KUSKUREN BAYA 1 TO 48

tashi yayi ya mike tsaye tare da fad’in “me ?!
Hawaye suka Kara zubo mata a hankali ya koma ya zauna saboda juyan dake dibansa bakinsa na karanta salatin manzon Allah gbdynsu tsit sukayi na tsawon lokaci sai mumy dake zubar da hawaye bai yi auni ba yaga numfashinta na fita da kyar da sauri ya tarairayota zuwa jikinsa Yana Kiran sunanta “Zainab !Zainab !!Dan girman Allah karki Kara min tashin hankali akan Wanda nake ciki ya jawo Goran ruwa ya zuba a hannunsa ya yarfa mata ya cigaba da shafa mata ruw a fuskarta a hankali har ta dawo haiyacinta ta bude idanunta tana kallonsa sannan ta sake fashewa da wani sabon kuka da take Jin radadinsu har cikin zuciyarta Nan take tausayinta yasa hawayen minister suka zubo bakinciki kamar ya Kai mumy lahira “kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Zainab wannan jarabawa ce daga Allah Babu Wanda ya Isa ya Hana Hakan faruwa ,ban son ki cigaba da tsananta damuwa domin zata jefaki cikin mummunar matsayi ki dogara da Allah shine zai magance komai mu ma godewa Allah da qaddara ce ta fad’awa tanweer ba bin Maza take ba.
” Aranshi yace Ina ma zan iya goge kuskuren baya dana aikata hakika na tafka kuskuren gashi ya shafi yaruwar dilon diyata .Ta goge hawayenta tayi iya yinta ta tashi zaune ta kasa yace karki damu da sai kin tashi yanzu kiyi kwanciyarki ki huta bari na kwaso magunhunaki naga Wanda ya dace ki Sha .
Ya mike da sauri wani duhu ya rufe idanunshi baya ganin komai sai wasu taurari dole tasa ya dawo ya zauna Yana furta hasbinallahu wa ni’imal wakil yayi ta maza ya sake mikewa mumy tace “ka zauna karkaje ka fadi ka nakasa bai kulata ba ya fice dan yafi bukatar rayuwarta akan tashi .
bai dade ba ya dawo d’akin da kwadon magungunanta ya zauna yana bincikawa jikinsa na rawa
Saboda bacin rai Amman haka ya daure ya d’auki kanta ya d’aura saman cinyarsa yana mata sannu ya goge mata kwalla sai daya kwantar mata da hankalin sannan ya mike ya nufi dakin tanweer cikin tsananin tashin hankali.
tana kwance tayi ruf da ciki ya tsurawa bayanta Ido daman wannan shine karshen masu halin munafurci irin nasa, karshen mai son zuciya kenan, Kuma duk Wanda yaci bashin Allah sai ga karshensa tun anan gidan duniya ,sannan karshen mai irin halinsa kenan dansani.
a yanzu ya gane kuskurensa da yayi tsawon shekaru yana aikatawa a boye ,ya goge kwallan data zubo masa ya kirasa sunanta “tan!
Ta juyo a natse tana fuskantashin “Tashi ki shirya muje hospital a cire miki cikin ” da sauri ta shiga girgiza masa kai alamun bazata zubar .Wani irin juya ne ya soma dibarsa nan kuma ya shiga furta Kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yana maimaitawa cikin haka mumy ta rarrafo ta shigo d’akin adaidaita lokacin da dady yake sake bawa tan umarni “ni dady Abar min abuna ina so …”
“Kina son me dan ubanki ?”me zakiyi dashi ? kina hauka ne Ko kin fara Shaye shaye ne ?”tayi mata tmbyr ajere juya na sake dibarta kafin kace me tuni ta soma yin kasa da sauri tanwer ta sauko daga kan gado suka hadu da dady a lokacin da take kokarin kaiwa Kasa da kyar take fidda numfashi bakinta na rawa tace “tan..! tan !! ki amince a cire cikin ….”
Assalamu alaikum yan’uwa barkanmu da wannan lokacin jama’a , ku taimakawa wannan baiwar Allah Mai suna rukayya wacce ta kasance budurwa ce tana fama da ciwon no-no tsawon shekara daya Kenna saboda iyayenta basu da halin da zasu dauki nauyinta yasa brest dinta d’aya fara lalacewa , rukayya tana zaune ne a garin Kaduna a unguwar kanawa tare da iyayenta dan Allah ku taimaka mata saboda Allah da darajan fiyayyen halitta annabi Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam ga masu bukatar taimakawa ga account number nan 1438775094 Aishat Abdullahi access bank .Domin Jin qarin bayani a tuntubi wadan nan numbobin
07039569430
07037450698
08059623096
Allah ya bada iKon taimakawa .
????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
“Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
????️24
Mumy bata qarasa maganarta ba numfashinta ya sake tsarkewa idanunta na faman zubar da hawayen tashin hankali ,” Ina ta ta’ba ganin balai irin wannan , Allah ya rufa maka asiri ka nemi ka tonawa kanka, dady kuwa duk ya rud’e ya gigice sai zufa yake fitarwa da kyar ya bud’e bakinsa yace “zainab ki rufa min asiri dan girman Allah karki d’aga min hankalinki da sannu zata fahimcemu ta janye kudirinta. mumy taja numfashi da kyar ta sauke ta sake fashewa da kukan bakinciki
ita abinda ya d’aure mata kai mai yasa tanwer zata ce abar mata cikin “?
“To tayi meye dashi ?” cikin muryar kuka tace “da kunnenka kaji abinda ta fad’a wai tana son abunta “. ta k’arasa maganar tana zubar da hawaye.
nan take tausayin mumy ya kama tanwer bisa kuncin data jefa mahaifiyarta muryarta na rawa tace “mumy kiyi hakuri ” ta k’arasa maganar tana zubar da ruwan hawaye mumy ta sake matso ruwan hawaye “tayi hakuri akan me Kenan” ? ” akan zata yarda a zubar da cikin Ko kuma bazata yarda ba ?”
“Sannu zainab komai zai daidaita inshaallahu tanwer yarinyar ce har yanzu batasan ciwon Kanta ba ,batasan rayuwa ba sai mun zaunar daita mun fahimtar daita illar abinda take son jefa rayuwata “.mumy ta sake runtse idanunta gam jikinta na wani irin rawa saboda bacin rai .”
Sallama suka jiyo daga parlour babu tantama muryoyin yan’uwanta ne take jiyowa bashir da Jamil da sauri dady ya jinginar da mumy ya nufi waje yana fad’in ” gamu anan ku shigo ya fad’a tare da juya ya Koma d’akin ,suka biyo bayansa jugun suka ga yayartasu ta rasa kuzarinta. “yaya dai aunty meke faruwa dake ba dai jikin bane ya tashi ?sun fadi haka ne saboda zuciyarta data soma ciwo adalilin dauke tanwer .
dady yace “shine dai yake k’okarin tashi bashir , nan take suka zube gabanta kamar zasuyi mata kuka uncle Jamil ya d’auki Kanta ya d’aura akan cinyoyinsa yana cewa “sannu auntynmu !shima bashir sannu yake mata faman jera mata
sam hankalinsu bai ga tanwer ba ta matso kwalla ta dubesu d’aya bayan daya “kunzo lafiya ?”ya mantaku da yaranku suke “? suka had’a baki suka amsa mata da “lafiya suke sunce agaisheki “ina amsawa ta k’arasa maganar da kyar wasu sabbin hawaye na gangaro mata ta gefen Ido bashir ya goge mata kwalla ,Kannenta uwa d’aya uba d’aya itace babbarsu su hudu ne agurin iyayensu kuma sun mutu sun barsu maza uku ita kad’ai ce mace acikinsu shiyasa ma ta d’auki soyayyar duniya ta d’aurawa tanwer duk da bata rasa kulawa da gata da komai ba daga gurinsu dan sun maye mata gurbin komai duk abinda tace shi sukeyi kafin ma tace sunyi mata suna tsananin qaunar junasu .”