FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

A ta fannin saheeb kuwa abubuwa yau sun gama cunkushe masa babu qamshin khalid babu dalilin razia dukansu wayoyinsu a kashe Gashi baida lambr wayan da zai nemi maman razian bare yaji abunda ake ciki.

Lokacin dinner na karatowa 8pm na dare kowa ya shirya prof da momy omatere suka biyoshi wajen saidai basu shiga ba sabida abun zallan su yasu ne da manyan bakinsu.

Chief medicals da associations masu karfi duk sun halacci taron saheeb yaje ya saka irin kayan da taheer ya sa jiya zak zak da yaqinin shima ayabeshi ko ayi admiring dinsa still awajen bai rasa wanda sukayi mocking dinsa ba
Wasuma ke ce masa copy cat duk dai ya basar ya daukesu mahassada.

An fara program bada dadewa ba,taheer yafarajin missing din matarshi aranshi sosai duk abinda akeyo awajen hankilinsa baya kai tunanin wasimen shi gabaki daya ya cikka masa kirji tun akan case din mamanshi da ya jijji bayanansu sai jikinshi yay sanyi sosai Yasan dolene yakasance ya zalunce matarsa itama.

Tuntuni tunani yake na yadda zai kama saheeb ya dandana mai azaba amma komin zuciyarshi bazai iya tozartaa shi anan wajen ba,ya sani Allah bayason mai yawan fushi,kuma yana yin fushi da duk wani mutum mai tozarta dan uwansa mutum,its too risky nd dangerous yayi wasa da mutuncin saheeb anan wajen a idon manya, yasan in yay mada haka ya rugaza ma saheeb duniyansa ne gabaki daya but definately yasan zai dau fansa akanshi ko akan tsafeshi daya sa akayi.

Yana zaune shikadanshi a seat dinshi karfe 8 aka fara gudanar da taro by 8.30 lokcin kowa ya hallara.

Can Saiga kiran prof ya shigo wayarsa bai dauka awajen ba yay xcusing kanshi zuwa waje,saheeb yana ganin hakan yanayinsa ya sauya izuwa na farinciki atake.

Duk ya dauka giya taheer zaije ya dauko dan yaga yanayin fitarsan a dan gaggauce kaman da akwai matsala. Haka kawai saheeb ya bige da murmushi yanajin wani sabuwar dadi na mamayeshi.

Taheer yana fitowa ya tarar da mum dinshi a tsaye yace momy lpya?
Tace son i need to go,innono ne ta kirani tace yanzun nan inje tsohon gidanmu na sameta”..she have something important to tell me about ur wife’s parents..kirjinshi take ya buga yace “how important isit amma ai iyayenta basa raye ko?..

Prof tace eh..shiyasa nakeso inji komeye ne inkanaso momy sai tazauna dakai anan ni sai in wuce kadunan yanzu ,”Yace no no momy ku zauna i wll take excuse we ll go togther ko acikin daren nan ne.
…yana fadin hakan bai jira me zatace ba ya koma ciki.

Dede lokacin anata kiran sunan saheeb kan stage akn yazo ya amshi honour dinsa na jiya dabai karba ba taheer ya shigo, just like dat aka neme saheeb aka rasa akan seat dinshi ashe ya fitane yaje wine bar din hotel din yana neman giya a haukace,sanda aka bashi giyan yasha yasha ya cire necktie dinsa ya watsar yay zanzaro da jacket dinsa ya balle buturan rigarsa,yana ta kwangwadar giyar yana tafiya yana layi, can da taher ya same ganawa da ogansu yana neman permision barin wajen sai ga saheeb ya bullo ta kofar waje da kwalban giya a hannunshi.

Yuuuuuu idanun mutane yay kanshi,a buge yake magana cikin ihu yana cewa am here am here for my…myyyyyy
For myyyyy…for myyy honours…yana fadin hakan ya tuntsire da wata mahaukaciyar dariya.

Atake securities sukaje suka rirrikeshi yanata kkrin yin kokawa dasu,ana rikesa yana kufcewa yan dura musu ashariya.

Tsaye ogoginsu sukayi harda masu daure masa gindin,da corrupt officials da suke taimaka masa sukecin kudin ubanshi dan a basa matsayi, kowa ya mike tsaye in shock ana kallon draman da saheeb yakeyi.

Kafin faruwar haka,razia tana farfadowa daga suma,saiga wasime,haka ta dinga birgima akasa ta dinga rokon wasime ya Allah ya Annabi akan ta sassauta mata zafin wutar nan dayakecin jikinta.

Sanda Wasime ta zazzageta ta wahal da ita sosai snn tace mata intana son haka saita maida muguntan da suka shirya akan mijinta ya koma kan saurayinta saheeb inba haka ba wallhy bata ma soma jin azaba a hannunta ba tukuna.

Saboda tsananin radadi da razy take ciki acikin sauki ta yarda ta kwallawa saheeb kira a madubi bisa ga umarnin wasime razia ta masa kiranyen tsafi ta umarce shi dayasha giya ya zubda makanshi mutunci fiye da yadda ya kulla sharrin akan taheer.

Aikuwa tana fadin hakan,komi ya faru saheeb yaji kamar an tsakureshi shine yaje ya nemo giyan a duk inda yake yasha ya soma aikata abinda razia ta umarceshi dayayi.

Nan da nan taro ya rikice securities suka rike saheeb da har an dauka tabon hankli ne ya kamasa.

Amma Suna hade ido da taheer aka ga saheeb ya birkice Yana maganganu da gaba da matsanancin fushi yana cewa saina toxarta ka saina tsafeka kasha giya ka ci mutuncin kanka abainar jama’a..akace maka zaka yi nasara akaina ne? Ni ni ni saheeb na fika gata na fika kudi,waye ubanka ubanka talakan banza wahalalle ma,kai taheer baka isa ka shamin gabana ba.

Zan kwace matarka, zan kwana da ita kuma zan kulla maka sharrin da harka mutu bazaka manta ba,yana ta ihu yana cewa haushinka nakeji,ka karbe komi daya dace ya zamto nawa nine na dace da matsayinka,nine na dace da matarka wllhy saina kashe ka na amshe abuna,..saika sha giya kabi mata,tsafi na ba karya bace,..arazane mutane ke kallon bakin saheeb daya ambace tsafi, masu dauka a waya suna dauka jounalist da sauran yan tada zanne tsaye take suka daddauki videon saheeb aka soma yamadidi dashi a social media.

Nan da nan superiors din sojoji suka saka aka kamashi aka kulleshi a gurdroom ya kwana ana cin ubanshi da duka a hannun sojoji masu jan hula.

Take case din ya dawo wani babba sabida abubuwan da saheeb ya furta akan taheer,nan da nan aka fara shirya case wanda za’ayi dashi a gaban kotu,marmaza munafukai acikin su suka kira waya suka sanar da babanshi faruwar komi, washe gari sassafe aka zo aka dauke saheeb da cewar ai ba a sharia da wanda baya cikin hayyacinshi aka wuce da saheeb kaduna aka boyeshi a gidansu yana karban immidiete treatment.

Kafin nan razia ta gama cikawa wasime burikanta da niyyar zata sassauta mata zafin datakeji,
videon saheeb yana fara bazuwa online wasime ta kalla tay murmushi,dan tsabar walakanci ta juya tace ma razia ita ba haka tace ba,tana mata dariya mai kulawar tace” ni dama ba dagaske nake ba bawani warkan dake da zanyi ,dan haka na fasa yafe maki jibari sai gobe inna huce zan gani ko zan iya warkan da ke.

Awaje a backyard ta bar razia tana kuka haka tay baccin azaba ranan saida ta gwammaci mutuwarta dan azaban datakeji ajikinta.

Wasime ta kwanta duk ta kasa samun bacci wani bangare na zuciyarta yana cewa da bata rama mugunta da mugunta ba amma wani bangaren yaki saduda tana ganin rainin wayo da cin zarafin da suka mata yayi yawa musamman inta tuno da zama da ita da razia tay suna sharing miji alhalin bata aure mijinta ba,da giya da suka sa mijinta ya dandana a rayuwarsa sai taji sam bazata iya saukowa daga dokin zuciya ba.

Acan kuma hanklin taher ya tashi sosai game da abunda ya faru,mutane suka dada azzzala abun sukakai social media anata yawo da sunan saheeb ana fadar mugayen dabiunsa.

Abun bai wani masa dadi ba shiyasa baiko kula yan jarida da manema labari ba,Prof da momyn kam dadi sukaji da Allah yasaka kaikayi ya koma kan mashekiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button