FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wasime na dakinta tana kwance tun safe bata motsa ba sabida ciwon kai da hayaniyar datasha shi acikin kwana biyun nan bana kadan ba.

Juyi take duk hanklinta ba a kwance yake ba yau wata guda kenan rabonta da suyi magana da mijinta,gashi nasihohi da jan hanklinta da manyan mata sukayi mata gabaki daya yasa zuciyarta ya karajin sha’awar rayuwa kusa da mijinta, tana son ta dandana zaman aure.

Can da yamma bayan ta idar da sallahn asr kenan tana zaune akan dardumarta can saiga prof ta shigo dauƙe da murmushi mai sanyi akan fuskarta suna hade ido wasime ta sauke kanta a ƙasa da sanyin murya ta gaisheta

Prof nadaga tsaye ta amsa tana cewa ki tabbata kin shirya nan da karfe hudu da rabi driver zai kaimu airpot flight din taheer ya kusa isowa.

Bata san komi gameda hakan ba gabanta ne ya wani irin fadi…

Tsabar yadda kirjinta ya buga tanajin faduwa gaba mai karfi bata ko iya amsa prof ba,dan tasan da ta budi baki yin wani magana ynzu hala shirme ne kawai zai fito wanda akarshe zaisa taji matsanancin kunya.

Kanta na kallon kasa har prof ta sake kofar tay gaba,tanajin sakin kofar prof ta mike a rikirkice ta daka wani tsallen murna cikin tsananin farinciki tana cewa Alhamdullhi Alhamdulli yau zanga yaya na wayooo Allah na
Tana cikin murnan hawayen farinciki suka taru acikin kwayar idanunta suna saukowa jiki a matukar sanyaye ta koma kan gadonta ta kwanta a sulale ta shiga
Saukesu slowly suna diddiga akan pillow Kirjinta na wani irin bugawa da tsumayin sassanyar shaukin dayake neman zautar da ita,daga yanzu fa shikanan damuwarta da bakin cikinta da duk wani wahalarta ya kare.

Yau muradin zuciyarta abun kaunarta zai dawo gareta..raunataccun idanunta da suka cikke da hawayen farinciki ta lumshe tunanin yadda idanuwan su yau zata soma cin karo da juna…

wani irin estactic feeling ne ya mamayeta,tsumayi da shaukin kaunarsa na dada shigarta ta kowani sassan kofar dake zuciyarta wanda sanyin sa yake ratsata tamkr ana watsa mata ruwan sanyi.

Da kyar ta iya finciko kanta kanta daga wannan fitinanniyar yanayin ta mike a gurguje tayi hanyar bayi Allah ya so daman yanzu nan ta fito daga wanka kafin tay asr,so wanke fuskanta kawai tay da sabulu ta dan kikkimtsa kanta sann ta fito tay gaban mirror tana ta kallon kayan kwaliya dake wajen kirjinta na bugawa da dan karfi saitaji ma kamar ta rude ta rasa wani irin fuska ya kamata ya ganta dashi.

A karshe ma bata iyayin komi ba sabida karantowar lokaci Kwalliya tay sama sama ta shafa smooth l’orels powder fuskan ta yay smooth yana sheqi kamar ka lashe as usual
Ta yi ma lip dinta nude make ul shima tay lining da brown liner,snn ta goga tsinken kajol a idanunta ya dada fito mata da zarran idanun nata shape din su sukayi
ÆŠara É—ara suka bada wani mersmerising looks
A hankli tay creating smoky eye looks da bakin eye shadows ata saman idonta,inda yaja fasalin idanun suka dan tsaya acan sama making the eyes to look sexy nd smoky at same time cool as flowing morning breeze.

Wata hadaddiyar turkish Abaya plain dede jikinta with touch of shiny gold ta saka ajikinta,tasaka bakin hula snn tay rolling plain black veil na abayan ta saka asalin heels mai tsiririn igiya,da har ta dauko damin turarruka zata feffesa sai kuma ta tuna rigimar mutumin na ta yanxun nan zai samu dalilin yimata fada saiyace tana sa qamshi wanda ba muharamnta ba sunaji

Sama sama ta fesa turarruka masu sanyin qamshi har kala uku taking note on special spot irin su hammata gefen wuya da tafin hannu..bayan ta kammala komi ta dauki side bag dinta baki da wayarta golden colour snn ta fito .

Samu tay har anono ma ta fito suna jiranta a bakin motar,tana fitowa kowa na satar kallonta yadda tay kyau, kanta na kasa bata ce musu komi har aka nufi hanyar airpot itadai bata dena Addua acikin ranta tana kiran sunan Allah a zcyarta ba sabida harwayanzu bakaramin bugawa kirjinta yakeyi ba.

Karfe 4:30pm dot suka iso kaduna state international airport da motarsu babban jeep din BMW sabo kal da taher ne ya siyawa mum dinsa just few month ago tun kafin ya dawo.

Suna sassauka sukayi cikin waiting area na arrivals suka tsattsaya sunata kalle kalle hoping by now kam har taheer ya iso tunda karfe hudu da rabi dama yace mata flight dinsa zai sauko.

Anono ce kawai take cikin hayyacinta sauran daga mai duba agogo akai akai sai maijin kamar numfashinta zai dauƙe sabida tsabagen bugun zuciya.

Gabaki daya hanklin wasime baya jikinta zumudi da faduwar gaba ya gama rikirkita mata yanayi.after 10 min da basugansa ba prof ta juya a gurguje tacewa anono su zauna anan bari taje tay tambaya taji ko hala an shifting time din flight din ne basu sani ba.

Akan wani silver colour chair anono ta zauna abunta, prof tana barin wajen Wasime ta kalli agogon hannunta ganin karfe biyar saura yasa ta ajiye jakarta da wayarta kusa da anono tana cewa inno dan Allah barinje ta chan ina dawowa ynzu,tun bata gama rufe bakinta ba anono ta riko hannunta da fuskar tuhuma tace “ke kuma ina kika sani anan da zakije can din?yo sai du kutafi ku barni nikadai akan me?…cikin langwabar da wuya wasime tace inno dan Allah zan dan duba wani abu ne yanzu zan dawo”..bata tsaya jin me inno zatace ba ta kwace hannunta cikin hanzari ta kama hanyar dosar wajen da ta tsaya tana kuka the very Last time da suka rabu tun ranar da zaije karatu.

Tafiya take kanta na kallon kasa jin yadda kirjinta ke tsananta bugawa,tana isa dede wajen ta dingajin wani iri kamar ana kara ma kirjinta bugu mannuwa tay da jikin bangon glass din a hankli ta kafa shanayayyun idanunta akai tana leÆ™awa ta ciki koda zata gansa,wani sanyi ta dingaji ajikinta kamar ana mata fifitata,gabaki daya hanklinta na gun ganin babu wanda yake wulgawa ata wajen face ma’aikatan jirgi ana famar clearing kayayykin wanda suka sauko just few min ago,ata can kofar dake ta bayanta taheer ya fito yana tafiyar sa very calmy bayan rabuwar sa da wani mutum da tuntuni shi ya tsaresa suke tattaunawa,

Dago kwayar idanuwan sa na farko saida kirjinsa ta amsa da bugu ganin yanayin tsayuwarta awajen babu abunda ya tuno masa face ranar rabuwarsu dabazai taɓa manta yadda yaji tsananin rauni da karayar zuciya akan kukan data dingayi a wancan lokacin ba.

tun daga yanayin yadda yaga tsayuwarta ya san tabbas wancen wasime ce,tahowa yake ayayin da ya dora kyawawan idanun sa akanta yana mata kallon kurilla zuciyarsa ya gama zaucewa akan yadda yaga matar Sa ta wani girma,ta kuma hadu ta dawo wata babban budurwa mai aji,p cap din daya saka na plain green kalar sojojin america was customised da sunanta writen boldy ata gaban hular,tafiya yake yanajin yadda kirjinsa yake bugawa da dan karfi,zuciyarsa na kara tsananta halbawa yanajin kamar bazai iso gareta ba.

Wasime dakejin kamar zatay kuka tsabar yadda gabanta ke faduwa da bata ganshi anan ba hawayene suka taru a idanunta kamar wata marainiya ta rungume bangon wajen haryanzu de tana tsammanin ganin bullowar noorul qalbinta.

can sai ta juyo ahankli ta sanyan idanuwanta ta bayanta caraf sai taga mutum na tunkarota, acikin sauri taheer ya dauke kansa ya dena kallon ta ya sauke kansa can Æ™asa yana kan dosota inda take acikin sanyin takunshi mai bala’in daukar hankli.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button