FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

tsaye tay a falon cikin tashin hankli,idonta na lura da time har sai wajen karfe goma saura na dare snn ya shigo,dirin motarsa dataji a waje ya
Sa ta bude windown falon tanata kallonsu.

Da alamn duk agiye suke,
Uniform din islamiyarta ne ajikinta ya riko hannun ta suna tafiyarsu a nitse ahaka har sukayi sallama suka shigo ciki.

Yanayin sallama suka hade ido da maman shi ya hade ransa ya dauke kansa akanta yanamai gaisheta ciki ciki ,a hnkli wasime ta tsuguna cikin sanyin murya tace ina wuni,kallonta kawai prof tay bata amsa ba..

Kallonshi tayi tace
Taheer ina kuka fito haka kuka dade tun safe fa?kuma shine ina kiranka bazaka dauka kacemin bazaku dawo da wuri ba…

Shiru yay mata,muryansa ciki ciki yace mata am sleepy…snn yaja hannun wasime sukayi dakinshi suka barta tsaye awajen da abincinta cikin tsananin damuwa.

Washe gari ma haka ya fito sasafe baiko yaje ya dubata ba,daga masallaci ya je ya siyo ma wasime abincin karyawa dana makarntar ta yazo ya saka mata a schl box dinta ya shirya mata komi.

6:30 wasime ta shirya ta fito,sukaci karo da prof ta kuma gaishe anma still kallonta kawai tay batace mata uffan ba..hakan yasa wasime acikin wani yanayi na tsoro…Taheer yana saukowa haka ya kama hannunta suka fita a gidan yakaita schl yabata abincin da kudin da zata rike a hannu

Yauma bai koma gidan ba ya wuce gararinsa lokacin tashin su wasime yanayi yazo ya dauƙeta suka kara tafiya yawo kome take so haka zai siya mata,shide kawai bazai koma gidan bane bare mamanshi taji dadi

Haka kwana biyu dukansu suka kasance acikin damuwa,
musamman ma maman nashi dataga ya dena gaisheta a mutunce snn ya dena cin abincin ta kuma daga ya fice a gidan baya dawowa wanibin ma bacci ne kawai ke dawowa dashi.
Gashi kullum tareda wasime suke kwana
Haka Sam yaki ya barta tay kyakkwan ganawa da wasime

Ata fannin wasimen ma gabaki daya duniya ta sauya mata ganin maman taheer bata amsa gaisuwarta saidai tay ta kallonta amma most times batace mata cikanki.

Duk dama dai bata nuna mata alaman fushi fushi ba,amma rashin amsa magananta datakeyi bakaramin damunta yakeyi ba.

Shikam ko ajikinshi snn yana lura da damuwar kowaccensu akan lamarin amma dukansu baice musu uffan ba.

Kwana biyu haka rayuwarsu ta cagwalgwle a gidan,ranar wasime ta farka da safe zata dafa mishi taliya dayace mata yanason ci,ta shiga kitchen din kenan sai ga maman nashi ta shigo data tambayeta taji me zata dafa haka ta amshe girkin a hannunta tay masa dakanta ta kawo masa har falo inda yake zaune,duk dama baici ba..amma abun nan ya balain damun zuciyar wasime..Ganin ta nuna damuwarta hakan yasa kwata kwata ya dena sakata tay mishi aikin kome agidan.

Morning to night ko mamanshi tay abinci bazaici ba,haka zaije ya debo na waje yaci snn ya bawa matarsa acikin gidan tana kallo.
Duk saida yasaka abun duniya ya damesu.

Da Abun ya ishe prof ranar da sassafe ta tsare sa a kofar dakinshi tana tuhumarsa akan kincin abincinta dayakeyi,agaban wasime akayi komi suka kara samun wani saɓanin.

Ganin bazata iya da fushin taheer ba kawai saita shirya ta wuce gidansu bilti..

Daidai isowarta ta samu kawu ibrahim yana kan cima bilti mutunci yaba zaginta kamar shiya kawota duniya

Duk dama ya girme ta amma hakan bai hanata saukowa daga motarta izuwa gareshi ba,haka ta wankeshi tass tanamai tuna masa cewa tasan komi, kuma tasan da akwai arzikin bilti dayaci na gadon iyayenta Tace idan har yacigaba da muzguna ma bilti saita makashi a kotu ya biya duk wani hakkin bilti dayaci snn arabasu na har abada,kawu ibrahim bai taɓa tsorata kamar nayau ba,dan ko ba komi yasan prof is an influencial personality koda anje kotu dashi dawuya ne in bata daureshi akan bilti ba.

Prof kuwa Sanda tagama
Masife shi tasss akan bilti snn ta samu waje ta zauna ta kawo karar taheer wajen bilti akan abunda yake mata agidan.

Hakuri bilti ta dinga bata Da kyar ta sauko,washe gari da sassafe saigata tazo gidan,tasha mamaki yau da kawu ibrahim baice mata komi ba ya kyaleta ta tafi.,bata taɓa sanin shine ya cinye mata gadonta ba sai jiya
Da mahaifyar taheer ta tona asirinsa wajen yin masa baraxana.

Dama acikke take dashi jin wai yarjejeniya akayi a kotu don kar bilti ta koma kan aikinta..

Bilti Tana isa gidan ta samu basuma farka ba
Haka ta shiga kitchen tay musu hadadden family breakfast koda wasime taganta sai taji kamar mafarki takeyi tafara murna,duk ta gama daukawa bilti ta dawo kenan na din din amma ina abun ba haka ya kasance ba.

Ashe nasiha kawai tazoyi ma taheer akan abunda ya shiga tsakaninsa da iyayensa, da ikon Allah kuwa akaci nasara ya saukar da fushin har ya bada maman nasa hakuri komi ya dawo dede.

Yau karfe hudu saura ya dawo da wasime gida baijata sunje dakinshi ba ya kyaleta ta wuce nata dakin danta huta,can bayan ta kammala kimtsawa yunwa ne duk yabi ya isheta Gashi tana tsoron taba wani abu a kitchen kar maman taheer ta fito ta hanata. Ita tun ranar data amshe mata girkin taliyarta ta somajin tsoro da kuma shakkarta.

Hijabinta dogo har kasa ta saka da niyyar zuwa binciko waje taga ko taheer ya dawo,tana bude kofar dakinta sukaci karo da mahaifyar san a tsaye a bakin kofarta tana mata murmushi mai taushi da sanyi,hannunta harda hidiman tray din abinci datazo mata dashi…

gaban wasime na fadi ta tsuguna har kasa
Zata gaishe ta,acikin sakin fuska tace taso muje karki damu,wann abincin kine na kawo miki naga tunda kuka dawo baki sauko ba..i knw u must be very hungry so no talking
Harse an koshi .

A mamakance wasime ta dinga kallonta har sukakai site dinta da bata taɓa shiga acikin gidan ba,simple falour ne haddade an jera wasu L shape leather cushions wanda daga shi sai plasma tv da rug da kuma center table,palon babu wani kayan tarkace.
Amma yana qamshin turaren wuta bana kadan ba.

A kasa ta ajiye abincin snn ta umarce wasime data zauna ta ci,tsoro gaba daya ya cikka zuciyarta ta rasa sauyin yanayin na menene..

Waje taga maman taheer din ta samu ta zauna da remote din tv a hannunta tana kallon tashar nat geo wild, time to time haka zata juyo tanai ma wasime murmushi tana dada tursasa danta ci abinci.

Wasime tanakan ci taji tafara mata maganganu kamar dai hakuri take son bata amma a hade yake cikin zolaya tana tuhumarta akan yanayin shakuwar dataga sunyi da taheer,dake abun acikin zolaye hakan yasa wasime bata dago abun daidai ba amma definately dai tasan acikin maganganun akwai hakuri kawai dake tabata akan recent behaviours dinta towards her….
08060712446
7/25/22, 19:19 – Kawata: 49#
Dreams comes true

Yau yakasance ranar jumu’a,rana ce da ake expecting bullowan result sheet dinsu taheer a millitary hdqtr dake can cikin gari,kasancewar safiyace ya jima xaune Akan dardumansa yana karatu bayan ya kai Ayan karshe tacikin Suratl kahfi,daga kansa sama yay ya kalle agogo ganin har bakwai da rabi yay, ya sa shi miÆ™ewa a hankali ya rufe qur’anin ya ajiye a bedside drawer.

jallabiyan jikinsa ya cire ya nufi bathroom ya dau lkci yana wanka da sabulai masu dadin kamshi da shower gel duk ya cika dakin da qamshi sanye da bathrobe blue colour ya fito yana goge lallausan fatar jikinshi da karamin towel,gaban mirror ya nufa direct ya dauko lotions dinsa daga tsaye nan ya shafa yabi ko ina ajikinshi yana gamawa ya jawo man gashinsa ya shafa ya shiga combing gashin nasa sosai..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button