FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana zaune a daki tana ta lissafe lissafen yadda abubuwan ta zai kasance
Gashi wann karon haka zata koma bata da ƙawa tunda sun raba gari da babban kawarta najaha.

Aganinta ko taje schl ma yanzu bazata kara kula wata yarinya da sunan kawance ba saidai kawai a gaisa da yan aji amma bazata kara amincewa da wata ƙawa ba.

Wasime tana da zafin kishi sosai har ayanxu bata gama amince da cewa najaha zata kyale mata mijinta ba..

Sai can after asr prayer snn ta bar wajen ta sauko kasa ta dada kimtsa falon ta bade shi da qamshi snn ta nufi kitchen tafara tunanin abinda zata dafa mishi wanda zaici yaji dadi .

Dankalin turawansu daya rage saura dan kadan ta kwashe dika a tray ta zauna ta fere su in round shapes masu kyau ta wankesu acikin ruwanta mai tsafta ta barshi yana tsantsanewa a colander.

Da akwai sardine fish dasuka rage shima baifi saura gwangwani biyu ba ta dauko dika ta fito dashi waje.

Kayan miyanta ta hada dan dede nayin irish poridge Kominta ta hada tsaf,Abunda kawai ya rage mata babu shi agidan shine ganyen alaihu,gashi kuma bata ma da kudi ahannu bare tace zata dan fita waje ta zaga koda xataga kasuwa ta siyo ganye.

Basarwa tay ganin lokaci nakan karatowa ta dora tukunya ta zuba mangyada ta soya kayan miyanta da spices masu qamshin dadi..
kafin kace wani abu har faten dankalin turawarta ya nuna,yaji kayan miya da man gyada ga kifin sardines nasha nash bakaramin qamshi da kyan gani a ido yay ba..ganin abincin yay mata yadda take so yasataji farinciki acikin zuciyarta..gashi kusan komi ba gidan yadan ja baya,ashe najaha inta amshe kudi ahannunsa ba wani siyan abincin dayawa takeyi ba saidai ta siyo dan kadan sauran ragowar kudin kuma sai takai ma uwarta ta soke matasu a asusunta.

Hatta madararsu yaja ƙasa hakama kwai shikam ba baifi guda biyarne acikin mazaunin sa ba,kyabe bakinta tay ta jawo gwangwanin madarar ta juye duka a bowl ta hau hada masa kunun madara wanda baiyi kauri sosai ba tana gamawa ta juyeshi acikin flask da zafi zafinshi.
Tukunna Ta debo abincin da komi ta kawosu falo ta jera masa akan dinning table komin ta neat.

Komawa kitchen din tay ta kimtsa waje yay fes
Snn ta wuce daki ta doro wankarta ta fito ta shafa manta na palmers coco butter ajikinta maicsulbi da sheƙi, shima kanshi man saidata bubbuga gwagwaninsa kafin yake saukowa sabida shidinma ya dau hanyar karewa kuma bata san ta yadda zata fada mishi tana son wani man shafawar ba

Farar powder kawai ta murza akan fuskarta ta saka ma idonta kajol yay baki ya fito da girman idanunta wanda sukenan farare tasss kamar ana wankesu da ruwan madara, sosai wasime tay kyau duk dama bata goga komi a soft and surple lips dinta ba.

Riga da skirt din wani material ta dauko tana kallo, zuciyarta cike da tantamar sakashi ajikinta dan harga Allah ita bata cika son saka skirt yana matseta ba, gani take kamar xatanajin kunyar yawo agaban mutane da matsatsen kaya,ita dai dressing in har kana so ya burgeta tanajin kanta so comfortable toh ka dinka mata zani da riga ko ka mata bajajjen gown ko A shape gown wanda bazai wani takurata ba.

Haka de ta daure ta saka wannan material din light purple colour ne kuma kalar bakaramin dauke ido yake dashi,barinma daya hadu da coca cola shape din wasime dake barazanar tsatsafowa.

Haka dinkin sket din nan ya cika shape din hips dinta fam yay mata cas cas duwaiwaikan har wani juyi suka soma,rigar ma fitted ce mai three qtr hands hakan yasa nonowarta suke nuna alamar girmansu sosai.

Dankwalinta ta dauka ta daura agaban mirror ayanayin daurin push back daya balain dacewa da shape din fuskar ta,gashi turaren ta ma ya kare babu ko na kale
.wani white humra mai sanyin qamshi da bilti ta mance dashi akan mirror ta dauka ta shafe ilahirin jikinta dashi tana saukowa kasa cikin kamammiyar yanayi adaidai lokacin ne taheer ya iso bakin gate ya danna horn mai dan kara ..

Agogon falon ta kalla taga har biyar saura.
Tuno da cewa ta cikin gida yau ta kulle gate din yasaka ta sauƙa kasa da wurwuri tayo waje domin ta budeshi..tana bude mishi gate din ya shigo ya isar da motarsa har wajen dayake parking

Satar kallon wasime ya dingayi harta ja gate ta rufe taheer bai daga idanunshi akanta ba ..

Cikin sanyayyar takunta mai tafe da aji da saurin shiga rai ta iso gareshi lokacin yana daga zaune yana jiranta daga zaune yadan bar murfin motarsa daya abude yana dan murmushi

Kakkaf ya kare mata kallo daga sama har tsakar kanta harta iso gareshi kanta na kallon kasa, zata sunguna kasa ta gaishe shi kenan yay sauri wajen dagata
,jawota cikin motar yay game da dorata akan lallausar cinyarsa cikin sauri da jin kunyarsa ta rufe idanunta sosai tanamai kin hade idanunta dashi

Murmushi yakeyi jin yadda gaba daya jikinta yake fidda sassanyar qamshin turaren humra,turare na wanda baisa amfani da irinsu ba,ahankli yakai bakinsa ta gefen wuyarta yana mai shunshuna qamshin ata wajen wanda atake sanyin dadin yahau shigarsa yana shakowa yana wani lullumshe idanunsa akasalance

Qamshin gabaki daya sai ya bi jikinta wani irin rungumarta yay idanunta haryanzu a lumshe tayi wani lamo itama ta kankameshi suna shako bugun zuciyar juna.

Acikin fitanannyar numfashinsa maganan nasa ta sauÆ™a acikin dodon kunnenta yana rada mata cewa “u smell nice nd look beutiful”..da kyar wasime ta dago ta bude idonta ta dan kalleshi sabida bugun zuciya datakeji akansa mai tsanani.

nakasashiyar kallon dayake binta dashi yasa haka kawai taji ta kasa iya resisting din kyaun fuskarsa, ahankli cikin gushewar hankli da tunani da tunzirata da zuciyarta yakeyi takai hannunta kan sajen fuskr sa dake mata mugun kyau tana shafa mishi wajen ahankli tanai masa ziriya.

nishi nishi ya soma sakar mata jin hakan datake mishi yana kkrin jefa shi cikin wani hali

Gani ya narkewa mata fuska gaban ta saiya hau fadi ta soma kicin kicin akan cinyarsan da alaman zata sauka.

Wani fizgota jikinshi yay ta dan firgita ta lafe akan kirjinshi,a cikin wata shagwababben salo a can cikin kunnenta ya rada mata sautin muryanshi yana cewa
“Hey Im back nd i dint get my welcome back kisss”

Idonta ta kara rufewa dan kunyarshi,yana ta kallon ta ahaka,can saiga ta budesu ahankli tana murmushi mai kayatarwa harta matso kusa daf da kuncinshi ta dora masa kiss mai tsuma awajen…

Wani komawa da baya taheer yay ya jingina bayanshi akan seat ya wani lumshe idanunsa ya sake jiki kamar ya suma..

A dame Wasime ta dinga kallonshi kirjinta na bugu a dan tsorace ta matso kusa da kan kyakkwan fuskarta daf da nashi suna shakar numfashin juna,kai hannunta kan fuskar nashi tay tana shafawa ahankli farareb idanuwanta cike tam da ruwan hawaye Muryanta na rawa cikin sanyin murya tace”Yaya?……
Is not free,chat 08060712446
ASSALAMU ALAIKUM PLEASE INA NEMAN ALFARMA WAJEN KU GOBE BAZANYI POST BA ZAN MUKU EDITING DUKA PAGES NA WEEK DIN NAN NA TURO MUKU SHI ON SATURDAY NIGHT,COS I WLL BE FASTING FROM MONDAY DOWNWARD BANA SON INYI TYPING AWNN LOKUTAN,AND BANA FUNCTIONING WELL WHEN IM HUNGRY SEF,SO PLS BE NOTIFIED SARTUDAY NIGHT U WLL GET ALL THE POSTS FOR THE WEEK,NAGODE.
THIS NOVEL IS NOT FREE IS 300₦ VIA 0152983148 MOHD SULE SURAYYA GTB 08060712446.
7/25/22, 19:19 – Kawata: SURAYYAHMSFR44
my love my world …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button