FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

A fannin professor oyiza ma ba a barta abaya ba,ganin kokari da jajaircewan da su inno sukeyi akan surkuwanta yasaka itama taji shaukin bada nata muhimmiyar gudumar ta wajen hada shaharriyar hidiman biki,just to make wasime feel speacial itama taji kamar tay aure kamar yadda ake auro kowacce Æ´a mace.

Gashi yanzu kudi ya zauna musu iya zaunawa arziki kam masha Allah kominsu nata bunkasa harma prof tana neman tay retire tabar aikin gwamnati sabida danta is now earning more than enough to sustain her livng, dan haka nema ta fara shirye shiryen kayatattun biki bidiri wanda za’ayishi a zamanan ce amma ba hidimace wanda zata taro kan jama’a masu yawa ba.

Acikin mutanen ta wanda ta sanar da su iya wanda suke close da itane sosai,sai relations yan uwanta na nesa da kusa da kuma few colleques dinta na wajen aiki.

Innono ce dai ta taro mutanen ta birni da kauye,dan wasu na kusa da itan ma a sashen ta suka tare tun ana saura sati daya hidima ana shirye shiryen bidirin biki.

Tun abu na kamar wasa saida yan uwan prof mata sukazo sukasaka shirye shiryen ya wuce tunanin jama’a abu yana nema ya dawo wani babban hidima dan kuwa bakaramin naira prof take narkawa awajen tsare tsaren hidindimon da za’ayi ba.

Programes kala uku wanda ba’aza somayin su ba sai ana saura kwana uku da zuwan ango nigeria,dan hakama yasa aka buga invitation card tun wuri aka babbawa wanda ake son su hallici wajen taron wanda mafi akasari mata ne,mazajen da aka gayyata basufi a kirga ba yawanci ma abokan mahaifinsa ne da wanda ake mutunci dasu sosai.

Day one na budirin bikin da wankan amarya aka fara tradional bridal wash colour of the moments was red nd gold, akayi decorating cikin gidan aka kawata shi da ado irin na al’adun indiyawa ga tabarman alfarma masu shegen kyau Inda fratenal sisters din prof oyiza su anty safeena da aysha da sister aneesa da zuzu kowa ya dauki nashi sashen hidiman da zai kula dashi.

Ranar wankan amarya anty aneesa ce dakabta ta gayyato tradional beauty nd spa artist dinta tundaga Æ™asar sudan saidai ita irin asalinta yar buzuwa ce din nan, hadin gambizar niger da kuma Æ™asar sudan din,itama da mukrabbanta tazo gidan aka tara mata ana yan raye raye na al’ada akayi ma amarya traditional spa,waxing etc,snn aka mata wankan madara da caramel dilka,da wani irin kwabin skin mask na pormenganete.Bayan an gama wanka har 12 dare aka kai ana mata tsumi da kayan qamshi.

Tun ba aje ko ina ba jikin wasime ya fara fidda wasu irin rikitattun qamshin turaruka tun daga tsakar kanta qamshi hartafin kafafunta qamshi ne mai tsananin dadi yake fitarwa.

Washe gari sassafe haka aka sake taron bridal sitting inda aka tsantsara ma amarya lallen heena ja da baki a hannu da kafafu masu mugun daukar hankli,duk wanda yazo wajen shima saida aka zana masa nasa a hannunsa..

Tun daga rana na biyu manyan mata da antys suka fara ma wasime nasiha da hudubar zaman aure da wani dan karamin Al’adan su da sukeyi kamar budan kai,wanda saida yammacan akayiwa wasime kwalliya ta saka golden chantilly lace dinta mai matching color design na amina muaddi heel cover shoes da purse dinshi,an mata kwalliyarta nude kamar dai yadda take so mai daukar numfashi.taji gwalagwalen nan wuya da hannu bakaramin kyau tayi ba.

Wani babban mayafi mai sharara dogo aka mata rufi dashi duk inda tabi qamshine mai ratsa zuciya yake ragowa awajen,few schl mates dinta data gayyata wanda basufi su uku ba su suka dan tssattsaya mata akayi program din kamar budan kai.

Yan uwan miji bayan sun mammana mata kudi suka kawo mata ruwan kwakwa mai sihirtaccen hadi suka bata ta shanye
Snn aka bude fuskanta a sarari kowa ya kalla.fannin anono ma ba abarsu abaya ba dan sosai mutanenta suka rufa mata baya tay manni iya manni wa amarya.

Washe gari Ranar juma’a ne randa aka saka ranar liyafa,yauma bakaramin kyau wasime tayi ba makeup artist sun tsantsara mata wani nude nd breathtaking kwalliya bakinta na wani irin shining da lipsgloss, ta saka wani tsadadden white lacy flowing weding gown mai cuts nd ruffle neck da dogon hannu,kayan is so decent nd damn classy mayafinshi shima transparent ne har kasa yakeja yana sharar kasa,bayan nan komi na jikinta da akayi pairing silver colour ne.

Can Da yamma aka wuce wajen wata gawutacciyar liyafa da zasuyi acikin wani babban hall inda duk wasu mazajen da prof ta gayyato suka hallara aka ci aka sha aka babba da souviernies wa baki,wasuma dai saiyanzu suke sanin taheer yay aure yana da mata,bakaramin kashe kudi prof tay don tsara hidindimonta ba dan sosai liyafarta ya kayatar kusan kowa awajen na burin samun irinsa kowa na masha Allahu tubarkallah.

despite kudinsu da suke dashi yanzu bai hana wasu daga cikin abokan baban sa da wasu yan uwa da abokan arziki sun tara musu kyautaukan kudi ba babu laifi prof taga tsantsar aminci da kara da kararramawa barinma yanzu da kowa yasani danta ya zamo wani abu arayuwarsa.

Washe gari taheer zai diro nigeria kowa fatan alheri yake musu…

A fannin anono ganin komi da akayi yatafi dadai yasa yan uwa da abokanta na kut da kut sukaga ya dace suyi ma prof wani abu a matsayin su na dangin Amarya.

Daga nan marmaza suka hada kai suka je can gidan inna harira aka har hada kayyaykin tsaraba dake yawancin su girma ya kawo sharp sharp akayi su cincin dublan da su alkaki harda guzirin dakuwa snn suka hada kayan tsaraban uwa da uba aka siyo madaidaicin akwatuna guda biyu masu kyau daya na uwa daya kuma na uba,suka zuzzuba kayansu daidai gwargwado,da tarkacen kuloli,Tray din silver da buta da manyan kofunan silver da kwanon sha da setin samira.Haka suka hada kayan tsarabarsu cif cif waidan su miƙa wasime a mutunce kada yan uwan miji suje surenata.

Tun bayan liyafar wasime tay sallama da kowa ,dik baƙinsu ma suka watse
Agidan yanzu anty safeena ne da anty zuzu da anty anisa suka rage suna tare da prof akan washe gari da sassafe zasu mikawa anono kayan lefe da taheer yay wa matarsa da wanda itama kanta tayi.

Tsadadun Akwatinan wasime designers ne guda goma sha hudu da tangamemen jakar ghana most go shima cikke da tarkacen kaya.

Da safe karfe tara da rabi
Aka hadu duka a babban falon anono lokcin har inna harira da umma shatu dayar aminiyar su, da kuma inna Yengel wanda take yar uwace ga anono ta wajen uba suma har sun kawo kayan tsaraba da jiya suka hada kai akayi.

Mahaifiyar taheer da yan uwanta sai wasu kawayenta guda biyu suka kawo akwatuna sukayi prsenting kayan duniya masha Allah wasu abubuwan ma tsabar kyaunsu da tsadarsu su anono basu taɓa ganin sa ba haka aka sassaka albarka ana tubarkallah.daga bisani suma suka dunguma suka kaima prof duk wani kayan tsarabar da suka tanadar,it was so unxpected for them abun bakaramin yin dadi yayiwa yan uwan professor oyiza ba.

Kowa yaji dadi matuka da dan abunda su anono sukayi,hakan bakaramin tasiri yay wajen kare mutuncin wasime da daga mata daraja wajen dangin mijinta ba.

Kawayen prof tun ana raha har saida akan taɓa yar gulma.Dan kuwa duk wanda yaga yadda aka tafiyar da abubuwa so smoothly nd dilligently sai ya danji ina ma shine acikin wann matsayin

Kafin karfe biyu na rana har kowa ya watse agidan masu tafiya kogi kudin jirgi prof ta biya musu bayan hilimin tsaraba da kayan biki da suka koma dashi gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button