KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


Bangare tanweer kuwa yau tashi tayi da kurmususun ciwon ciki , ita kad’ai a d’akinta dan mumy da dad basu shigo d’akin ba a tunaninsu bacci take karsu takura mata, sai wajen azahar bacci mai nauyi ya d’auketa, rabonta da cin abinci kirki kuwa tun tana gidan jaguwa, shiru har kusan karfe bakwai na dare bata fito ba yasa mumy ta shigo d’akin kallo d’aya tayi mata gabanta ya fadi ta taba jikinta taji zafi rau a hankali ta dinga shafa mata jiki har ta farka wani irin nauyi taji jikinta yayi mata ta Kasa motsa jikinta ,da kyar da taimakon mumy ta mike ta rakata har bayi ta hada mata ruwa wanka sannan ta fito ta tsaya jiran fitowarta cikin kankani lokaci ta fito ta shirya
Yayinda mumy ta jawota zuwa falo ta shiga kitchen da kanta ta daura mata ruwa zafi ta kawo mata ta zauna a gefenta tana mata sannu bayan ta sha ruwan lip ton ta numfasa tace “mumy wallahi bani da karfi juya juya nake gani “to ai kece ki tsaya a duba lafiyarki a hospital kinki kika matsa lallai sai kin fito ai ga irinta Nan “wallahi mumy naji jiki jiya da daddare banyi bacci ba kwana nayi ciwon ciki “shine dan wauta baki bari mun sani ba yanzu da wani abu ya faru dake fa ?” karki Kara min irin wannan ganganci gashin nan har wata katuwar rama kika yi Ina fatan dai yanzu bakya Jin komai “?
Ta gyada mata Kai alamun “eh .
Mumy ta sake tashi ta kawo mata abinci da kyar ta tura tana kammalawa lokacin mumy ta mike tana fad’in “ki tashi kije kiyi sallah ta amsa da “to” ta wuce d’akinta mumy ta kwashe kayan ta maida kitchen bata tsaya jiran masu aiki ba sannan ta nufi d’akinta dan tayi sallah itama .”

Bayan tanwer ta Idar da Sallah wayarta ta janyo daga inda tayi sallahr ta shiga turawa jaguwa Sako.
Idan ma Wani aiki ne ya rikeka why not ka kirani ka fada min zuciyata ta Samu natsuwa ,Ina da kwarin gwiwa cewa lallai kana sona me yasa ka juya min baya ta hanyar sakani cikin damuwa, ba sai na kai karanka gurin Allah ba but ka Natsu sosai kayiwa kanka hisabi akan abinda kake Shirin aikatawa
Shiru tayi bayan ta tura sakon hawaye na zubo mata akan quncinta wanda take jin zafinsu yau ita soyayya tayi wa Kamun kazar kuku ?” hakika soyayya bata kyauta mata ba tana son wanda bai damu daita ba …”
Tun daga wannan lokaci al’amura suka sake kwance ma tanwer ta rasa kanta ta rasa meke damunta na rashin son kamshin d’akinta da rashin son cin abinci ,hatta turaren d’akinta wari yake mata bata son kamshinsa ga yawon tashin zuciya ga wani ciwon ciki safe da Jiri wani lokaci jikinta yayi zafi dan kanshi Kuma ya sauka batare data sha magani ba duk ba wannan bace matsalarta “me yasa jaguwa yaki d’aukar kiranta duk da ta tura masa sakoni Kashi cewar itace ya d’auka Ko yayi reply dinta , me yake nufi daita ?, shikenan ita dashi sunyi hannun riga ?” shikenan ya mantata arayuwarsa bayan ya rabata da budurcinta ?
Kai! kai !! karya ne ba shikenan ba dan dole zai nemeta ko ba yanzu ba domin jikinta na bata zai dawo gareta akwai tarin qaunarta acikin zuciya da gangar jikinsa “wayyo Allah na zan mutu Adnan idanuwana da zuciyata sun gaza jurewa rashinka na yanwanki biyu danayi babu Kai. tunda ta dawo gida take kunshe kanta a d’aki mumy da dad sun rasa gane kanta mussaman rashin fitowarta da walwalarta ko neman abinda zataci batayi nan fa hankalinsu ya tashi suka tasata gaba suna mata kuka “ki fad’a mana maye damuwarki tanweer mu iyayenki ne zamu fahimceki baki da wad’an da suka fi tunda kika dawo baki da walwala baki cin abinci baki komai da kika Saba please ki tausayawa rayuwarmu mumy ta fad’a tana rike yatsun hannunta .
dady ma kusan yafi mumy shiga damuwa sai dai shi ya kasa cewa komai domin dai idan ya bud’e baki to Shima kukan zaiyi mata “.
Numfasawa tayi tare da sanyawa jikinta jarumta tace “babu komai fa ,atare suka girgiza mata kansu alamun basu yarda ba “Allah mumy idan akwai abinda ke damuna zan fad’a muku kawai dai bana Jin dadin jikina ne yanzu haka Ina treat din kaina da magani malaria ne , inshallahu nan da wasu kwanaki zan dawo daidai “.
atare suka sauke naunayen ajiyar zuciya maganarta ta shigesu tunda sun san ba lallai agurin Mai kyau yanfashin suka ajiyeta ba.
Ta tsurawa iyayenta Ido tana Jin kamar ta fad’a musu gaskiyar halin da take ciki na soyayyarta da jaguwa amman tana Jin tsoro dan bata san yadda zasu d’auki abun ba, ta dai San duk yadda suka Kai ga qaunarta bazasu ta’ba barin tayi soyayya da dan fashi ba bare har su bashi aurenta , idan ma fa yana sonta Kenan mutumin da bai qaunarta ,” kaico dina ni tanwer , ita kanta bata hangowa kanta dacewarsu ba Amman ya ta iya da sharrin soyayya abincin wani gubar wani ita kuma nata qaddarar Kenan soyayya da dan fashi , Allah ka rabamu da muguwar qaddara. “Ameen “taji iyayenta sun furta a lokaci daya sai lokacin ta fahimci a fili tayi maganar Basu kawo wa ransu komai ba dan a tunaninsu saboda rasa budurcinta datayi yasa ta fadi haka sun dade tare daita kafin daga baya duk suka fita suka barta da rukayya .”


A yau asabar gidan shiru ba kamar da ba da gidan ke cika makil da mutane dabam dabam Kuma kowanne zaka Kalla fuskarsa cike take da farinciki da annushuwa a baje a falo aci wannan asha duk abinda ake so a daura wannan a sauke daga safe har dare basu da Hutu daga ita har masu aikin gidan a tsaye suke yini saboda hidimar mai gidan da abokansa.
a falo ta wuce wasu abokan minister daka zo tun awa uku data wuce ta shiga zuwa dakin minister ,dad na zaune a d’akinsa Shi kadai shiru zuciyarsa nayi masa Saka kala kala tunda yasan anyi wa tanweer fyade ya tattara komai ya watsar,hatta nombobin agent dinsa masu kawo masa mata tuni ya gogesu a wayarsa , mumy ta karaso kusa dashi ta samesa zaune shiru ya rafka tagumi tace “ya ka zauna shiru baka shiga wanka bare ka samu damar fitowa ga jamarka can sun hallara yayi dan gajeren tsaki yace “rabani dasu duk gayawar tsiya ne suzo su cika mutane da surutu marasa amfani ta numfasa tace “yaushe ka fuskanci surutu suke damun mutane dashi “? Yayi shiru “na godewa Allah da ka fahimta hakan dan ada ka makance akansu bakaji baka gani kowa sai su numfashi ya fesar batare dayace komai ba.

Ta cigaba da magana to dai ka d’aure ka fito ko dan hira kuyi dasu tunda an rigada an Saba “to shikenan naji jeki kira min tanweer kice ta biyo ta kofar baya saboda su ta mike ta nufi dakin tanweer ta tura kofar alokacin kakarin amai ya fara dibar hankalinta cikin fargaba ta nufi kofar bayi ta Murda ta Bude “tanweer !.
Tana durkushe cike da ciki kamar zata mutu kan mumy ya sake daurewa domin bata ta’ba ganin tana kwarara amai haka ba ,ko rashin lfy take bata amai sai dai zafin zazzabi dan haka ta nufota da sauri ta dafata “me zan gani haka tanweer har yanzu malaria ce “?
Bata iya amsa mata ba tana tsaye har ta gama kakarin ta kuskuren bakinta hade da fuska ta fito waje batare data kula mumy ba kan gado ta fad’a tana numfarfashi .
mumy ta biyota a matukar fusace tasa hannu ta birkitota “bakya Jin Ina Miki magana ne?”nace malaria ce har yanzu take damunki har kike amai haka ?idanunta jajur cike da kwalla tace cikina ke min ciwo “tun yaushe “.
“Yau kwana uku shiru tayi kafin daga bisani ta kamota zuwa byn gidansu cikin haske , gabanta na faduwa ta kamo hannayenta tana duddubawa sannan ta gwale idanunta ta duba cikinsu a matukar tsorace ta tambayeta “ke !kina yin alda kuwa ?
Tanweer tayi shiru tana zazzaro Ido sai lokaci kwakwaluwarta tashiga caji yaushe rabon data Yi alada a tunaninta wata na uku kenan idan batayi wannan watan ba.
Nan take gabanta yayi wata irin mummunar faduwa wanda yasa jikinta ya kamata rawa sai dai cike da dakiya tace “ni wata uku kenan ta k’arasa maganar tana fashewa da kuka “shine dan ubanki ake ta faman ki bari ayi Miki wanki mara kika ki kina so ki haife shege jinin tsinannu ne”?
nan fa tanweer ta kideme ta gigice tabbas ciki gareta sai yanzu tunaninta ya hasko mata hakan, koda take gidan jaguwa tana zazzabi amman bai Kai na yanzu ba mumy ta tsura mata Ido jinita na Kara hauhawa da sauri ta juya ta barta tsaye ta nufi dakin dady tana kuka tana salati “Mai akayi ?ya tambayeta cikin tsananin damuwa da tashin hankali”alhaj mun shiga uku ka d’auki tanweer ka kaita asibiti ayi mata abortion yanzu yanzu “abortion Kuma ?”eh abortion dan kuwa wallahi ciki ga tanweer …..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button