FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hmm kawai Bilti taja, toh ya isa haka wasime surutun nan naki yay yawa,maida kayayyakin ki kimtsa wajen in taheer yazo kya nunasa masa sai Kice masa saheeb ne ya siya miki..cikin gwalo idanunta waje tace TAB nikuma sai in gayamai!!
a’a kam,nide wallh bazan je wajenshi ba,kedai kije..ai shi masifa kawai zaimin.

Bilti tace “Masifan me zai miki?ai inkinga taheer yay miki masifa to kece bakiyi dadai ba

Dan dakatawa tay da abunda takeyi snn ta kalli bilti cike da son ta fahimce ta”Amma bilti, ni mena taÉ“a yi masa yakejin haushi na kullum?yo mesa halinsa ba irinna yaa saheeb ba ne? shifa ko dariya bai taÉ“a min ba barema ya siyamin dan sweet ko babyn robber..

Hmm kawai bilti tace snn ta sauke boyayyar ajiyar zuciya cikin shashantar da zancen tace “wasime ina fatan dai bake kika roke saheeb ya siyamiki kayan nan bako?

Wani Dafe kirjinta tayi
Cikin zaro idanu waje
“Tace Ni?..wallahi tallahi wabillahillazi ban rokesa ba,shine fa yakaini wajen waidan nace mishi ya dawo dani gida shine mukaje wani babban shago ya sissiyamin wayannan.
Tana dasa aya bilti tace
“Toh nide ina gargadin ki da ki kama kanki Wasime banda roko banda kuma kwadayi,Kai daga yauma inya kara cewa zai siya miki abu ko zai baki kudi karki amsa kice kin gode kawai,inya takura ne saiki karba shima bavkoda yaushe ba..kuma ki tabbata kin kawo gida kin nuna min kowa taheer
Idan ba hakaba duk abunda ya biyo baya ke kadanki zakiji dashi.
Kwadayi ba abunyi bane wasime,kwadayi da son abun duniya yana saurin jefa mutum halaka koda kuwa shi mai imani ne.
Kiyi hankli da rayuwa karki jefa kanki a tsabgar da bazaki iya ficewa ba.
Karkiga waike yarince nitsuwa da sanin yakamata shine kadai girman ba yawan shekaru ba,yakamata kisani ke marainiyar Allah ce wasime kiji tsoron Allah mahaliccin ki kiyaye dorawa zuciyanki kwadayin abun hannun wani..

Wani Shiru wasimen tayi cikin yanayin nitsuwa tanajin abunda din biltin take cewa dan bada wasa taga tanayi mata maganan ba,sosai bilti ta gargade ta ta kuma ja mata kunne sosai musmn akan ƙarban abun duniya a hannun mutane musmmn ma shi saheeb.

Atake Jikin wasime yay sanyi har bilti ta gama maganganunta ta fita bata dago kanta dake kallon Æ™asa ba..ajiyar zcya kawai ta sauÆ™e zcyarta cike da fargaba ta mike tsaye ta cire kayan jikinta snn ta shiga bathrum tay wanka tare da yin alwala,sharp sharp ta idar da sallahnta wanda bawai ta gama iya shi bane,yau kam ma kwata kwata zcyarta da mind dinta gaba daya sun raja’a ne akan kayan wasa.

Tana idarwa ta kimtsa dakin tsaf, snn ta kwaso su teddies da barbie dolls dn ta jerasu akasa daganan kuma ta tsunduma wasan baby bataji bata gani.

A fannin saheeb kuwa fitarsa a gidan ya same su tolu da malam musa awaje sun kasa sun tsare a bakin motarsa suna jiran fitowarsa, haka ya ciro sabbin kudade ya rarraba masu goron sallah kowa yana washe baki, a bakinsu yakejin labarin cewa Taheer yy tafya baya gari,Perfect oppurtunty for him ya gayyace wasime zuwa asalin gidan iyayen sa domin suganta cos in two days time za’a ayi big birthday party blast ma kanwarsa anisa duk dama abun na gidane kawai so shiga wajen sai wane da wane sabida a cikin family house dinsu za’ayi.

Burinsa ayanzu baifi yakai wasime wajen mahaifyarsa ba kodama zasu soma sabawa da junansu, ta inda xata nan gaba zai iya dogara da cewa mahaifyar tasa zata taimaka masa wajen yaƙin kwato ragamar kulawa da rayuwar wasime daga wajen familynta, danso yake ta girma tasan cewa shi yay mata komi na rayuwarta kafin suyi aure.

Mahaifyarsa hajiya mufidat Garba bakare babban jamiar kare hakkin dan adam ce,snn ta karance fannin lauyanci tana da doctorate degree dinta.
Tana kuma bada gudumawa mai matukar
Muhimmanci wajen taimakawa marayu da marasa galihu (humanatarian)a reshen ƙasar amurka.

Washe gari da safe wasime tana farkawa a bacci ta soma lalubar ababen wasanta sanda tay wasa iya isarta snn ta tashi tay sallah
Ahakan ma Saida bilti ta tsawatar mata snn ta aje taje tayi sallahn a nitse,kayan datay fitsarin dasu ma yau kasa wankesu tay ta dukunkuna su kawai ta aje a bayan gida,yau hatta abinci shareshi tayi koda bilti ta tursasa mata a gaggauce taci dan kadan snn ta koma kan ababen wasanta ranan gaba daya bilti bata gane kan wasimé ba.

Washe gari da safe ma hakan abun ya kasance saidai sukayi fada sosai da bilti snn ta nitsu tay ababen dake gabanta wasan sosai ya shige cikin ranta, Duk abun duniya ya dame zucyar bilti ,at around 12am lkcin bilti ta kammala dukkan wani ayyukanta ta fito kenan tana zaune a falo akan kujera riƙe da remote din tv a hannunta tana neman tashar arewa tanata famar scrolling har tazo ta wuce kan tashar bata lura ba saboda harga Allah babu wani cikakken nitsuwa atattare da ita,tunanin rayuwar wasime tasaka agabanta tun jiya,da shi ta kwana dashi ta kuma farka,kuma haryanzu tana kai bata fasa ba.

Tunani kashi biyu ke wanzuwa a kwakwalnta har yanzu dai itama hanklinta bai wani kwanta sosai akan tarayyar wasimé da saheeb ba,koda ma ace babu wani cutarwa acikin tarayyar nasu, amma dai tasan dolene salonshi na kashe mata kudi da bata ababen duniya yaxo ya gurbata mata rayuwarta na nan gaba.

Takanyi duba da yanayib bambaci dake tsakanin su da saheeb,shifa dan gidan masu shine masu fada aji..anan kuma su basu mallaki arzikin komi ba face iya wanda Allah ya basu na rufin asiri.

Toh ta ina kenan zasu iya da wasime nan gaba inhar ta kyaleta ta saba da kalar rayuwar da batata ba?yarinya marainiyar Allah kuma ga igiyar Auren wani akanta.
Kamata yay wasime ta zamto killataciya tun yanzu,ita kanta tarasa dalilin dayasa taheer yaki cewa komi akan tarayyar wasime da saheeb aganinta sam sam bai dace ba, duba da yadda sabo na yau da kullum daa kuma shaƙuwa da juna yakeson ya soma yin tasiri a zukatansu.

Bawai iya nan ne ciwon nata ba,hatta sauyawar halayyar wasime yana daya daga cikin abunda yake tada mata hankli.
Lokacin da anono ta kawo wasimé ko kara kasaka abakinta bazata tauna ba,amma yanzu gabaki daya ta sauya ta dawo wata marar da’a gashi bata son girmama na gaba da ita.

Tasan hala dan bata taba haihuwa ba batasan zafin É—a ba amma rayuwar taheer da na wasime tamkar wani babban responsibilty ne akanta tunda amana iyayensa suka damka mata,bazata ce tayi nasarar rayuwarta ba inhar ta kyale tarbiyan dayan su ya gurbace.

aynzu kam taheer ya dan girma,tasan ba lallaine ya bata ciwon kai mai yawa ba,duk dama yakan dan taba yarintar,amma aynzu batashi take ba yazame mata dole tasaka ido akan rayuwar wasime,dole ne tasan yadda zatayi ta saita tarbiyanta dan kwata kwata wnn sabbin dabiu da halayyar nata sam basu dace da ita ba.

Tana cikin wannan tunanin wayarta ya soma ringing saheeb tagani akan screen da kamar bazata dauka ba can dai ta hakra ta dauÆ™a gameda kara wayar a kunne..babu yabo ba fallasa tace “salamu alaikum saheeb? As usual da fararsa ya amsa suka gaisa..kai tsaye ya tambayeta ko zai iya zuwa ya dauÆ™i wasime izuwa birthday partyn sistersa yau..”tace a’a saheeb kasan dai wasime bata fita acikin gidan nan saida umarnin taheer kuma kaga taher din bayanan kabari mana sai wani lokaci inyaso by then taheer ya dawo amma ynzu kam baya gari.
..,yace eh nasan da hakan shiyasa ma nake neman alfarman ta wajenki dan Allah bilti,namiki alkwarin baxata jima ba zamu dawo,taheer dont even need to knw this, ana yanka cake akayi dan hotona shikenan saina dawo da ita,it wunt take dat long…please kitemaka min . ya karashe maganan cikin magiya..dan shiru bilti tay sabida rashin sanin hukuncin da zata yanke
Wasime ne ta dosu falon
Goye da white teddy bear a gadon bayanta tana tafiya tana wasa da wani abu mai balls balls aciki.
Bilti bilti doramin abuna ya tsinke…
Saheeb yana tsinkayo muryanta yace
‘Is that beauty?bilti bata amsa ba,yace bilti dan Allah hadani da ita..
Mika mata wayar tayi kiyi magana saheeb ne,”da uban zumudi ta amsa taa kara a kunnenta tace “Alo?yeeeeyyy yaa saheeb…dariya yay beauty beauty..beauty na kitayani rokon bilti mana tabari in zo in dauÆ™eki kije kiga mummy na.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button