KUSKUREN BAYA 1 TO 48

PAID BOOK
LAST FREE PAGE
Za’a iya biyan kudinsa yanzu
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number
+234 703 534 8686
alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,
domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
????️22
“Shiru yayi yana cigaba da dubansu cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa, gbdy zuciyarsa ta karye sosai , tsananin tausayinsu ne ya lullu’be zuciyarsa dama gangar jikinsa . “hakika ya cutar da zukantasu na tsawon lokaci tunda ya nesantasu da sanyin idaniyarsu ,”ko yaya mahaifiyarta zataji idan ta d’aura kwayar idanunta akanta”? .
A hankali minister ya Kai bakinsa daidai saitin kunnen tanweer ya furta sunanta cikin wani irin yanayi na farinciki da tausayawa “tan my baby !
“Yes dad ta amsa cikin tsananin farinciki da fad’uwar gaba dan jikinta ya bata har lokacin jaguwa na nan atare daita bai tafi ba.
a natse ya zare bakinsa sannan ya dafa kafad’unta yana kare mata kallon tsab , ji yayi hawaye masu zafi sun zubo masa , itama hawaye ne suka samu nasarar zubowa akan quncinta sai dai ita nata hawayen na abu biyu ne suka gangaro mata ,hawayen
rabuwa da burin ranta da Kuma na farinciki dawowarta gurin iyayenta . “Sai dai azahirin gsky wacan damuwar tafi ta dawowarta gurin iyayenta cin ranta da quntata zuciyarta , iyayenta nata ne na har abada ,
amman rabuwa da Adnan fa “? Abu ne mai ciwo da wahala agareta wata Killa ma shikenan ita da shi har abada …”
Wasu sabbin hawaye ne masu radadi suka sake silalo mata “I will miss you my Adnan …..”
ta fad’a akasan ranta tana mai lumshe tsumammun idanunta sannan ta juya a hankali ta tsurawa hanyar data ga yabi Ido tana kallo tana jin kamar karta bi mahaifinta “Ina ma zata iya hakura dasu wallahi da ta koma garesa ta k’arasa rayuwarta dashi “.
cikin mugun tashin hankali ta dawo haiyacinta alokacin da mahaifinta ya dafa kafad’anta yana cewa “yaya dai tan “? ya tambayeta ganin ta kafe guri daya ko kwakkwaran motsi batayi ,wani yanayi yake gani atattare daita wanda bai san ko na meye ba .
Gbdy ta kasa danne kukanta hawayenta suka zubo sharri ….”
nan take hankalin minister yayi kololuwar tashi “menene tan “? ya sake tambayarta cikin tsananin damuwa kallonsa kawai tayi tare da ciza lip’s dinta na kasa da karfi sosai taji zuciyarta na bugawa amman tayi saurin sanyawa jikinta jarumta tace “babu komai dad muje gida Ina tsananin son ganin mumy nasan itama tana can tana jiran qarasowata “. cikin sauri ya riko tsintsiyar hannunta cikin nasa suka fara takawa yana cewa “sosai ma kuwa yau ban san irin farinciki da zainab zatayi ba idan ta d’aura kwayar idanunta akanki , surprise zan mata sai dai kawai ta ganki daga sama “.
“Kai dad ba dai mumy batasan da dawowata yau ba ? tayi maganar tana waigen bayanta ko zata sake ganin Adnan dinta sai dai ina batai nasarar hangosa ba .zuciyarsa ta sake tsinkewa ta shiga karkarwa da shiga tashin hankali , “gsky bata sani ba saboda dan fashin da yayi kidnapping dinki yace kar na kuskura na bar kowa ya sani muddin Ina bukatar diyata araye .”
shiru tayi tana sauraren dad dinta zuciyarta na wani irin bugawa da karfin gaske wanda adaidai wannan lokacin Shima gaban jaguwa banda bugawa da karfi babu abinda yake.
a hankali ya dinga jin kamar rayuwarsa tana rabuwa dashi ne , tafiyarta tafi muryarta burgewa yana zaune yana kallonsu suna takawa da mahaifinta har sanda minister ya bud’e mata gidan gaba ya sanya ta shiga ciki ta zauna ya maida kofar ya rufe sannan ya zagayo da sauri yana waige waige ya bud’e bangaren direba ya shiga ya zauna ya tada motar tare da riko yatsun hannunta ya damke gam cikin nashi kamar wacce za’a sake kwace masa ita .”
Wani irin tsalle had’e bugawa zuciyar jaguwa dake zaune agurin yayi wanda har sai da numfashinsa ya d’an tsaya na wani lokaci hatta bugun zuciyarsa sai daya tsaya wanda yake daidai da barazanar da tarwatsa kwakwaluwarsa da zuciyarsa yana zaune har sai da ya ga tashin motarsu sannan ya samu kuzarin soma k’okarin barin gurin zuciyarsa cike fal da matsanacin firgici da fargaba ya nufi hanyar gidansa .
Yana tafiya zuciyarsa na cike da fargaba da alhinin rabuwa da tanweer yarinyar da kullum yake ikirarin baya sonta zallar tausayi ne kawai .
A hankali zuciyarsa ke sake raunana da narkewa akanta yana tuno abubuwanta da abinda ya faru a yanzu kafin rabuwarsu, ta nuna masa so iya so mai tsayawa a rai , ya lumshe idanunshi a lokacin da zuciyarsa ta hasko masa gefe da gefen quncinta Inda ta bukaci ya sumbaceta a mintunan da suka gabata har a karshe sai da tasa yayi kissing dinta mouth to mouth “bye tan ! ya furta a lokacin daya kawo karshen rabuwarsu yayinda ita Kuma tayi shiru tana kallonsa .”
tafiya yake sai dai tuninta yaki barin zuciyarsa ta huta gabansa sai faduwa yake yana Jin kamar ana buga masa guduma ne sai dai shi anashi kokari yake yaga ya manta daita arayuwarsa tun akan hanya Amman Ina Hakan ya citura yana yakiceta a zuciyarsa tana sake makalewa zuciyarsa da rayuwarsa ma gbdy . a hankali yaja dogon tsaki tare da dukan stearing motar kana ya kamo lip’s dinsa na kasa ya ciza da karfin gaske yana furta “why tan ? ” kar muyi haka dake . dan Allah ki bar zuciyata ta huta “ta yaya zuciyarka zata huta ai yanzu ma ka fara tunaninta”? zuciyarsa ta bashi amsa da haka .
“zuciyata ki shiga hankalinki ki dawo daidai kamar yadda kike before , bari kiji duk nacinki da son karki manta da tan acikinki dole sai kin mantata tun da ba tare kukazo duniya ba dan dole sai na yakiceta sai na mantata don ni nake dake bake kike dani ba, nine zan juyaki ba kece zaki juyani ba ya fad’a yana sake dukan stearing motar tare da falfala gudu akan titi sam yaki goyawa zuciyarsa baya akan kamuwa da son tanweer .
haka nan Kuma ya dinga jin ransa na mugun baci dan haka ya dinga sharara gudu akan titi batare daya san Ina zai dosa ba dan baya jin zai koma gida a lokacin tsaki yake ta faman aikin ja yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa a hankali ya lumshe idanunshi dake kallon titi na second daya sannan ya bud’esu a natse yana tunanin Inda ya kamata yaje domin dawo da zuciyarsa daidai ..”
yana k’okarin d’aukar hanyar zuwa shurem gidan rawar fela wayarsa ta d’auki ruri ,a natse ya Kai idanunshin kan wayar dake qara sunan anas ya gani yana yawo da kamar bazai d’auka ba sai Kuma ya kasa aikata hakan ,anas na dabam ne agurinsa duk runtsi duk tashin hankali bazai iya kin d’aukar wayarsa ba jiki a sanyaye kamar wanda akayiwa mutuwa ya d’auka yana cewa “anas ya’akayi ne ? “Normal jaguwa kana Ina ne ?
” Ina kan hanyar zuwa shurem !
“Kayi me Kuma acan ? Amman dai ka mayarda yarinyar nan ko ? “eh na had’ata da mahaifinta har ma sun kama hanyar zuwa gida “.
“shine Kai Kuma damuwar rabuwa daita zatasa kaje shurem ba “?.
shiru jaguwa yayi yana sausauta gudun da yake akan titi “karka min haka aminina Ina tsananin bukatarka, Ina sonka fiyye da tunaninka banason damuwarka ,haka zalika bana son na rasaka dana rasaka gara na rasa raina raina fansa ne agareka dan Allah ka dawo gida a yanzu, Idan Kuma bazaka dawo ba nima zan biyoka yanzu mu had’u idan ma damuwar ce muyita tare”.
sai lokacin jaguwa ya sauke naunayen numfashi tare da cewa “no kayi zamanka anas banason tafiyarka Kai kad’ai Kai ganin nan ma dawowa gida yanzu ya fad’a tare da karya kwana ya d’auki hanyar zuwa gida Cikin kankanin lokaci ya Kara so gidan saboda mugun gudun da yayi a haraban gidan ya iske anas zaune shi kad’ai ya had’e hannuwansa duka a qirjinsa yana jiran qarasowarsa . naunayen ajiyar zuciya jaguwa ya sauke yana jinjina girman qaunar da anas yake masa baya samu kwanciyar hankali muddin baya tare dashi ,baya iya runtsawa muddin bai ga ya runtsa ba ,baya samun natsuwa muddin yana cikin damuwa , numfashi ya fesar ya cigaba da tafiya a natse batare daya ce masa komai ba .
anas na ganin haka ya mike ya biyo bayansa, kai tsaye jaguwa d’akinsa ya shiga ya janyo kujera tsood ya zauna ya tsurawa mirrow Ido yana kallon Kansa yayinda anas ya tsaya ya jingina bayansa da bangon d’akin yana kallonsa cike da tausayawa dan ya rigada ya afka son tanweer sai wani iKon allah.”
a hankali jaguwa ya sauke naunayen ajiyar zuciya , lokaci d’aya idanunshi ya sauka akan zoben da tan ta saka masa , shiru yayi yana kallon zoben yana Jin kamar ya cire ya yar dan sake nisanta kanshi daita , sai kuma ya kasa yana cewa zuciyarsa”Me yasa zaka yar “?.
“Saboda zoben zai sa ka damu kanka akanta ? ya bawa zuciyarsa amsa da hakan ” damuwa daita ai ba lallai ne kana sonta ba ,sabo ne , shi Kuma daman sabo haka yake ,ka rigada ka saba daita ne shiyasa , har yanzu Kuma akwai wannan sabon da sannu zaka manta daita ne a rayuwarka .”