KUSKUREN BAYA 1 TO 48

DARLING’S????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
WRITING BY
BAGUDO& MIMI’S QUEEN
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
????️04
Ganin tabbas mutumin da idanunta suke kwad’ayin sake had’uwa dashi ne a gabanta, yasa ta mike tsaye tana fad’ad’a fuskarta da murmushin da ita kanta bata san dalili yinsa ba , ta tsaya a gefensa bata damu da yanayin yadda ya daure fuskarsa ba ta kamo hannunsa ɗaya cikin nata ta shiga murzawa ,a hankali ya ɗan waiga inda take tsaye yana sauke wani wahalallen numfashi tare da ƙoƙarin zare hannunsa cikin nata, tayi saurin matse hannunsa wanda d’uminsa ya soma ratsata ,kafin daga baya ta dawo gabansa ta tsaya suna fuskantar juna ,ta kamo dayan hannunsa ta rike tana kallonsa shima tsura mata kwayar idanuwanshi yayi fuskarsa a haɗe tamkar hadari yana kallon yadda sumar kanta ya hargitse, kasa yayo da idanunshi suka sauka akan pinky lips dinta kana ya lumshe idanunsa sannan ya zare hannuwansa ya juya zai bar d’akin zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfin gaske, tayi saurin shan gabansa tana murmushi har fararen hakoranta suka bayyana cikin siririyar muryarta mai daɗin sauraro da jan hankali tace “kana kallona like baka gane ni ba ko ?
ya furzar da iska yana kawar da kanshi gefe dan Kallonta nasa shi jin wani irin kasala gashi har lokacin sanye take da kayan bacci , ta kai hannuwanta duka
ta kamo fuskarsa zuwa gareta ta sanya kwayar idanunta cikin nashi tace “please don’t tell me baka gane ni ba nice wacce na kusan bigeka koma nace na ….
yadda ya kafeta da sexy eye’s d’insa ko kiftawa ba yayi yasa ta kasa k’arasa maganarta ,yanayin yadda take makale ajikinsa yasa zuciyarsa jin wani abu akanta, wani irin sanyi ya dinga ji a sansar jikinsa kamar ana masa wanka da ruwan sanyi , ta sake shige masa tana son ya tunata “idan ba zaka tuna ni ba ka fada min how did I end up here with you? How?!”. Nan ma shiru yayi mata ya kasa bata amsa ta d’aga idanunta sama alamun tunani can ta dawo dasu gareshi tace” ko ka sake taimaka min ne a karo na biyu ?” still shiru yayi mata zuciyarsa na harbawa da karfi “please help me dan Allah ka da’ukeni daga gun wadan nan robbers d’in ?”tsura mishi ido tayi cike da muryarta kamar zatai kuka ta bud’e k’ananun lips d’inta. “Please ka mun magana dan Allah”ta karasa maganar tana zura yatsun hannunta cikin kunnenshi , da sauri ya janyo wani dogon numfashi ya sauke har lokacin bai iya bata amsar tambayoyinta ba saboda bashi da abinda zai ce mata ,idanunshi ya ɗan lumshe tare da matsawa daga jikinta da yake jin kamar ana tsira masa allura kasancewarsa matashi kuma mai karfin sha’awa , sai dai duk da wannan karfin sha’awar nashi ba kowani duri yake iya ci ba ,ita kanta abinda yake cin zuciyarsa kenan ya azabtar daita da baiwar da Allah yayi masa sai dai a daren jiya yaji bazai iya aiwatar da nufinshi akanta ba tausayin mahaifiyarta ne ya d’arsu a zuciyarsa yadda yaga hankalinta ya tashi a lokacin da zai bar gidan daita ,bugu da kari shi kansa yasan illar abinda zuciyarsa taso aikata daita.
a hankali yaja tsaki tare da sake dubanta sannan ya had’iye wani wahalallen yawu gata dai da gani yarinya ce da bazata wuce shekara sha tara a duniya ba amman komai yaji ajikinta , ba komai yafi daga masa hankali ba kamar dukiyar fulaninta dake tsaye suna nema rikitashi da neman zautar dashi gata yar siririya amman duk taku daya sai qirjinta ya motsa ,cike da natsuwa ya raba gefenta zai wuce yana magana can kasan makoshi “me zaki ci ? “bana bukatar komai “Well it seems like baki buk’atar komai bye then”. Ya wuce abinsa batare daya sake furta komai ba .
lumshe idanunta tayi da sauri saboda kamshin turarensa daya sake kaiwa hancinta ziyara wani irin wahalallen ajiyar zuciya ta sauke tare da bud’e manyan idannunta, ganin ya kusan kai bakin k’ofa yasa ta tab’e kyawawan ‘yan lips d’inta tare da d’an cizawa da fararen hakoranta, ta tsurawa bayansa ido qirjinta na wani irin bugu, bata daina kallonsa ba har ya ‘bacewa ganinta sake runtse idanunta tayi tana jin wani abu ajikinta wanda bata tab’a jin irin sa ba game da wani d’a namiji a rayuwarta, shiru tayi tana mai haɗe yatsun hannunta guri daya ta tsakesu , take kwakwaluwarta ta shiga tunanin kalmar daya faɗa mata a lokacin daya shigo dakin “dan ubanki zaman me kike yi ? ki fitar min daga d’aki a tsawace yayi maganar ,ta yaya aka yi ya kawota gidansa ita da take hannun d’an fashi ? ta ɗan zauna a gefen gadon tana zurfafa tunaninta “why did he spoked to me in that manner why? Why zaimun magana cikin tsawa da hargagi haka why? Why?!”a hankali take tambayar kanta kasancewar bata da amsa tambayar yasa ta koma ta nad’e agun cike da damuwa dan ta fara tsorata , babu abinda zuciyarta bata saka mata akanshi ba.
Main parlour’n din gidan ya nufa anan ya tarar da Anas zaune shi kadai yana danna waya ganinsa yasa ya d’ago yana kallonsa tare da sakar masa murmushin gefen baki ,zama yayi akan doguwar kujerar dake kusa dashi yana sauke numfashi “jaguwa!”. Anas ya kira sunansa a tsanake yana kallonsa ya ɗan tsura masa ido yana kallonsa batare daya amsa masa ba ,bai damu da rashin amsawarsa ba dan idan da sabo ya saba da halinsa ya cigaba da magana “me yasa ka d’auko yarinyar mutane batare da kayi tunanin abinda zai biyo baya ba duk da nasan kana da dalilin d’aukota ?”ko zaka iya faɗa min dalilin da yasa ka d’aukota ? yayi masa tambayar ajere yana mai sake tsura masa ido “babu wani dalili ya fada a takaice yana sauke numfashi da kyar “karka faɗa min haka jaguwa kasan yadda muka taso babu boye boye a tsakaninmu ka sanni kasan halina nima haka nasanka na san halinka nasan kana da dalilin d’auko yarinyar nan ba wai dan marin data maka ba Anas ya ɗan yi shiru yana mai zuba masa ido domin bashi damar fadar albarkacin bakinsa .
“naji zafin marin data min fiyye da komai yayi maganar yana furzar da iska mai zafi “nima naji zafi fiyye da kai data mara,amman da ajiyarta da zamuyi mai zai hana ka ɗauki fansan marin data maka idan kuma bazaka iya ba ka bani ita yanzu na gama maka daita Jaguwa yaja tsaki kana yace “matsalata da kai kenan son mata Allah yasa kar ….”dan Allah karka min baki, maganar bakinka bata da kyau ,yanzu dai ya zamuyi daita? “a gaskiya na daukota da niyyar aiwatar da abubuwa dayawa akanta cikin muzgunarwa da zan mata har da kusantarta sai dai zuwa yanzu zuciyata tayi sanyi, ina ganin zan sa amaidaita kawai “better ! domin ajiyarta babu abinda zai mana mu da kullum yan oya oya ne ,yanzu haka akwai aikin daya taso sannan wannan mutumin daya kawo aikin gidan minster ya iso “jaguwa bai ce komai ba ya mike shima Anas ya mike suka fito tare zuwa bangaren da makamansu suke anan ya iske sauran abokan halkallarsa da yaransa ,yaransa na ganin shigowarsa suka sake gyaran tsayuwa suna sara masa zama yayi yana duban jakar kudaden da suka shigo dashi daren jiya ,yayinda agbako ya fice da sauri domin kawo masa abun ruwan zafi bai dade ba ya dawo hannunsa rike da cup din coffe ya ajiye akan ƙaramin table din dake gabansa sannan jaguwa ya soma magana a natse tamkar wanda akayiwa dole ” eku remo “. “yesssss boss!”. jaguwa ya gyara zama yana nuna masa babbar jakar ghana most go “ka buɗe wannan jakar muga adadin abinda yake ciki “, babu mutsu eku remo ya mike ya soma fito da bandirbandir din daloli masu yawa wanda baza’a iya fadar adadin su ba ,”ka raba su kashe biyar duk ku ɗauki kashi day day eku remo ya fad’ad’a fuskarshi da murmushin jin dadi ,ya cigaba da firfito da kudi yayi su kashi kashi kamar yadda jaguwa ya bukata sannan ya umarci kowanensu ya ɗauki nashi kason , bayan kowannensu ya dauka suka kama gabansu dan bawa aminan gurin kamar koda yaushe idan sun yi operation .