FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ture hannunsa tayi game da fashewa da tsinannen Dariya irinna rainin wayo
Din nan,Baya taja tana hararsa snn ta juya ta kare ma gidansu taher din kallo cikin yanayib gatsine

Gani tay ko gidan P.A din ubanta baikai ba,gidan ubanta kuma ya taka wann gidan nasu sau hamsin a kyau da tsari da komi da komi.Yanzu akan wann tsukukun gidan ne har ake saka wani doka?..

Adaidai lokacin data juyo ta fadi wannan kalman tej ke fitowa daga gidan su tare da wani shirgegen belt din sojoji a hannunsa ya riƙe fuskansa bada wasa ba yana dosuso da no nonsense face dinsa

dama shi kowa ya shedesa da akwaishi da saurin kufula abu kadan ne yake irritating nasa yaji ya tsana abun har abada,kamar yadda ya tsani dabiun zee kamar mutuwarsa..kuma harga Allah baison harkan saheeb da zee amma saheeb sam yakijinshi wai kawai shi ita yake so.

Zee tana kallonsa ta wani ja da baya ta ƙime ta dora hannunta a kugu tana zuba yauqi tana wani gatsine up and down wai ita gata babban yarinya wacce bata shayin kowa.

Saheeb ya dora hannunshi a goshi ransa a mugun dagule yana kallonta ke waimesa bakijene”babe jeki mana..ki shiga cikin mota kawai kutafi

Wani uban harara ta watsa mai a fuska snn tace”haka kawai toh Akan me?kai bari kaji Inkana tsoronsa ni wallhy banaji.Dan haka babu inda zanje..inkaga na barnan to ganin damatace..ta karashe maganan cikin jiji dakai

Riko hannayenta saheeb yay yana kkrin janta cikin lallami yana cewa”baby please now.. Bafa wannan maganan akeyi ynxu ba just do wat i ask u to..

cikin zare masa ido da masifar karfin hali ta fauce hannunta Tace
“nace baxan barnan bako,dokan kirjinshi tahauyi yana matsawa baya baya”..matsoraci kawai!Saheeb kai wawane tufff,banza..jaki kawai!kare..doki!

taheer dake tahowa yanajinsu take idanuwansa suka sauya kala sukayi wani jaaa danji yay kamar washi aka watsa ma wann zagin…

matse lababbansa yycda ƙarfi yau Da kuwa shi ne ta zaga haka da saidai uwarta ta haifo wata mai kamanta amma ba dai ita ba.

Saheeb kam ko ajikinshi yanata kkrin controling nata ita kuwa sai dada hawa takeyi tun abu na cikin fushi sai tamayar da abun ya dawo kamar wani kokawa a tsakanin su,yana tattaro hannunta tana fixgewa,tana zaginshi tana kaimasa duka yana kaucewa.

A daidai wann gabar dukka kawayenta suka sassauko ƙasa kowacce da kalar barazanarta dukkansu su daddame jikinsu da kananan kaya

kallo daya kamasu ya isheka ka fahimci cewa Æ´ayan masu shine ,kuma sakaltattu yan gata,dudu dai bazasu wuce shekaru 17 zuwa 18 ba dan ko zee din datayi girman jiki sosai bata gama cika shekaru sha takwas din a duniya ba,Wanda isowarsu yay daidai da isowar taher wajen”

..wai meyeke faruwa anan ne?daya daga cikinsu ta tambaya tana wani gatsine tana turo kirjinta dayaci uwar acucin dunlop bra gaba

Cike da hade rai taheer ya kallesu.”Cewa nayi kubar kofar gidan nan yanxu yanxun nan koda matsala ne?Taher na bata amsa dukansu matan suka zubamai idanu kowacce da kalar kallon datakemishi

Gabaki daya Farin fatar namiji kabila daban take wajen dauƙe ido,ga taheer agabansu ya hada komi da komi na cikakken namiji, jarumi, kuma kyakkwawa, wanda ko dan sarkin saudiya aka ƙirasa dashi ai zai amsa sunan sabida ya cika kota ina!shi hasken sa ba dau bace tay wani irin pale yellowish colour mai daukar hankli gata tana sheki yana glowing kamar kullum ne ake wankesa da madara

daya daga cikin babes din ta zubawa gefen wuyarsa idanu tana kallon tsantsar freshness da kyaun kalar fatar wajen kamar xata shanyemishi jini…

Daya kuma tsantsar hasken hannayensa da kafafunsa kawai take kalla…

Juyowa saheeb yay yace “guy pls dont do this”
Kabarsu yanzu zasu wuce.

Ransa a É“ace yace
‘right now!

cikin runtse ido Saheeb yace guy waimesa kakemin hakane?nace maka thy r leaving..why me?

Yace”saheeb this Is not my wish but my compulsion”ai nafada ma,banason tarukucen mata musmmn ma irin wayannan..in suna son ganinka sunsan inda zasuje su sameka amma not here infront of my parents house.

Tuni xee baby ta caɓe maganar cikin masifa da nuna izza tana wani hura hancinta cikin zafin zcya

..”aikin banza aikin wofi..Da makaho ya rasa ido ai dole yace ido da wari ana wani jiji da talauci da tsiya?meye wannan?ni fa banga gida anan ba, akan wannan
Dan tsurkun gidan ne har za’a mana iko sai kace gidan gwal..
Toh dakai da gidan naku sai insaka a walakntaku..
Kaji ko taheer?…yatsa ta nunamai cike da bushe idanunta”…Kasanni kuwa..i think ure yet to knw who i am,am the unshakable zee…bana gudu bana ja da baya kuma tsoron kowa…yau inna ga dama saina saka anrushe gidan nan mark my words,sainasa anmaida wannan ragajajjen gidan naku ta dawo toooka…

Bata ƙarasa zancen ba taji saukar wata gangariyar mari wargajaujau akan dandamalin fuskarta

Layi ta soma yi,snn jiri ya debeta zai kwaɓata akasa kawayenta suka rirriketa,suna furta inna lillahi,zee dake riƙe da kanta Bata taɓa sanin cewa dagaske ne ana iya kallon yan wuta suna tsinan wake sabida zafin mari ba saiyau, kuka ta saka mai ƙara hannunta dafe da kuncinta.

kawayenta duk ransu ya É“aci zasuyi magana kenan ya bisu da wata tsawa
“No one is talking to u bitches! Wata ta yarda tay magana anan saina tattaka ta.

A lokaci guda gabaki dayansu suka rife bakinsu suka tsuramai ido..

Babu abunda xee take sai rabza uban kuka jini da majina duk sun wanke mata haɓarta

Saheeb ne yajanye hannunta cikin sauri suka doshi inda motar su yake ya bude ya jefata aciki…wani irin kuka ta kara fashewa da shi
Ta kallesa da jajayen idanunta,acikin fushi mai tsanani tace sakarya kawai!Wallahi saheeb saika ramamin
Ko ni inje in rama dakaina

Juyowa yy ransa a bace
Yace “shut the hell up.
Meya hanaki ramawaa dazu?
Shiru tay tacigaba da rabza kuka kamar andaketa

Taheer Yana huci ya juya ya kalle kawayenta daga can nesa inda suka tsatsaya tsuliyarsu a zage, Bulalansa ya kuma zargewa ya faudeta wa iska tayi kara feewww
“snn ya haÉ—e ransa yace ku kumafa?ubanwa kuke jira anan?ko kuma zakusa a rushe gidan ne in zazzane ku?

Daga wann ta kalle wancan sai wannan ta kalli wancen atare duka sukayi yaƙen fargaba.

Turancin karya kowa tasako saiji kake ana “no..issakay…sai anjima bros!kaga tafiyarmu

Tsaki yaja snn ya koma ƙofar gidansu ya tsaya kikam yana kallonsu har suka tada motar suka tafi.wani fuuu ya wuce cikin gida Ko ajikinshi bai damu ba dan sunsaba indan wannan ne.

Yasan in akayine saheeb yace zaiyi zuciya ya shareshi kwana biyu bazai masa magana ba.
.kada kafadarsa yay irin kodata faru baidamu ba..dakinsa ya nufa ya dauƙi jakar karatunsa snn ya bar gidan,barrack din sojoji ya dosa inda ake musu cikakken medical classes dinsu
,bai dawo ba sai wajajen tara na dare

Samu yay har an kammala dinner,yau bilti tay wani lafiyayyen tuwon eba da miyar egushi da yaji barkwano da dagedagen kifi, dan kadan yaci snn ya koma dakinsa yacigaba da koyan zanensa,dan aranshi so yake yaga yay kkri ya jajirce snn yafi kowa kwarancewa a fannin sanin tsala tsala na gangan jikin dan adam da kuma dukkan wani jijiyoyin da suke cikin kwakwalwa.

Karatunsa na farko dayay acan baya general surgery ya karanta a can makarntr su ta sojoji,shekara hudune kacal,yanzu kuma ya dawo takan area of specialization dinsa which is neurosugeon
Wato likitan cututtukan dake cikin kwakwalwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button