KUSKUREN BAYA 1 TO 48

yana ganin fitarsu ya fito daga cikin motar ya nufi cikin gidan
a falo suka hadu da tanwer tana daga kafafunta da kyar ,tana ganinsa taja ta tsaya ta kasa cigaba daga kafafunta da idanu ya bita yana matukar jin tausayin diyarsa dan bashir ya sanar masa da yadda sukayi daita ,jiki a sanyaye ya karaso inda take ya riko hannunta, zafin jikinta ya ratsa tafin hannunsa bai ce uffan ba ya shiga dakinsa daita .
Suna Shiga d’akin mumy ta mike zaune da kyar ta soma magana cikin zafin zuciya “wato burinki daman ki ruguza rayuwarki da taimakon kanki Ko? ” wallahi danasan haka zaki dawo ki zame min da ban daga hankalina a lokacin da suka tafi dake ba ,Ke dama basu dawo min dake ba da sun rikeki kin cigaba da rayuwa agurinsu , wallahi idan kika bar cikin nan wulakanta zakiyi zaki wulakanta tanwer wannan abun kunya ne duk da qaddara ce ta janyo miki haka amman abun kunya ne mumy takarsa mgnr tana girgiza kai “.
“Dan Allah Zainab ki natsu ki kwantar da hankalinki ,wannan bashi bane mafuta dady ya fad’a “yanzu dai meye abunyi ?”Jamil ya fad’a dady yace “abun yi shine a zubar da cikin “wannan dole kam a zubar dashi Idan ita mahaukaciya ce mu da hankalinmu ai .
uncle Bashir ya gyara zama gaskiya bazata haifi cikin ba ta daurawa aunty ciwo Idan ita bata bukatarta araye mu muna bukatarta dan bamu da wacce yafita a zukatanmu ,bamu da Wani burin daya wuce mu rayu tare dake auntynmu kar bacin ran yasa ki dakatar mana da farincikinki .
Hawaye suka zubo ma mumy ucle Jamil yayi saurin rungumota jikinsa yana share mata hawaye “ki daina kuka idan kina kuka kina kara daga mana hankali ,ki daure awanni ne kawai sukayiwa cikin saura arabata dashi .
Tace “na gode kannena Allah yayiwa rayuwarku albarka kema tanweer zo kusa dani ta fad’a tana mika mata hannu, dady ya rikota ya kawota gurin mahaifiyarta mumy ta rike hannunta gam cikin nata “kiyi hakuri tanwer ki rabu da wannan ciki nayi Imani da qaddara kuma nasan komai daya faru dake qaddara ne bana jayayya da Ikon Allah sannan bazan juya Miki baya ba amman nayi bakinciki cikin nan duk da hallitar Allah ne, wallahi da zan iya dana bar miki duba da haihuwar muke so Ke kadai fa allah ya bani taya zan so ki cire ciki ?dole ce tanwer ,ki bari acire kinji Allah yayi miki albarka kuma Allah yayi muku albarka.”
suka numfasa suka ce” ameen kuka tanwer take sosai Kamar ranta zai fita ta zura musu Ido hawaye nata zuba a idanunta
ta kasa cewa komai domin ita Kanta batasan me zatace ba game da matsayar ciki jikinta
ta rike hannun mumy gam tana kuka Kamar zai fada zuciyarta bakaramin rikita dady tayi ba dan bayason kukanta da sauri ya juya ya bar d’akin ya dawo falo yana cigaba da goge hawaye zuciyarsa nayi masa ciwo ,wani irin bakinciki yake ji a zuciyarsa da gangar jikinsa .
Jiki a sanyaye ta yunkura da kyar ta fito daga dakin zuwa nata zuciyarta cunkushe da bakinciki wayarta ta lalubo ta soma rubuta ma jaguwa sako Kamar haka .
Slm Adnan I don’t why my heart is telling me you can do that to me there’s something behind, dan Allah ka kirani yanzu naji muryarka ina cikin tashin hankali mai tsanani muryarka Kawai bance ka aureni dole ba naji muryarka zai qara min kuzari da kwarin gwiwa idan baka kirani ba zan mutu ???????????? Ina sonka banason na kai kararka gurinka
Ta tura masa tare da rike wayar tana jujjuyawa ta rasa dalilin da yasa ta kasa fada masa cewar tana dauke da ciki ,wallahi da tana cikin haiyacinta baza taba daukar jikinta ta bashi ba dan tasan Ko tabashi ta dadin rai shima wulakanci zai zame mata, yanzu ma da fyade yayi mata tana gani jala inaga itace ta bashi da Kanta ,ita Kanta bata taba zaton zata tsinci rayuwarta haka ba Kusan minti talatin tana zaune tana jiran ta gani zai Kirata Ko kuwa , aikuwa yadda ya saba haka yayi mata yaki kira ta fashe da kuka ta sake tura masa wani sakon .
sakomakon fyaden da kamin mahaifata ta d’auki cikinka sai ka Kira asan yadda zaa yi dashi
Byn ta tura ta koma ta kwanta lamo tana tunani rayuwa tana fitar da mumfashi sama sama Kamar daga sama taji shigowar sako da sauri ta zabura ta mike ta zauna tana adduar allah yasa shine ilai kuwa sakonshi ne ya shigo sai dai ba abinda tayi tsammani ta gani ba dan cewa yayi .
ai likita ce ke dan haka ki cire mana, meye ma na fad’a min cewar kina dauke da cikina?” ni babu abinda zanyi dashi kema kuma nasan babu abinda zakiyi dashi abort it
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta furta tare da daura hannunwanta duka saman Kanta nan take ta shiga wani yanayi na kuncin rayuwa wanda ya wanzar mata da cututtuka masu yawa ajikinta kafin kace me tuni ta rikece ta sake tura
masa wani sako .
Burinka dama ka rugaxamin rayuwa, burinka kuma ya cika sai dai kasani Ko sama da kasa zasu had’e bazan zubar da cikin ba tunda nasan abinda kike bukata Kenan na zubar da cikin jikina ,sai abu na gaba ka jira sanda zan haife abinda Ke cikina Idan ka ga dama ka karba danka Ko yarka Idan baka karba ba na kaiwa mahaifiyarka amman kasani Sai kayi nadamar abinda Kamin karshenka dana sani arayuwa Allah ya Isa tsakanina Da ka
ta tura masa sakon tana goge kwallan da suka zubo mata bisa kuncinta sannan ta sauke numfashi ta koma ta jingine bayanta da abun gado tana tunanin mafuta dan dole ta samowa Kanta mafuta kafin gari ya waye Kwanciya tan tayi cikin tashin hankali da faduwar gaba tuni kwakwaluwarta ta amince mata da maganar mahaifiyarta “na amince azubar dashi mumy, kuyi hakuri mumy da jainja da nayi daku ku yafe min …”
Tunda jaguwa ya karanta sakon tanwer na karshe sai ya dan shiga tashin hankali sbd jin zata kaiwa mahaifiyarsa amman kuma daya tuna batasan kowa bashi ba sai ya dawo daidai ya Shiga jan tsaki ,ya mike tsaye tare da doguwar mika mai isar da sakon gajiya, murmushin gefe baki yayi ya dan yi taku daya biyu ya tsaya yana furta” tanwer Kenan kina dauke da ciki kuma ba zaki zubar dashi ba to me kike nufi da ba zaki zubar ba?
“anas ya shigo dakin a lokacin da yake furta hakan a fili “Yaya dai mutumina ? naga Kamar kana cikin damuwa ?ya numfasa amman bai ce uffan ba “ya Ina Magana kayi banza dani lafiyarka Kake Magana kai kad’ai ? ya sake sauke numfashi yace “ina fa lafiya tanwer na dauke da cikina “
gaban anas yay mummunar faduwa”ci me ..”?
“Wai ciki gareta kuma bazata cire ba.”Anas ya saki baki yana masa kallon mamaki mai cike da tashin hankali ganin Kamar hankalinsa akwance.
jaguwa ya kwashe da dariya yana dafe goshinsa “meye abun daga hankali Kamar kai kayi cikin ?”
cikin tsananin tashin hankali Anas yace “ban sanka da rashin Imani ba kai din mutun ne mai tausayi da sanin yakamata dan Allah ka amshi cikin nan tunda tace bazata cire ba ka aureta Kawai karka ruguza mata rayuwa babu wulakancin da yafi wanda kayi wa tanwer Ko tanko gote bakayi masa wannan hukuncin ba ,ka barshi yana yawonsa son ranshi .
ya zauna kan kujera yana cewa “Na amshi cikin nayi me dashi ?
“me akayi dashi ?”idan baka so ka karba ka bani dan gsky aure zanyi tunda kai bakasan zuru ba an zura maka Ido aga ko zakayi amman sai wasu abubuwa kake ni zanyi aure ka amshi cikin ka bani”. jaguwa ya bishi da kallo yana kada kai kafin daga baya ya kwashe da wata dariya “lallai Anas aure abun yayi min dadi a ina kasamo matar?”bansani ba dan rainin hankali Kawai “.
Aure zanyi na haifi ko d’aya ne kar na mutu bani da masu min addua samun sausauci .