FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai can dayaga tay shiru snn ya juyo cikin sanyin murya yace hey dama inason nay magana dake.

Da kyar ta dago ta kalleshi gaba ki daya idanunta ya tara ruwan hawaye sabida soma dago zancen datay acikin bayanansa daya Æ™are yanzu,yi yy kamar baiga hakan ba ya riko tender palms dinsa zuwa nashi ya rike snn yace”..cuty na jibi fa zan tafi..tana kallonsa batace komi ba ya kuma cewa”ina sone ki kwantar da hanklinki kijirani anan harnaje na dawo insha Allah na miki alkwari zan dawo din,hannunta ta kwace anashi da sauri kamar zata sakar masa kuka tace ina ne zaka tafi..yaa nima zan bika dan Allah..yace shushhh inkika bini makarantar ki fa?bazakiy karatu bane kingirma fa..snn kuma anan ga su mumy agidan nan zasuna kulawa dake inmunje Can kuma waye zaina kulawa dake,am going to study,am going to wrk.. kinga can ba kamar nan bane akwai bambamci mai yawa kulawa dake acan zaimin wuya sosai..hawayen dake cikke a idanunta ne suka tsilalo cikin muryan kuka tace nifa bangane ba..wai inka tafin bazaka dawo bane…ni gaskiya saina bika..ajiyar zuciya ya sauke ganin harta fara kuka sosai jikinshi a sanyaye ya sulalo kasa gabanta yace”i swear inda zan iya da zantafi dake, nima bana son nabarki anan nikuma ina cahn,but u have to understand me wann abunda zanjeyi din sabida rayuwarmu ta gaba ne dani dake da iyayen mu..ya tallafo fuskarta suna kallon junaa marairace yace “ko bakiso muyi rayuwa mai kyau ne?Baki son mu koma sabon gidanmu mubiyun mu kullum kina kallona nikadai?Tana tare hawayenta tace inason hkan..dada riko hannunta yay yace then u have to blieve in me,ki kwantar da hanklin ki koda bana kusa dake kisaka aranki zan dawo miki wata rana kinji?
“..kukanta na dada tahowa tace..ina dai bazaka dade ba ko?shiru yy yanata kallon ta dan baison yay mata karya.

Tashi tsaye yay snn ya dagata cak ya dorata akan cinyarsa tare da rangwafowa da fusknsa kasa kasa izuwa nata fuskar yana dubanta
Cikin muryan lallashi yace”cuty zan dan dade
Mana,Amma hakan ba yana nufin bazan dawo bane.Nide abunda nakeso shine ki kwantar da hanklinki ki kuma kulamin da kanki sosai.
Ai Kinsan duk abunda banaso ai bazakina yi bako?kanta ta gyada mishi ahankli jin krijinta kamar zai fashe sabida fargaba..yace good ok..yanzu kin amince naje nay kratun ke zakiy hkri kijirani?muryanta na rawa tace eh amma nidai ka dawo da wuri..
hannunta ya kama acikin nashi yana murzawa yace ok toh naji..

Haka suka kasance a wajen sun jima suna ta tattaunawa haryaci nasaran kwato mind dinta izuwa manufarsa sosai.

Duk dama ta kasance karamar yarinya yasan dolene tanada hakkinta akanshi,duba da hakan ne yasa ya lallabeta sosai harsaida ta fahimce sosai ta kuma amince.

Wajajen karfe daya saura suka yi alwala yajasu sukayi sallan nafila guda biyu,tun bayan gamawar su basu tashi awajen ba yana rungume da ita ajikinshi suna aduoin su tare ahaka har bacci yay awon gaba da ita.

Wshe gari sassafe ya tashe ta da mayyar kisss asaman goshinta,ta bude idanunta ganin haryay alwaln sa zai wuce masallaci.suna hade ido ya sakar mata murmushi
Yace tashi kiyi sallah barinje masallaci sai kije ki shirya schl kuma ko?
Cikin lumshe ido da budewa ta gyada masa kai.

Bayan ta kammala kominta anan ta gyara mishi dakin snn ta wuce nasu dakin ta samu anono harta idar da nata sallahn tana zaune akan
Darduma tana lazimi.

Gaisawa sukayi tana ta binta da ido batace mata komi ba,harta shiga wanka ta fito ta zauna tana shiryawa.

Ata fannin taheer kuwa koda ya idar da sallahn sa bai wani jima ba ya dawo gidan ya nufi part din maman shi ya sameta kwance akan gado zama yay agefen ta suka gaisa snn suka soma maganan su ta bankwana,dauriya kawai takeyi amma a kullum ji take kamar tace masa karyaje koina ya zauna da ita.

Ya dade tare da ita yana mata dukkan wani abunda takeso tare da mata alkwari akan abubuwan da suka tsara na yadda zasuna gudanar da rayuwarsu nan gaba.

Har wajen karfe takwas da rabi suna tare snn suka rabu yaje dakinshi yay wanka ya shirya snn ya dawo falon ya gaida innono suka zauna cin abinci,daga nan ya wuce da wasime makarnta,
after like 2hrs yazo ya dauketa sukaje wani wajen da bata gane wajen ba aka dauka mata hoto d sauransu snn ya dawo ya ajeta.

Daga nan har dare basu samu sun kara yin wani magana mai tsawo ba
Saida ya kammala hada mata komi nata dazai bar mata snn ya dawo yana dakinsa yana karasa kimtsa kayanshi
Dan flight dinshi na karfe takwas ne..

Tunda asubahin yau sukayi ban kwana da mahaifyarsa,wasime tana bacci ta tsinkayo muryansa da anono duk ta rude tana ganin kamar shima inya tafi bazai dawo ba..gashi yanzu ji take kamar shikadaine hasken idaniyarta dan babu miji babu É—a,shikadai ne ya rage jininta da zatana kalla tanajin nitsuwa.

Adua babu kalar wanda baishataba,musammn ma daya debo duk wani kayan bukatar wasime ya damka mata,school pocket moneynta 100
thousand ya bayar in raw cash da wanda ya saka mata a sabon acct dinta daya bude mata jiya domin biyan bukatunta nayau da kullum.

Wasime tunda tay sallah ta wuce dakinshi tana dan tayashi shiryawa
Tausayinta ya dingaji aransa don yasan baxata taba fahintar abun ba sai taga anja lokaci an dade bai dawo ba.ita ta tayashi shiryawan sa tsaf bayan suka rungume
Juna sun dade ahaka saida duk qamshin dake jikinsa ya koma nata.

Yau a tsattsaye ma sukayi breakfast a gidan
Snn suka fita su hudunsu a mota suka rakashi har airpot by 7:40 suka isa.

Dayazo zai tafi dukansu idanunsu saida yay ja sabida kuka daga prof har anono suna masa fatar samun nasara araunataccen yanayi kowa yana tuno da mahaifinsa wanda sunsan dayana raye da dashi za’a zo ayi masa bankwana.

wasime tana dan dauriya bata wani karaya sosai ba,harsaida ya gama komi zai tafi snn ta somajin kamar da ranta za’a rabata.

Babu yadda anono batay akan ta sake masa hannu ya tafi ba amma haka firrr taki tafara sabon kuka,prof kam tuni tabarsu ta koma mota tana kukan tunoda da mijinta wanda mutuwar sa ya dawo mata kamar fresh a memorynta yanzu,sanda yay aikin rarrashin wasime sosai lokcin hr ankammala shiga jirgin kusan shikadai ne bai karaso ba can snn ta hakura ta sakeshi…ajikin glass din no go area ta mannu tana ta kallonshi yana tafiya gabaki daya idanunta sunyi jaaa tanajin kamar ta bishi da gudu su tafi tare.

Tafi minti talatin a tsaye manne da glass din wajen har jirginsu ya tashi bata iya motsawa ba..anono ne ta jawo hannunta da karfi suka koma gida,ranar wuni tay tana shure shure cikin kuka.

Kwana biyu kowanne acikinsu yana jimamin rashin sa a gidan,daya hadu ma wasime da ciwon al’ada bakarmin zazzabi ta rinkayi ba.

Daga nan kuma sai abun yaso yabi jikinta,yau lpya gobe ba lpya ba,ta cusa tunanin taheer sosai acikin ranta bana wasa ba.da wasa da wasa har abun ya soma affecting dinta,bata samun nitsattsen bacci,hakama abinci saidai ta tattaba sama sama daga ta tunoshi ta dinga kuka kenan tanajin tanason taje wajenshi dama can kuma gata da iya rike abu acikin ranta,anono tay lallashi tay fada harta gaji..inhar kaga ta nitsu to agabam mahaifyarsa ne..ata dalilin haka karatun ta ma yafara komawa baya baya
A daddafe ta kammala wnn term din bata gane kanta ba.Saidai aka dan dauko hutu snn anono ta som ficewa ayyukan gwagwayanta data saba
Prof ce agidan tare da ita
Komi zatay takan jawota ciki suna yi tare har hakan ya soma debe mata lokcin yawan tunani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button