FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sabbin Halayen malam
Musane kawai matsalar ta ayayinda ya samu wani sabuwar sarar shigowa kitchen gatsau saida kawai ta ga mutum abayanta yana mammatse kafa yana lashe baki,abun na damun bilti bana wasa ba..ta rasa meya manufarsa amma bata kawo wani mummunan abu aranta ba.

Wasime kuwa tunda ta fahimce cewa taheer baya nan ta bude shafin wasan baby babuji babu gani gabaki daya rayuwarta ta sallama akan wasa,safe da rana har da dare wani bin sai bilti ta tsawatar mata ko tace zata kira taheer awaya ta fada mishi kafin take denawa.

Satin taher biyu a abuja tare da iyayensa kafun ya dawo kaduna,shigowar dare yay babu wanda ya sani,kafin yay bacci saida yaje ya leka dakin ya duba lpyarsu,yanata kallon wasime wanda duk kayan wasanta ne a barbaje akasa.

Komawa dakinsa yay da tunanin yadda zai rabata da wannan wasan.
Tunanin sakata a makaranta shiya fado masa aransa for the first time ya somajin hakanne kawai ya dace da ita ayanzu.

Washe gari da sassafe bayan wasime tayi sallah,jira tayi saida bilti ta wuce kitchen snn ta zauna ta cigaba da wasan babynta…

Kwata kwata batasan da cewa taher ya dawo ba.
Angama breakfast bilti ta wuce zata kirawo ta saigashi nan yana saukowa da mamaki anayayinta ta tsaya suka gaisa snn suka karasa cikin dakinsun tare.

Da Sallama suka shigo wasime bata kulaba sabida hanklinta yay nisa akan wasa..”bilti tace ke wasime?jiyowa tayi adan firgice tana hade ido da taheer tayi wuf ta miÆ™e tsaye a daburce ta sulale kasa kamar munafuka ta shiga gaishe sa cikin sanyin murya..

Shiru yy bai amsa taba yana ta kallon kayan wasan yanakuma jin fadan da bilti ta danyi mata akan yadda take nacewa da son wasa.

Kwana biyu baice mata komi ba yay kamar hanklinsa baiya wajen itama bata fasa wasanta ba sabida abun ya balain shiga cikin ranta….
ALHAMDULLAHI FANMILY THANKS FOR YOUR SUPPORTS THROUT DIS JOURNEY
ANAN NAKE KAWO KARSHEN FREE PAGES NA WANNAN LITTAFIN.
LABARIN ZAI CIGABA DA ZUWA MUKU RANAR LARABA…GAMAI BUKATAR JIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN WASIMÉ DA TAHEER DA KUMA SAHEEB YA HANZARTA BIYAN KUDIN KARATUN SA NAIRA 300₦ VIA

0152983148
MOHD SULE SURAYYA GTB
ZAKA IYA TURO DA KATIN WAYA NA MTN TA WANNAN LAYIN 09132352275
SAIKA TURO SHEDAR BIYANKA A 08060712446.

NAGODE MUKU MATUKA AND SPECIAL THANKS TO ALL THOSE WHO PATRONISE ME,I LOVE U ALWYS ND FOREVER !

URS TRULY SURAYYAHMS…..
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR21

Way to school

Ranar jumua da yamma can gabanin magriba wasimé tana zaune tanata wasa har aka kira sallah bataji ba sai wasanta kawai takeyi…taher ya sauko yanata kallonta baice mata uffan ba ya wuce masallaci haryaje ya dawo bayan ishai tana wajen bata tashi ba..

Yana yaye labulen kofar falo ya hangota, motsin takunshi dataji daga bayanta yasaka ta juyowa adan razane suna hade ido cikin sauri tabar abubuwan datakeyi ta mike tsaye sum sum tayi da kanta kasa zata bar wajen,binta da kallo yay baice mata uffan ba harsaida tayi nisa ta soma takawa kan step
Zata nufi daki.Daga bayanta taji sautin muryansa yana cewa kina gamawa kizo kisameni a daki…

Tsayuwar dole tayi dan Bakaramin faduwa gabanta yy dataji yace hakan ba, A sassarfe
Ta juyo ahankli ta kalle shi snn ta amsa shi da toh ta wuce sum sum ciki cikin sauri duk tana tsarge tsoro ya gama cika mata zuciyarta. tana idar da sallah ko cire hijabi batayi ba ta nufo waje tana waige waige.

Wani kauri kaurin kunan wuta ta dingaji ayayin da take saukowa daga matakala,wani irin tsananta bugu kirjinta yay.,kamar ance mata ta daga ido ta duba kayan wasanta aikuwa taga ankwashe su tasss babu ko daya a inda ta bari.

Wani irin bugawa zcyarta yay atake gabanta ya fadi idanunta suka cikka da ruwan hawaye Haka kawai jikinta ya soma bata wani abu Da mugun gudu ta karasa saukowa kasa ta bude kofar waje cikin hanzari ta leka kadan,a can taganshi yana famar É“abbaka wa babynan rubbernta da sauran kayan wasanta wuta….

ragwabewa tayi wajen tanaji kamar an cakkawa zucyarta mashi, rushewa da wani irin tokarriyar kuka tay, da mugun gudu ta koma cikin gidan tana rusa ihu tana kiran sunan bilti a gigice,kusan a raxane bilti ta fito daga wanka batare data shirya ba Hankli tashe take cewa ‘innalillahi Wasime lpya kuwa? wasime meyasameki…

Akasa ta turmusa tana kallon bilti da shagwababben yanayi ta dinga ihu tana birgima tana wulla kafafun ta”wayyo Allah na na higga uku, kayan wasa na, baby na baby na…

Bilti tace ikon Allah wasime toh meya same su?

ACikin kuka Tace “Ba yaa dahiru bane ya konamin kayan wasa na, Wayyo Allah na ni wallahi saiya biyani abuna.Bilti batace mata komi ba.

Wasime ta rungume kanta tana gunjin kuka tana surutai duk ranta a dagule”Yanzu hikenan salamatu ta mutu?(sunan favrite toy dinta kenan salamatu)

tana kukanta tsakani da Allah harda jajjan majina ta cigaba da cewa “wayyo hikenan ni yau naga mutuwar salame..,
yaa dahiru makashine,ya kashemin salame wayyo salame na…na higga uku…”tafadi a kasa ta rike kai cikin yanayin zabura mai ban dariya
Wani tsalle tay ta tumu “..Wayyo Allah na fatima ma tana cikin wutan,hikenan fatu,fatu sa’i yayi, ya Æ™onata wallhi bilti kije ki gani wallhi ya cannata acikin wuta.
…yanzu kodan aminatu bazai barmin ba?. .dazun nan fa nayi ma salma wanka nasaka mata kaya mei hegen kyau… wiii wiiii ta cigaba da kukanta Kamar xata tsaga kanta tana yi tana bori tana cillo kafafuwanta akasa tanaji kamar zata haukace…

Bilti ta tsaya agabanta emotionless duk sai ta rasa mexatayi kwara daya,shin dariya zatayine koko kuka?dan abun wasimen gaba daya ya rikirkita mata hankli…
Kukan nata abun tausayi amma surutayyan nata kuma abun dariya.

Tana cikin fetsa maganganunta caraf taji kamar motsin kofa ta bayanta a rikirkice ta mike tsaye ta hadiye kukan mel tayi shiru kamar ba ita takeyi ba.
Kallon kasa ta dingayi kamar marar gaskiya

Ahankli ya turo kofar dakin ya tsaya daga can bakin kofa yana kallonta,
Ya hade rai yce ihun waye nakeji Haka?

…kafin bilti ta amsa caraf wasimé ta cabe maganan muryanta na rawa rawa tace “

“Ummm ba ihu bane fa. Dama Salame ne da fatiti da amina da salma suka rasu shine nake gaya mata,shine kawai naji tausayinsu, shine kawai na ga kuka yafara xubomin saina farayi..sai gaka nan ka higgo,kasa daurewa tayi ta rushe da wani uban kuka mai ban dariya tanayi tana goge hawayenta ahnkli dan kar yagani,cikin shessheka take cewa “Allah ya jikan su salame…wayyo Allah na hikanan salame ta mutu tabarni…inama zan iya da saina bita lahira…

Ta cigaba da hawaye duk tsoro ya gama rikirkita mata yanayinta is like bata ma san tana furta wayannan maganganun ba.

Bilti mezatayi inbanda dariya,..ta lura bakaramin drama queen bace wasime…she look so funny and serious at same time har wani sharrr tayi takoma kamar
Wata wanda takecikin matsanancin halin makokina gaske.

Dada harde ransa yy yaja tsaki mai tsayi, yi yy kamar ma bai gane me take nufi ba “yace suwaye kuma salame?..
Bilti ta cigaba da dariya ganin wasime ta dora hannu akai sai gunjin makoki takeyi tana jimamin babynan robanta batama ji meyace ba..,bilti tace
“wai kayan wasanta ne tacemin ka konasu awaje…Bai jira ta karasa maganan ba ya dada harde rai yace ohh,da wani matsiyancin harara yabita snn ya zare mata idanunshi yace”ke?bakida hankline will u Comon get out of this place?akan dan wann abunne kike bude wa mutane baki?nace akan wannan shirmen kike cika mana kunne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button