FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da taimakon Allah ana dan daddane ta harta samu ta dan nitsu tana amsa ta’aziyar mutane dakanta kwana biyu gidan harya dan samu sarari

A rana na uku bayan anyi addua an watse taheer ne ya fito sanye da Ash colour jallabiya ya rako wasu abokan babanshi da sukazo gaisuwar suka kawo musu breakdown na list din kudin da alhj qasemu yake bibbin wasunsu bashi,tare da kudin biyan sukazo sai suka damka mishi a hannu sukace koda zaiyi amfani dashi wajen biyan wasu basukan da ake binshi wanda basu sani ba,altho taheer ya bincika sosai amma bai samu wasu wanda suke bin mahaifinshi bashi daya wuce mutane biyu ba,kuma suma atake ya cire kudi ya biyasu hakkinsu.

Har bakin hanya ya raka abokan mahaifinsa na kwarai wanda ayayin da suke takawa atare dashi suke dada bashi karfin gwiwar cigaba da rayuwarsa.

Ata daya bangaren titin daya shigo anguwarsu ta hannun hagu kuwa wata hadaddiyar mercedez benz ce mai zafi ta shigo adede kofar gidansu taheer tay parking daidaikun mutanen anguwar dake makale a bakin gate din gidan kaf dinsu suka zuba ma motar ido suna jiran suga wanda zai sako aciki,kusan kowa idonshi nakan motar ganin wanda yake cikin ya dau lokaci sosai kafin nan ya bude motar yasauko.

Saukowa yay acikin yanayin kasaita da aji Suturarsa mai tsananin tsada tana haskawa wal wal tana sheki, yadin jikinshi fara kall ce yolo yolo ya kafa hula mai tsananin tsada shima..

agefen sa kuma wani hadadden saurayine wanda suka jeru dashi suna takunsu cikin kasaitaccen tafiya wanda mafi akasari an sanshi É—ashi.

Idanuwan saheeb ne sakale acikin wani katoton bakin gilashi dayake dan batar da kamanninshi tare da abokinshi khalid big boy suka shiga gidan kai tsaye batare da sun gaisa da kowa awaje ba.

Sallama sukayi a kofar falon lokcin daidaikun matane aciki wanda basu fi biyar ba,suna ganin shigowar su wasu suka dan ja jikinsu daga wajen aka bari daga Prof sai innono sai yar uwan prof datazo mata jaje tun daga kogi state…

Da sakin fuska prof ta tarbe saheeb tana masa barka da zuwa

Ayayinda shida abokinsa suka durkusa har kasa
Suna mika mata ta’aziya suna miÆ™a ma anono jajen itama…

prof dake haryau bata san basa tareda taheer ba sai tambayarsa takeyi ina ya shiga kwana biyu, cikin waskewa saheeb yake cemata ai baya kasar ne shiyasa bata ganinsa Shima sai jiya ya shigo nigerian agurguje shine yakejin labarin rasuwar shine yay shifting flight dinsa nayau zuwa yamma yace bari yazo dai ya musu ta’aziya don in yakoma india da wuyane ya kara dawowa nigeria hala harse ya hada karatunsa.

Albarka ta dinga saka masa tana masa fatan alheri,Anono ma tana tayata mika masa godiya
“prof tace masa ayya ai yanzun nan kuwa taher ya fice da Abokanan mahaifinsa kozaka dan jirashi ya dawo..

Acikin hanzari Yace mata a’a sauri nakey amma zan nemeshi ata waje.

A dar dar yake duk hanklinshi baiya jikinshi,dama shi sabida ya ga wasime kawai yazo gidan dan sosai yay kewarta yana riƙe da ita acikin zciyanshi haryau baicire burin samunta a matsayin matarsa ba.

Gashi babu halin ya tambaya prof ko anono where abouts dinta baisan tayaya ma zai fara saka maganan ba

Wasime na can daki tana tare da bilti datazo tayi musu kwana biyu.

Basu tashi saukowa ba harsaida saheeb da abkinshi suka gaji da tsammanin ganinta suka fice agidan, har saida sukakai bakin gate tukuna ta sauko tare da bilti,lkcin ma sauri sauri su saheeb din sukeyi dan kar su gamu da taheer ahanya, dama da ɗan shirinsa yazo kawai domin yaga wasimé itama taganshi snn ya tafi abunsa.

Shi baizo da niyyar yin fada ba,dan yasan daga yanzu baifi masa nan da wasu yan tsirarrun shekaru ya gama medical schl dinshi ya dawo ba,aransa yana da wasu shiryayyun wasan daya keso ya buga akan taheer naganin ya kwato zucyar wasime izuwa garesa amma ya barine saiya dawo nigeria ne mai gaba daya.

Suna shigowa falon gaban wasime ya fadi jin prof tanace ma bilti Saheeb ne fa yazo…

Murmushi bilti tay tana cewa ayya aidana sani dana zo mungaisa na dade kuwa bangan shi ba
Tace Amma sun hadu da taheer kuwa?prof tace eh to yace zasu hadu ata waje,Daga haka suka bar maganan,bilti tay wucerta kitchen wasime tabita cikin hanzari da mamaki ayanayin ta tsaya snn tace bilti wai dagske yaa saheeb ne yazo?..bilti tace eh wai shine yazo Gashi harya wuce bamu samu ganinsa ba.

Ahnkli Tace eh walh bilti nima na fa dade banganshi ba,hmmm shine ko yadan tsaya in gaishe shi,halama harya manta dani,nifa tun ranar da yazo sukayi fada da yaya ko zuwa gidan nan banga ya karayi ba,Ko basu shirya da yaya bane oho?… Cikin kyabe baki bilti tace ..toh hala sun shiryane shiyasa yazo din wata rana ai zai sake zuwa sai agaisa…

Wasimé tana shirin budan baki,bilti tay saurin katseta..tana cewa;

“ke dai wasime kiyi shiru ki kiyaye bakinki da maganan saheeb din nan,Kibari har sai inshi taheer din da kansa ne ya ce miki kije ku gaisa snn sai ku gaisa,wancan karon ma aikinsan ata dalilinki ne suka samu tsabani,tunda yau yazo kuma bainemi ya gaisa dake ba kema saiki shiga hanklinki ki kama kanki dashi,.yanzu ke ba yarinya bace kuma kinsan kinada aure saiki kiyaye duk wani abunda zai hadaki da taheer ai kinsan halinshi basai na gaya miki ba.l

Bakinta ta turo gaba tace kai bilti nifa cewa kawai nay na jima bangansa ba
Yoni dama mezan masa kawai dan gaisawar da zamuyi?yaya saheeb fa mutunin kirki ne shine ya sissiyamin su salame na kintuna?dariya kadan bilti tay tace “shashaha”
kewai haryau bazaki rabuda maganan su salamen nan bako?
Cikin takune fuska tace ai bazan taÉ“a mantawa da su ba.mhmm Ai yaya ko?wancan lokacin baya da kirki ji nayi kamar na cijeshi daya kashemun su salame..bilti tay murmushi tace ai sai ki cije shi a yanzunma ai is not too late.”Tana dan dariya kasa kasa tace a’a yanzu aiyana da kirki sosai bazan iya masa komiba..nasan da yanzu ne ai da bazai kashemin salame ba aiyana min kirki kuma bazai sanayi kuka ba,..bilti tace hmm uhmm eh kam yanada kirki bazai kashe su ba saidai ya zamo baban su kuma,ince dai sunan yarku ta fari salame ce dan naga duk kinfi sonta acikin sauran yayankin

tace eh ai shima yasan dolene asama babyna suna salame”

..kyabe baki bilti tay cikin murmushi tace toh Allah ya kawo baby salame lapiya Allah ya nuna ma ciki da goyo
…atare suka danyi dariya wasime ta saukar da kanta can can kasa tana jin kunyar maganan duk dama bawani ganewa tay can can ba.”

Tunda akayi rasuwan nan prof bata iya aikin komi innono ke yawan saka wasime tana zuwa kitchen tana taya bilti aikin gida tunda ita surkuwarn gidan.

A kullum su biyunsu suke abinci safe da rana harda dare bilti tay mamakin yadda taga wasime ta iya abubuwa bakamar da can ba.

Ata fannin taheer kuwa baisamu dawowa akan lokaci ba sabida mutane daidaiku da sukan tsareshi akan hanya su miÆ™a masa nasu ta’aziyar.

Hakan yasa yay latti bai iso ya tarar da su saheeb a kofar gidan ba,suna barin wajen sai gashi ya doso, samu yay babu kowa akofar gidansun sai daidaiku yan anguwa.

Shigowarsa gidan bai wani dade ba mahaifiyar sa take sanar masa da zuwan su saheeb din,bai dauki hakan abakin komi ba dan dama mutuwa ta wuce wasa,koda ace hakan akan saheeb ya kasance shima da haka zaiyi,shiru yay baice komi ba ya wuce dakinsa ya kwanta dan haryau baijin dadin jikinshi,dan sosai mutuwar mahaifinshin ta jijjigashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button