KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bayan kwana biyu su uncle Jamil suka fara Shirin komawa uncle bashir yace zai wuce da tanwer dan ta kara samun natsuwa ko hankalinta zai bar mutumin da take so “ki shirya kinji tanwer muje Katsina.
uncle Jamil ya gyara zama yace gaskiya gara ka tafi daita dan ni Zan iya Mata Dukan mutuwa idan naga tana nacin wancan banzan mutumin,” kai dai kayi hakuri komai qaddara ce fa ni dai idan zata bini zan wuce daita.
dady yace “kuyi hakuri bazata koina ba ta cigaba da zama tare damu shine kwanciyar hankalina Ku cigaba da yi mata addua.
Allah ya tsare mana zuria inji cewar mumy uncle bashir yace “, inshaallah da sannu zata manta komai hawaye suka cika mata Ido bata Jin zata manta da Adnan, yayi mata tabon da bazata manta dashi ba ta yunkura zata tashi tana kuka sai kuma ta kasa tashi dan haka ta rarrafa jikin dad dinta ta kudundune ajikinsa ta rushe da kuka nan da nan ta Karya masa zuciya to daman Shi akwai sanyi da tsananin jin tausayi mutun bare tanwer dinsa daya fi qauna akan komai , idanuwansa suka cika taf da ruwan hawaye a hankali ya d’aura hannunsa a Saman Kanta muryarsa na rawa yake cewa “da zan iya tanwer da na Karbi number yaron nan na aura miki Shi ,wallahi Ke abar tausayi CE amman bazan Iya ba, bazan iya wannan Imani ba .”
“Please dad …..”Sai kuma tayi shiru ta kasa k’arasa maganar
Ahankali ya janyota yace”dubeni mamana da kyar ta dubesa hawaye na zuba “ki daina kuka yana daga min hankali ,baki dace kiyi soyayya da irin wadan nan mutane ba ,bare har ta kai ga aure jikinki bai dace dasu ba rayuwarsa rayuwar wulakacin CE “dady Allah zai daina wannan rayuwar “bazai daina ba “.
ta zuba masa Ido ta kasa cewa komai ta kankame Shi tana kuka washegari haka su uncle Jamil suka tafi sukar barsu cikin Wani yanayi kafin rana ta fadi duk sun isa gidajensu .
Sati biyu Kenan jaguwa na Kiran layin tanwer kwata kwaya bata d’auka ta danne zuciyarta ta cigaba da abubuwan gabanta a karshe ma ta koma bakin aikinta .
*“
Fitowar nazifi Kenan daga d’akin tiyata yaga wasu mutane su biyu a bakin kofar office dinsa suna k’okarin bud’e kofar office din , gabansa ne ya fadi .
wani irin bugawa had’e da tsalle zuciyar nazifi yayi har ya haifar masa da tsayawar numfashi haka nan yaji bai yarda dasu ba nan take Kuma maganganun alhj Tahir suka shiga dawo masa suna masa kuwa acikin kwaluwarsa da kunnuwansa “kwana biyu kawai na baka matata da dana su dawo Idan ba haka zan sa adaddatsa min kai sannan na aika ka lahira “ai Ko bai sa an daddatsa shi ba yasan zai iya sawa a nemishi a rasa na har abada take tsoron haka yake nema yi masa barazanar da tarwatsa masa kwakwaluwa da zuciyarsa, kallonsu yake yana tunanin abunyi .
yaje police station da sheidu daya tattara sai dai gbdy bai ga wanda ya dace ya mikawa sheidun ba, dan akan idanunsa yaga anyi rashin adalci muraran ” wani mashayi ne ya buge wata mata da tsohon ciki ta mutu har lahira shine aka kamo mutumin aka kawoshi office din yansanda aka nufi office din wani ma’akaci dashi , alokacin da shi kuma yake k’okarin shiga office din , abinda ya d’aga masa hankali bai wuce yadda police din Ke k’okari son su gyarota Kawai ya kama gabansa “
Kamar nawa zan bayar yallabai a kashe maganar ?”ka bada million dari “million dari yallabai ?”eh muddin kana son akashe case din Kamar bayi ba domin duk wanda yasan da wannan batun sai an bashi kudi “gaskiya ni bani da wadan nan kudadade “a she kuwa zaka gidan yari”.
cike da sanyin jiki ya juya ya bar station din zuciyarsa cike da bakinciki ya koma gida ranar kasa bacci yayi bai ya suka kare ba amman jikinsa na bashi zaa gyarota .
Naunayyen ajiyar zuciya nazifi ya sauke yana k’okarin juyawa domin tsiratar da rayuwarsa dan yasan idan sun kashesa sun kashe banza yaji an buga masa wata hadadiyar tsawa tare da cewa “ga mutumin da mukazo nema karka kuskura ka kara taku d’aya .”
” nan take jikinsa ya kama rawa” ya zubar da abinda ke rike a hannunsa ya falla da mugun gudu, aiko kamar jira suke suka biyosa aguje.
gudu yake suna binsa domin k’okarin kamasa amman ina tazararsu da nisa gudu yayi sosai yana haki yana neman inda zai boye kuma har lokacin suna biye dashi akan titi wannan karon har da garbi yana gocewa mutane sai kallonsu suke yana
K’okarin shiga wani super market domin buya yayi tuntube da gangar jikin mutun nan take ya zube a jikinsa yana haki yana furta “ka taimakeni dan Allah kasheni zasuyi zasu kasheni yana gama fadar haka numfashinsa ya dauke su kuma mutanen na ganin haka suka juya suka koma da gudun kar asirinsu ya tono dan basu san matsayin mutumin ba .
Nazifi bai sake sanin inda yake ba sai farkawa yayi ya gansa a wani hadadden daki hannunsa daure da drip a hankali ya karasa bud’e idanunsa yana kallon d’akin ya zabura ya mike ya cire drip yana k’okarin durowa daga saman gadon, sallama yaji Da k’okarin shigowa d’akin shiru yayi tare da bin kofar da kallo ganin mutumin daya fad’a jikinsa ne ya sauke ajiyar zuciya .
“Sannu Ko ,ya ka cire drip din tun bai kare ba ?”numfasawa yayi wallahi rashin samun natsuwar zuciya ne dan ban san a hannun da nake ba ya fada yana maida drip din.
ya gyada masa yana duban wanda suka shigo tare “dan Allah Kawo masa abinci “okay yallabai !”ya fad’a tare da juyawa cikin kankanin lokaci ya dawo d’akin hannunsa rike da food flake da plet da spoon ya ajiye ya zuba masa abincin a plet ya saka masa spoon ya mika ma nazifi ya karba.
da hannun daya ya fara ci ya karasa inda fridge yake ya d’auko masa maltina mai sanyi ya bud’e ya ajiye masa ya samu guri ya tsaya yana dubansu .
A hankali nazifi ya d’ago yace “na gode fa ranka ya dade “karka damu me kayiwa wadan can mutane suka biyoka suna neman rayuwarka ?”naunayyen ajiyar zuciya ya sauke ya ajiye spoon din hannunsa a natse ya shiga Koro masa komai dayasani har zuwa sanda aka fara farautan ransa mutumin ya gyada kai Kawai sannan ya soma magana a natse “ka natsu ka kwantar da hankalinka zaka cigaba da zama anan har na tsawon sati zansan abun yi da fatan bakada iyali ?
“girgiza masa kai yayi alamun bai da”okay !ya fad’a tare da mikewa suka bar d’akin .”
Tanweer na zaune a falo tare dasu rukayya suna kallon zeeworld Kiran jaguwa ya shigo ta mike tsam ta koma d’akinta ta d’auka tana d’auka yace “dan iskanci me yasa kika d’aukar wayata kwana da kwanaki ?
“abinda yasa kake d’aukar tawa wayar kwanaki shi ya hanani d’auka .
“okay haka ma zakice? tace “eh!
Idan na bari kika haifi cikin nan mahaifiyata janyowa abun kunya ,wannan abu zai sata jin kunya “.
ai babu abun kunyar daya wuce satar da kakeyi aboye batasani ba wallahi sai tafin jin kunya idan ankamaka akan wannan cikin dan hakan ni dai bazan zubar ba sai kaje kajira ranar da Zan haifa maka danka Ko yarka ka Samu dan aike Ko magajin fashin ba sai kayi training yayan wasu …”
“Enough tanwer ki maida hankalinki jikinki kinsan irin maganar da zaki dinga fad’a min “bangane na maida hankalina ba gsky ce na fada kaima kuma ka sani .”dan nawa ne zai yi fashi ?”to meye aiki har ma sai yafika tunda magajinka ma fiyinka “.
Shiru yay kanshi na Kasa Kamar yana gabanta cikin sanyin murya yace”ni dai ki zubar Kawai idan Kuma kikaki zubarwa …”
“Me zakayi “?
“Nace Mai zakayi idan naki zubarwa ?babu abinda zaka iya yi Kuma ciki baza’a zubar ba kayi abinda zaka yi ina jira ta k’arasa maganar tana jan tsaki tana gama fadar haka tai disconnecting din Kiran ….”
Shiru yayi rike da wayar a kunnensa yana jin zafi da ciwon abinda tayi masa, babu abinda yafi masa ciwo Kamar tsakin da tai masa .