KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

ta mike ta shiga bayi ta d’auki lokaci sannan ta fito rike da towel tana goge gashin kanta har lokacin yana nan sai dai zuwa lokacin ya shirya mata Komai nata , ta wucesa ta zauna gaban dress mirror ta d’auki cum tana k’okarin taje gashin kanta.
ta cikin mirror taga ya mike kafin ta sauke numfashi har ya k’araso bayanta ya tsaya ya amshi cum din hannunta yana kallonta ta cikin mirrow sosai ta xuba masa Idanunta .
ya d’auke kwayar idanunshi akanta ya  cigaba da taje mata  gashinta baki sitik me sheki ga tsawo kmr na yaran larabawa yana mugun qaunar gashi a rayuwarsa  , ya d’auki man gashinsa ya shafa mata yana jin tsinkewar zuciya ba zai raba d’ayan biyu ba na rabuwa daita ne bayan ya gama shafa mata mai ya cigaba da taje mata gashin ita Kuwa Jin take kamar yana sake kunno mata wutar soayyyarsa ce ,ajiyar zuciyar data sauke da karfi yasashi  sake kallonta ta cikin mirrow murmushi ya sakar mata har dimple dinsa na lotsawa  ganin yadda gbdy yanayinta ya canza wani iri take ji ajikinta .”

a hankali ta rike hannusa da yake taje mata gashi  dashi  ta waiwayo gbdy ta fuskancesa Shima ita yake kallo yana jin wani sanyin na ratsa sansar jikinsa yatsina fuska tayi tana cigaba da kallonsa”ya’akayi ko Ina miki da zafi ne? Kamar bazata fada masa abinda take ji a gabobin jikinta ba Amman yadda ya kafeta da idanu yasa ta mike tsaye tana motsa labbanta “wani iri naje ji a sansar jiki….”
bata k’arasa maganar ba tajita a faffadan qirjinsa ya rungumeta tsam ajikinsa yana fidda numfashi atare qirjinsu ya dinga bugawa da karfin gaske tayi yunkurin barin jikinsa taji ya sake matseta gam idanunshi a lumshe kamar yadda nata yake a hankali ya dinga jin kasala me had’e da sha’awa yana kashe masa duk wata gaba ta jikinsa yana jin kamar ya canza lokaci komawarta ko yaki maidata gbdy su dangwama a haka “lokaci na tafiya  fa …”
“nasani kin matsu ki tafi kou ?
ya fada yana zareta ajikinsa tare da had’e girar sama data kasa “Allah ba wai na matsu bane Ina son naga dad dina ai zamu dinga had’uwa “Bai zama lallai ba tunda bazaki iya auran dan fashi ba ” ya fad’a tare da  juya wa ya bar d’akin.
shiru tayi cikin damuwa ita dai duk runtse bazata auresa da wannan sana’ar da yake ba amman muddin ya canza aiki  sai Inda karfinta ya kare itama zatayi confused din iyayenta akan aurenta da ib su amince ta auresa .
“zaka daina wannan sana’ar  tabbas zaka daina Kuma kana sona tunda har kayi tunanin zaka iya aurena  inshallahu zamuyi aure sai mun Tarawa amminka  jikoki masu yawa kwanciya tayi akan gado tana fidda numfashi sama sama . abubuwan da ya dinga mata daren jiya suka shiga dawo mata daki daki .

Sai laasar sannan jaguwa ya shigo ya kamota ya rungumeta na kusan minti goma sannan ya zaunar daita akan stood ya tattara gashin kanta ya tamke mata da ribbon ya d’auki mayafin rigar jikinta ya yafa mata ya d’auki jakar kayanta ya nufi kofar fita “muje ko jiki a sanyaye ta soma d’aga ka’fafunta kmr wacce ake tsomawa acikin ruwa sanyi  ,duk sai taji kuzarinta yayi kasa komai ya fita aranta a falo ya tsaya ya ajiye jakarta ya bud’e fridge ya d’auki fresh milk da chocolate cake ya mika mata ta girgiza masa Kai alamun bata ci bai sake cewa Komai ba ya zauna ya fara ci ,haushi kmr ya kasheta taso ya sake yi mata mgn dan yadda ya had’e fuskarsa abun har tsoro ya bata ,bai gama ci ba ya ajiye sauran ya mike tana ganin ya mike ta juya kawai taji ya fixgota ya had’eta da jikinshi yana sauke numfashi tanweer ta dan lumshe idanunta tana Jin yadda numfashinta dana jaguwa ke gauraya kusan minti goma suna rungume da juna sannan ya sausauta rikon da yayi mata ya had’e fuskarsu guri d’aya suna shakar numfashin juna .

harshensa ya dan fito dashi yana lasar lip’s dinta a karshe ya had’e bakinsu ya fara tsotsa sai daya tsotsa sosai sannan ya sakar mata baki still bai ce mata ummm ba bare Uhmmm ya sake d’aukar jakarta yayi gaba tana biye dashi a baya har suka fito haraban gidan yaransa na ganinsa duk suka mike zasu nufo Inda yake da hannu ya tsai dasu ya bude mata gaban motarsa range Rover ash colour ta shiga ta zauna tana kallon haraban gidan datayi rayuwa wata uku a ciki ,bazata manta da komai daya faru daita acikin gidan ba,komai  ya zamo tarihi a rayuwarta .”

bata Ankara ba taji tashin motar me gadi ya bud’e masa suka fita daga gidan tun da suka hau titi babu Wanda yayi magana tafiyar minti goma sukayi ta Kai hannunta ta d’auki wayarsa ta mika masa “ka bude min bai ce mata Komai ba ya amsa ya bude mata ya mika mata ya cigaba da tukinsa ta shiga message sako ta turawa tsohon layinta dake cikin karamar  wayarta sannan  ta ajiye wayar a inda ta dauka .

tafiya me dan nisa sukayi dan sai byn magrib suka k’araso royar stream yayi parking nesa da gidan man tsakanin inda yake  zai Kai tafiyar minti goma  tun daga nesa ya hango minister tsaye yana baza idanu yaga ta Inda tanweer zata bayyana shiru yayi yana karewa gurin kallon tsab”ki fita ga mahaifinki can ya fad’a yana nuna mata Inda yake tsaye ,shiru tayi kmr bazata fito ba “ki fita mana kina bata min lokaci, ta kallesa kmr zatayi kuka dan har hawaye sun cika mata Ido ta yunkura da kyar zata tashi ya fixgota jikinsa ya rungumeta tsam  kuka ta fashe masa dashi.
a hankali ya shiga shafa kanta zuwa  bayanta “is okay ki  kukan please  ya Isa haka  ke da zakiyi farinciki zaki kwana a gida tare da iyayenki da dinbin masoya shine zaki dinga hasarar hawayenki dan zaki rabu dan fashi  ” girgiza masa Kai ta shiga yi tana sheshekar kuka  ya d’ago habarta  Yana kallon  kwayar idanunta da fuskarta  dake kwance shabe shabe da ruwan  hawaye.
tsadadden murmushinsa ya sakar mata “why tanweer ?ya zaki min hk?idan kina son na dinga tunaki a duk bayan second biyu ki daina kukan nan .
da sauri ta shiga goge hawayenta ya Kai bakinsa yayi mata light kiss “oya kije ga dad dinki can ya matsu bai d’aura idanunshi akanki ba ya saketa ta bud’e kofa zata fita yace “karki manta da alkwarinki ” ta dawo kadan tana dubansa kwayar idanunta d’auke da tmby “na zaki sa akamani mana dan naga kin saci numbeta”  dukan wasa ta Kai wa  qirjinsa “Kai ko Allah shiryeka “Ameen na gode da addua “,Ki kula da kanki  sosai ki daina tsiwa da rashin kunya dan akwai  irinmu dayawa acikin garin nan “Kaima ka kular min  da kanka akan wannan sa’anartaka banason ka fad’a hannun  police ”   Faduwa  da nasara  duk daya ne agurina duk wasu  kwalaye dake dakona bazasu iya komai  ba har sai  idan na tare dani ne suka bada hasken cutar dani.”

“karfin zuciyarka na burgeni ta Kalli yatsun hannunta  ta  ciro zoben  silver  me shegen kyau   wanda kakarta wacce ta  haifi mahaiyar ce ta bata zoben, ta kamo yatsun hannunsa   ta zira a karamin dan yatsansa dan anan kawai zai zauna “Ina sonka adnan !”
ta fad’a tana lumshe masa idanunta bai ce mata Komai ba bare tayi tunanin  zai bata amsa.
  Jin yayi shiru yana kallon zoben da tasa masa  tace  ” muje  ka  rakani   bansan gurin nan ba “, numfashi ya sauke yace ” muje anything for you ta sake yunkurawa ta fito Shima ya bud’e bangaren da yake ya fito .
tafiya kad’ai suka yi ya juya yana cewa  “iya nan zan tsaya ” tayi saurin juyowa da sauri  ta  kamosa tare da  nuna masa gefen kumatunta da hannunta alamar yayi kissing dinta  ” kiss  yayi mata  ya juya  ta sake biyosa ta nuna masa d’ayan gefe “oh my goodness tanweer lokaci na tafiya fa kar  dad dinki  ya wuce ya d’auka karya nake masa “.
“sorry! sorry!!  daga wannan shikenan ya furzar da iska sannan yayi mata har   zai sake juyawa  ta sake riko sa “wai meye haka ne ? Yayi mgnr a fusace  “,ai Kaine Kaki  yin aikinka da kyau  saura me mahimmancin tayi mgnr cike da shagwaba tana  nuna masa bakinta daidai lips dinta .
Numfashi ya sauke da karfi  ya janyota gbdy ya rungumeta tsam ajikinsa  ya hade bakinsu guri d’aya ya  fara  tsotsan bakinta nan  idanun mutane sukayi musu  chaaa  tun da suka fara dramar soyayyarsu mutane  suke biye dasu jiki a sanyaye ya zare bakinsa  “,bye tanweer ya fad’a yana juyawa ta tsaya shiru tana kallon bayansa  bai juyo ba duk da jikinsa ya bashi bata wuce ba .
jikinta a sanyaye ta juya ta soma taku a hankali adaidai lokacin da jaguwa ya juyo a  natse  ya tsurawa  bayanta Ido yana kallon yadda take taku a hankali tana rausaya  har ta Iso gurin mahaifinta ,tana gama k’arasawa gurin mahaifinta ta zube ajikinsa .
Jaguwa ya  lumshe idanunshi ya sake  juyawa ya karasa Inda motarsa take pake  ya shiga ya tayar sai dai hakan  nan yaji ya kasa control din motar ya daura duka hannuwansa akan stearing  ….”
????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button