KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“nasan kin fahimci wani abu akaina , ta sake d’ago ta dubansa tace “ban fahimci komai ba idan akwai wani abu ka sanar min ina da tarin ayyuka a gabana ya sauke numfashi yace “nasan kin fahimci yadda nake sonki Ko?”ta numfasa sai dai bata ce uffan ba “wallahi ina sonki tanweer kuma da aure ta runtse idanunta tausayinsa ya kamata tayi sauri ta bud’e idanunta a sanyaye take cewa” kayi hakuri kayi addua Allah ya sauya maka wata dan ni zuciyata tayi nisa a soyayyar waninka inshaallah nan kusa za’a shafa fatiha
“inshaallahu Ke rabona ce bata Wani ba ba kuma zan hakura ba har sai an shafa fatiha wanda nake fatan da ni ne “to wannan kuma yana ga Allah domin shi Ke shirya yadda yaso amman dai ina maka fatan samun wacce ta fini domin Ko da zan zamo mallakinka gangar jikina Kawai zaka rayu dashi amman zuciyata baza ka taba galaba akanta ba “.
Ya gyara zama yana kallonta “shikenan na fahimceki amman fa bana jin zan hakura dake ki bani dama mu dinga zantawa koda kuwa a office ne kafin nasamu matsayin zuwa gida .
ta kallesa sai ma ya bata dariya “kaje ka nemi mata tun kafin a fara kiranka da gwaro dan nasan shekarunka sun kai hamsi ta k’arasa maganar tana murmushi “ki bari na rasa wacce nake so tukun na sai na rufe ido na kwashi Ko wacece inyi maneji “no karkayi haka ai ita rayuwa ..”
turo kofar office din akayi tare da shigowa ya katse mata maganarta aka maida kofar office din aka rufe garam cikin zafin nama da zafin zuciya .
a natse ta d’ago zuciyarta cike da mamaki rashin neman izini da ba’a yi ba kawai idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye ya soke duka hannuwansa ciki aljihun wandonsa ta gaba ,ya balain kafeta da rikitattun idanunshi yana jifanta da mugun kallo ,
yayinda take zuciyarta ya soma bugun tara tara ganin yaki dauke idanunshi akanta yasa ta sunkuyar da Kanta Kasa sannan ta cigaba da duba file din data fara aiki akansa sai dai gbdy komai nata ya tsaya dan batayi tsammanin ganinsa ba ji tayi kmr an zari wani abu ajikinta ” me ya Kawo Shi gurinta ?” tayiwa Kanta tmbyr da babu mai bata amsa sai Shi .
Dr muyis ya juyo a hankali ganin Kowa ye ya shigo babu neman izini ,shima sai da gabansa yayi mugun bugu da karfi ganin ingarma nmj tsaye sai dai cikin kamala yake sanye cikin bakaken kaya har facing cap dinsa da takalmin kafafunsa da agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunsa , ya juyo a hankali ya dubi tanwer fuskarsa da alamar tmbya “dr muyis nayi bako ka dan bamu guri “.
“okay my tanwer zan dawo
zuwa anjima mukarasa mgnrmu ya mike tsaye tare da juyawa ya mikawa jaguwa hannu amman kememe yaki bashi hannu illa kallon hadarin kaji da yayi masa yana yatsina face, dr muyis yayi mamaki active dinsa zuciyarsa cike da damuwa ya d’aga kafadunsa ya bud’e kofa ya fita .
kusan minti biyar shi bai fita ba sannan shi bai karaso inda take ba, dan haka ta mike tsaye da zumar bar masa office din idan ya gaji yasan inda dare yayi masa ta gefensa tabi zata wuce cikin zafin nama yasa hannunsa daya ya dawo daita ya tsayar daita a gabansa batare daya ce mata komai ba ya tsura mata rikitattun Idanunshi masu bugar mata da zuciya …..”
wani yanayi mai tsarkakiya da wuyar fassarawa ya ziyarci gangar jikin duka masoyan guda biyu a bangaren tanwer tsantsar soyayyar da qaunar jaguwa ne yake bin dukkan ilahirin sansar jikinta ,ji take Kamar ta mutu ta huta akan wahalar da take sha akansa . “
Shim abinda yake ji Kenan a sansar jikinsa ji yake Kamar ya zarta dukkan maza sa’a a duniya data makance akanshi, sun shiga wata duniya wanda ma’abota so da shauki ne suka san zakinta a hankali yake Jin qaunarta na sake huda zuciyarsa yayi taku biyu ya had’eta da qirjinsa yana fidda wani wahalallen numfashi..”
saurin dauke numfashi tayi tana so shi kamr ranta ita Kanta tana mamakin zazzafan soyayyar da take ma jaguwa mai tafiyar da dukkan wani motsi da bugun zuciyarta da numfashinta .
yadda soyayya Ke walagigi da zuciyar tanwer haka ne yake faruwa da zuciyar jaguwa a sukwane ya motsa lips dinsa “,waye wancan mutumin daya tasaki gaba kamar zan ciyeki “? ya k’arasa maganar cikin zafin rai .”
Shiru ya biyo bayan tambayarsa dan bata jin zata iya bashi amsa idan tace lallai sai ta bud’e bakinta to kuka ne zai biyo baya ta juya a hankali zatabi ta gefensa hannunsa ya kai ya rike tsintsyar hannuta gam ya karasa gaban table dinta ya d’auki handbag dinta ya makala mata a kafad’a ya soma tafiya daita har ya fito daga cikin office din magnata take son yi amma bakinta ya kasa furta komai illa jikinta dake wani irin rawa sakamakon had’uwar da jikinsu yayi , bai tsaya a koina daita ba Sai a inda yayi parking din motarsa ya bud’e mata gidan gaba ya Sanyata ya rufe ya zagaya ya Shiga ya tada motar ya bar haraban hospital din.”
Sosai yake gudu akan titi batare daya Kalli inda take ba ,itama bata Kalli inda yake ba idanunta na kallon gefen titi ,dan cija lips dinsa yayi yaso tayi masa mgn amman yaga ta sharesa saboda taurin kai irin nata dan haka bai yi mgn ba shima ya yatsina fuskar ya cigaba da tukinsa sunyi tafiya mai nisa still bata juyo tace masa ina zai Kaita ba har ya karaso bakin get din gidansa yayi hon aka bud’e masa get ya shiga da motarsa ya k’arasa inda aka tanada domin ajiye motoci yayi parking sannan ya kashe motar ya bud’e bangaren da yake a hankali ya fito ya zagayo side dinta ya bud’e mata kofa ya tsaya yana kallonta muryarsa a kasalance yace “fito !
“Na fito nayi me ?” sai lokacin tayi mgnr cikin karfin hali da dakiyar zuciya .
“Bansani ba kuma Karki kara bani irin wannan amsar Oya fito” .ya fad’a yana zabga mata harara kin fitowa tayi ta makale handbag dinta ta cigaba da zama tana girgiza masa jiki tana yatsina fuskar .
on-expecting taji ya sunkuceta ya fito daita ya shiga cikin gida daita suna shiga babban falon gida ya sauketa yana cewa “daman abinda kike so Kenan jikina ya hadu da jikinki gashi nan nayi miki abinda kike so .”
Ta kallesa idanunta cike da bacin rai ta rasa me yasa yake mata haka “ki samu guri ki zauna doctor na zuwa ta duba min lafiyarki idan aka dubaki baki dauke da ciki sai kinga yadda zanyi dake a gidan nan duk sai na fanshe d’aga min hankalin da wahalar dani da kikayi”.
still dai bata ce uffan ba sai tagumin da tayi cike da zullumi abinda zai mata .
Byn minti shabiyar sai ga doctor tayi sallama ya bata umarmin shigowa ta shigo suka gaisa da jaguwa Kawai dan ita tanwer Ko kallon inda take batayi ba .
ya mike tsam ya k’arasa inda tan take zaune cikin tashin hankali ya riko hannunta cikin nashi batare daya ce Mata komai ba ya fara tafiya doctor na biye dasu Abaya yana mata bayani abinda yake bukata tayi masa har cikin bedroom dinsa suka shiga ya zaunar da tan sannan yaja ya tsaya tare da rike kugunsa da hannun daya yayinda dayan hannunsa Ke qirjinsa yana shafawa a hankali .
Doctor ta ajiye kayan aikinta ta kalli tanwer sannan ta mika mata wata karamar roba “ki shiga bathroom kiyi fisari aciki ki Kawo”. kin amsa tayi sai da jaguwa ya maka mata harara sannan ta amsa ta nufi bayi bata jima ba ta fito ta mikawa doctor roba ta samu guri ta zauna tana mamakin karfin halinsa da rashin tsoronsa .