KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Mmn sudais????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
????️25
zama jaguwa ya cigaba da yi rike da waya zuciyarsa na zafi da farfasa a qalla ya kusan minti goma yana tunanin maganganunta,” bai san me yasa zai damu kansa akan cikin ba , cikin ma da bashi da tabbacin tana d’auke dashi .
wani dogon tsaki yaja yana sake kiran layinta , babu ‘bata lokaci ta d’auka qirjinta na bugawa fat fat “Ke ni zakiwa wulakacin ? “
shiru tayi taki ce masa komai sai dai zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri sauri .
“har kin isa ki dinga farfad’a min magana son ranki ?”
ya sake tmbyrta tare da jan tsaki “har ma da kashe min waya ? “shiru tayi still cikin tsananin tashin hankali tana tunanin abinda zata sake fad’a masa wanda zai sake d’aga masa hankali sai dai bata kai ga tattara abinda zata fada masa ba ta tsikayi muryarsa na dukan dodon kunnenta.
“dan kinga ina lalla’baki shine zaki d’auka ko ina jin tsoron ki haifi cikin ne ? “to kar allah yasa ki cire cikin ai cikin ba ajikina yake ba idan akwai shi kenan dan haka ko ki cire ko Karki cire ruwanki sannan matsalarki ce bata Adnan .
ba Adnan za’a dinga kwatance dashi ba , sannan ba shi zai rasa mai aurensa ba . aurenki ne dai bazan yi ba kije ki nemi abokin rayuwarki dan ni tuni na amince da zabin mahaifiyata aikin banza Kawai ki jira ki gani idan zan sake nemanki”.
ya k’arasa maganar yana jan dogon tsaki sannan ya katse Kiran yana fidda wani wahalallen numfashi ,yasa hannunsa d’aya ya dafe goshinsa yana jin zafi da ciwo a ransa, shiru yay na second goma qirjinsa da gangar jikinsa na rawa gbdy sai yaji kimai ya tsaya masa guri daya ya shiga tunanin abinda yayi mata a ganin zuciyarsa bai kyauta mata ba daya farfad’a mata son ranshi dan bata cancaci ya fad’a mata magangun daya fad’a mata ba ,ita din wata aba ce mai daraja da kima a rayuwarsa. amman daya tuna irin maganganun data fad’a masa da irin mugun fatan da tai masa a mintunan da suka gabata sai ya dawo haiyacinsa , komai ya dawo masa daidai, qirjinsa da gangar jikinsa da suka d’auki rawa suka daidaita yaga mai ma yayi mata ai bai mata komai ba . “
Bangaren tanwer kuwa maganganunsa sun daki Kunnuwanta sosai sannan sun wuce har cikin zuciyarta, gbdy ya kunno mata wutar damuwar da take dannewa acikin zuciyarta ,Kawai sai ji hawaye yazo idanunta ya fara zuba akan kuncinta, a hankali ta fara rare kuka mara sauti qirjinta na zafi “Allah ka gani ba wai nayi masa haka dan na wulakatanshi bane , “na yi dan na raunata zuciyarsa,na yine ko zai saduda ya zubar da makamansa ya canza rayuwarsa darajan tace bata zubar ba suyi aure ,ashe wata sabuwar maseefa ta jefa kanta ciki tayi maganar a fili tana sheshekan kuka “wayyo Allah ka d’auki raina na huta da wannan rayuwar da nake ” wani zafi take a kahon zuciyarta sam ba taji kashi daya na son da take masa ya rugu sai ma qaruwa da son shi yayi acikin zuciyarta , tana sonshi muddin zai aureta zatai confuse din iyayenta akwai hanyoyi da dama da idan ta bullo dasu dolensu su hakura su rungumi nata qaddarar su aura mata shi amman shi kuji abinda yake fad’a mata har ma ya amince da zabin mahaifiyarsa ita ko oho zama tayi ta cigaba da rera kukanta tare da rafka uban tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa .”
tana cikin wannan halin rukayya ta shigo d’akin ganin idanun tanwer na zubar da ruwan hawaye yasa ta karasa shigowa d’akin da sauri tana cewa “lafiya tanwer menene Kuma ?”
Rukayya ta samu guri gefenta ta zauna ta riko hannuwanta duka cikin nata tana dubanta cike da tausayawa , runtse idanunta tanweer tayi sai ga wasu hawayen sharrrrrr.”
“wallahi ina cikin damuwa rukayya ,ina cikin tashin hankali na rasa yadda zanyi da wannan rayuwar da nake ciki , komai ya canza min rukayya ina ma rayuwata ta baya zama dawo , “ina ma ban dawo kasar nan ba”..
Rukayya ta numfasa tace” haka ne kina cikin damuwa da jarabawar rayuwa tanwer amman kiyi hakuri da sannu komai zai daidaita ,”sannan kiyi kokari ki rage damuwar nan duk da tasan komai dake faruwa daita amman taki fitowa ta bayyana mata .
” ki kara imani da qaddara komai ya faru da bawa a rubuce yake bawa bai isa ya gujewa qaddararsa, rayuwar bawa tana tattare da qaddarori ne kawai dai Allah ya bamu Ikon cinye jarabawarmu rukayya ta fadi haka ne dan takaita maganar .
“nima ina son na rage tunanin Adnan acikin zuciyata amman na rasa dalili da tunaninsa kullum sai gaba yake , wallahi ina masa wani irin so da bansan ranar da zan daina shi ba , kuma bazan taba fidda raina akanshi ba sai ranar dana ji an shafa fatihan aurensa ta k’arasa maganar tana mai runtse idanunta.”
“Aure ma zaiyi shine kika zauna kina tunaninsa “? tanweer ta gyada mata kai alamun “eh! “gskiya dai ni aganina ki manta dashi kawai ki cigaba da rayuwarki tunda ma aure zai yi ki manta shi kiyi addua sai Allah yayi miki sauyi na alkhairi .
Tanweer ta gyara zama tana kallonta “na fahimceki yar’uwarta zan cigaba da addua na gode da shawarki “to amman banason kina damuwa, tanweer ta sake yin murmushin wanda ciwonsa yafi kuka gbdy kana kallonta kaga damuwa attare daita duk ta fita haiyacinta soyayya ya canza mata rayuwarta muryarta a raunane tace “na gode rukayya inshallahu zan daina .
.” Ki kwantar da hankalinki kinji dan Allah karki sake daga hankalinki akansa Ki fara nemi zabin Allah kiyi k’okari kiyi istahara domin neman zabin Allah “rukayya ko ya min wani irin adduar istaharar da zanyi”.?
“zan koya miki , mu nemi zabin Allah bamu sani ba ko akwai alkhairi atsakaninku idan babu idan kinyi zaki ga komai ya tafi daidai amman Karki yarda ki bari wani yayi miki kiyi da kanki ,zaki iya yi kullum idan zaki kwanta raka biyu zaki yi sai kiyi sallama sai kiyi addaurki ta istahara inshallahu zaki ga cigaba a rayuwarki hatta wannan radadin da kike ji akanshi zaki rage jinsa .”
Jiki a sanyaye tanwer ta janyo handbag dinta ta Ciro biro da farar takarda ta mikawa rukayya.
ta amsa ta fara rubuta mata adduar “Allahumma inni astakhiruka bi ilmika,wa astaqdiruka bi kudiratika wa as’aluka min fadilikal azim,Fa innaka taqdiru Wala aqdiru,wata alamun wala ahlamu ,Wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta tahlamu ana hazal amuru anan sai ki fadi bukatarki sannan ki cigaba,Khairulli Fi dini wama ashi wa akibati amri,Ajilihi wa ajilihi,Faqdurhuli wa yasshirhuli summa barikli Fi,Wa in kunta ta’alamu inna hazal amri sharruli Fi dini wama ashi wa akibati amri ajilihi wa ajilihi,Fasrifhu anni wasrifni anhu,Waqdurliyal khaira haisu kana summa ardini bihi.”inshallahu inshallahu tanweer sai kinga komai ya daidai ki mikawa Allah alamirinki zai isar miki wallahi idan Adnan rabonki ne zai dawo da kafafunsa har ma kuyi aure “na gode rukayya inshallahu zanyi ,sun dade suna hira rukayya na deba mata kewa , bata ta’ba sanin zama da mutun guri d’aya yana kawowa rayuwar mutun sauyi ba sai data dawo gida ta iske rukayya , rukayya na k’okarin kawar mata da dukkanin damuwarta tare da bata shawarwari masu kyau .”
Da misalin karfe goma na dare kowa ya shige d’akinsa tanweer ta shiga bathroom dinta tayi alwala ta fito ta sanya dogon hijab dinta tare da shimfida sallaya tayi sallahrta raka biyu sannan ta gabatar da adduar istaharar da rukayya ta rubuta mata sannan ta nemi guri ta kwanta akan katifa zuciyarta cike da tunanin Adnan kala kala a hankali wani bacci mai ni’imal ya d’auketa .”