjinsa sai dai gbdy hankalinsa da Idanunsa sun tattara ne akanta .
a hankali ta fara ganin komai tun daga shigowarta d’akin da yadda ta kunna wutar d’akin ta Isa Inda yake kwance tana shafa jijiyarsa har zuwa sanda ta d’auki bindigarsa da yadda ya amince mata ya kusanceta suman zaune tayi agurin , lokacin data ga yadda ya dinga sarrafa dukiyar fulaninta da yadda ya dinga tumurmusanta bata san sanda ta zamo kasa a gigice ba tana furta kalmar “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ” me ya sameni haka ?”me ya shiga cikin tunanina ?”wallahi ban san na aikata haka ba, bansan abinda ya sameni ba “inna lillahi na shiga uku shikenan na rasa budurcina ?” wayyo Allah ni surayya ka kuwa san maseefar da ka jefani aciki ? me yasa kayi sex dani ? “yanzu me kake son nacewa mijin da zan aura ?hawayen ya zubo mata sharr … akan quncinta take Kuma jikinta ya kama rawa “gbdy zuciyarta ta sake karyewa “me yasa baka dawo dani haiyaci ba a lokacin ?”wallahi bansan na aikata hakan ba Shima jikinsa rawa yake tausayinta ya kamashi gbdy ya manta wancan tashin hankali da dcp ya jefashi ciki ya matsota sosai yana me jimamin da nadamar abinda ya faru.”
kusancin dake tsakaninsu yasa ta jiyo yadda qirjinsa ke bugawa da karfin gaske “dan Allah kiyi hakuri nasan bakya cikin haiyacinki lokacin da abun ya faru nayi k’okarin kar hakan ya faru a tsakaninmu amman saboda bakya cikin hayacinki burinki na kusanceki alokacin shiyasa nayi .
“me Ka bani wanda ya gusar min da hankalina ? girgiza mata Kai yayi alamun “Babu ” Karya ne ka bani wani mugun abu idan ba haka banga dalilin da zai sa na kawo maka kaina ba kayi yadda kaga dama ba ta k’arasa maganar tare da fixgo numfashi da karfi ta fesar kmr me cutar asthma tayi shiru hawaye na xubo mata “kenan shiyasa a wacan ranar yayita matsa mata lallai sai tayi wankan tsarki ? ashe yasan mugun Abu da yayi mata ta zabura zata mike ya rikota gam ya makaleta ajikinsa yana shafa kanta zuwa bayanta yana jin kmr ya mutu , yana son ya fad’a mata cewar asiri akayi mata a waccen ranar yasa komai ya faru yana jin tsoron wani sabon tashin hankalin da za’a yi idan tasan da hakan.
“kiyi hakuri da abinda nayi miki nayi k’okarin gujewa hakan nasan illar abinda nayi miki tunda an ta’ba yiwa yar’uwarta
a lokacin ji nayi kamar na mutu duk yadda mutane ke bani hakuri akan nayi hakuri kasawa nayi har sai dana d’auki fansa da hannuna sannan ruhina ya samu salama ” iya radadi naji a wannan lokacin ,qunar abinda na miki ya tsaya min a zuciya kullum dashi nake kwana nake tashi na zubar da hawaye sosai naji kamar na kashe kaina a ranar ,ki ya femin tanweer domin kece mace ta farko dana amshi budurcinta , bana sonki amman budurcinki shine abinda yafi komai tsaya min arai har na mutu bazan manta cewar ni ne mutumin dana amshi budurcin tanweer ba, kuma bazan daina ganin kima da martabarki ba .”
“Zaka cigaba da ganin kima da martabata ? ya gyada mata kanshi “amman kace bani da tarbiya ? shiru yayi kawai dan rasa abinda zai fada mata “haka kayita maimaitawa abokinka cewar ni mara tarbiya ce kuma nasan shima zai tsaya maka arai baza ka ta’ba ganina da wannan darajar ba ? ” no karki ce haka ,kiyi hakuri da furucina na d’azu am really sorry bazan sake ba ya rike kunnuwansa da hannunwansa , “babu ruwana da nadamarka ka biyani budurcina kawai dan wallahi bazan yarda ya tafi a banza ba”.
shiru yayi yana kallonta maganarta tayi matukar bashi dariya amman ya hadiye ,
yarinyata ne zalla atattare daita bancin haka taya zai biyata budurcinta daya amsa ?
Numfashi ya fesar kafin a hankali ya mike ya Isa gaban wani katon akwatin me ratsin baki da ja ya janyo akwatin zuwa gabanta ya bud’e dalolin kudin american ne cike dashi “bani da abinda zan biyaki dashi sai dai ….. “dakata ai kasan ni ba bakuwarsu bace dan zan iya baka ninkinsu abinda nafi bukata ka dawo min da budurcina na koma yadda nake Kuma a yanzu “.
tsura mata tsumammun idanunshi yayi kawai yana kallon karamin bakinta ,ya furzar da numfashi wanda hucinsa ya doki fuskarta ,a natse ya d’auke idanunshi akanta zuciyarsa na tafarfasa “yau tazo masa da abubuwa a cukurkud’e “Ina dcp ya samu numbersa da har ya kirasa yana masa barazana ? sannan da wannan tashin hankalin da furucin bakinsa yayi nasarar jefashi ciki ,taku biyu yayi ya tsaya jikin window d’akin tare da juya mata baya ,bayansa tabi da kallo batare tace uffan ba illa sheshekar kukan da take zuciyarta na hasko mata yadda ya dinga juyata .
A natse ta soma jiyo sautin muryarsa na shiga kunnuwanta “ki shirya gobe zan mayar dake gidanku nasan zakiyi farinciki da jin hakan sannan dashi kawai zan iya biyanki budurcinki dana amsa ya k’arasa maganar tare da juyo ya kafeta da Idanunshi yana ciza lip’s dinsa na kasa da karfi “.
Wani sanyayyayen farinciki ne ya lullu’beta alokacin d’aya , duk cikin kalamansa babu wanda yayi mata dadi ya sanyaya zuciyarta kamar wannan “zani gida kace ?ta fad’a tana tsareshi da idanunta ya gyada mata Kai alamun “eh! gbdy taji raunin da yayiwa zuciyarta ya Kau hawaye ya gangaro mata amman wannan lokacin na farinciki ne, sosai take kuka wanda ya rasa dalili a tunaninsa murna da farinciki har ma da tsalle zatayi na barin gidan .
ta tsugunna kasa ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta hawaye na cigaba da gangaro mata ya rasa ya zai yi daita abubuwa dayawa suka zo masa kukanta da rabuwar da zai yi daita rarrafowa yayi ya dawo gabanta ya kafeta da tsumammun idanunshi masu kashe mata jiki tun ba’aje koina ba ya soma Jin babu dadi a ransa ,ya bud’e baki da niyyar yin magana kenan kira ya shigo wayarsa ya janye jikinsa ya mike ya karasa Inda wayoyinsa suke ya d’auki wacce ke ruri ya duba sunan amminsa ne ke yawo a screen din wayar dan haka da hanzari ya danna Koren madanni tare da manna wayar a kunnensa ya soma tafiya yana Kiran sunanta “ammi!
bata daga Kai ta kallesa ba har ya bar d’akin kusan minti biyar da barinsa d’akin ta d’ago kanta ta bin hawayen dake zuba akan tafukan hannunta da Kallo.
a hankali ta soma share hawayenta zuciyarta na tsinkewa , ta tsaya shiru tana kallon d’akin har zuwa kan bed dinsa da komai ya faru sosai take tunani matsayar rayuwarta , kwakwaluwarta ta shiga tunani “shikenan ya amshi budurcinta zai barta ? ” bana sonki amman budurcinki shine abinda yafi komai tsaya min arai har na mutu bazan manta da ni ne na amshi budurcin tanweer ba” kwakwaluwarta ta dawo mata da maganarsa “Adnan ka cuceni amman Kuma ka sake mamaye zuciyata da komai nawa , ka sake samun gurbi acikin zuciyata ,ka amshi abu me daraja da tsadarsa ya wuce komai acikin fad’in duniyar nan to me yasa har yanzu zuciyarka ta kasa amsar soyayyata ?why! why !! adnan kwalkwaluwarta ta toshe kanta ya cunkushe duk abinda ya fad’a rashin sonta daya furta shi yafi komai d’aga mata hankali “nima bazan manta da Kai ba har karshen numfashina ,Kuma har yanzu ban ji na tsaneka Ina tsananin sonka adnan nasan Allah yana da kyakkyawan nufi akan ni da Kai yasa ya had’amu , yadda nake sonka haka zalika Kai ma kana Sona duk da cewar kana boyewa , amman soyayyata ta gama fallasa kanta ajikinka tunda har abokanka suka san dashi , zan tafi na barka da dunbin qaunata daskare a zuciyarka , ba zaka gane hakan ba sai bayan bama tare idan Kuma hasashena dana abokanka bai zamo gaskiya ba ” ya Allah ka jarabi adnan da mutuwar sona , yaji idan bai dora idanunshi akaina ba bazai iya rayuwa ba ,
ya kasa samun natsuwa ,ya kasa hutawa ,ya kasa tsaye ya kasa zaune har sai ya tunkareni da batu na soyayya , Allah kasa na zamo silar shiryuwarsa ya dawo mutumin kirki ….” ta k’arasa maganar tana mai runtse idanunta tare da jingina bayanta da abun gado tana sake zurfafa tunaninta tun daga farkon haduwarta dashi har zuwa wattanin da tayi a hannunsa ta fahimci abubuwa da dama akansa illarsa dai shan wiwi da sanar satar da yake bancin hk bashi da wata makusa ,yana qaunar ahlinsa da taimakon mutane gari yana kyautatawa duk wanda yake tare dashi gashi shi din me basera ne ta kowani bangare yana da matukar da basera akan komai .”